JIDDO(Gidan aurena) PART 41

47 2 0
                                    

    JIDDO
(Gidan aurena)
       By
MAMAN NABEELA

HAPPY SALLAH TO ALL FAN'S, FREAND ND FAMILY.

ED-EL MUBARAK ALAINA WA ALAIKUM TAƘABBALALAHU MINNA WA MINKUM.
ALLAH YA MAI-MAITA MANA AMIN SUMMA AMIN.

________Hira sosai ta ɓarke tsakanina da Asma'u cikin hirar take bani labarin yadda yanzu rayuwar gidansu ta sauya har da labarin takarar da Suwiɗi keyi ta gwamna.

Dariya sosai maganar ta bani zuciyata  cike da tausayin jama'ar jahata a raina na ce “ya Allah karka jarrabi jama'a da shugaba irin Suwiɗi” ba don komai ba sai don shi tun daga gidansa ba adali bane ina kuma ga ya samu shugabancin jaha guda irin Kano....

“Ammey! Ammey!!” Kiran da Asma'u tayi min ya dakatar dani daga zancan zucin da nake.

Kallonta na yi na ce “na'am Husnah”

“Ammey tunanin me kike ina ta magana baki ji ba? ” Asma'u ta yi maganar fuskarta ɗauke da damuwa.

“Husnah babu wani tunani da nake tashi muje gurinsu Anty Hajju muma ayi aikin damu kar mu barsu su kaɗai” na yi maganar ina tashi tsaye, Anty Hajju itama tare suka zo da su Asma'u  harda Baba Ladidi da Amma ƙanwar Annarmu.

Tashi ta yi muka fita,  falon ƙasa muka koma wanda Anty Maimuna da Baba Ladidi ne kawai a ciki, miƙa mata sabuwar wayar na yi da tsohuwar tawa ina ce wa“Anty gashi ki saita min”

“To ai na ɗauka ma ɗoki yasa kin  saita da kanki, na yi tunanin ma da naga shiru ko ana chan ana soyewa ne”Anty Maimuna ta yi maganar tana dariya.

“Kai Anty ni ba wayar ma da na yi fa tunda na shiga” na yi maganar fuskata da murmushi.

“Ehyyee! Yanzu Yaron shi ya kawo mata wannan waya sai ƙyalli take kamar wadda aka yiwa wanka da mai? To ai kuwa da sake maza yazo na ganshi idan ya yi min ni zan shiga daga ciki, muddin  zan dinga asuwaki da naman Kaji sannan zan dinga zuwa Makka aikin hajji duk shekara” Baba Ladidi ta yi maganar cike da barkwanci irin na Kaka da Jika.

Dariya duka muka kwashe da ita.

“Aikuwa nake faɗa miki Hajja Kakus har naman ɗauwisu ma zaki yi asuwaki da shi ba iya na kaji ba,  hajji kuwa ai sai kinje har kin sa an biyawa wasu”Anty Maimuna ta yi maganar tana dariya haɗe da fara bawa Baba Ladidi labarinsa.

Tashi na yi na shiga kitchen gurinsu Anty Hajju da Amma da suke ta aikin har-haɗa kayan girkin da za'ayi gobe na suna.

“Sannun ku da aiki” na ce ina jan kujera na zauna haɗe da fara kama nima aikin.

“Yauwa Jidda”Amma da Anty Hajju suka amsa min suna cigaba da aikinsu.
Ban jima da fara aikin ba Anty Maimuna ta fara ƙwalu min kira tashi na yi na wanke hannuna na fita ina ce wa“na'am”

“Jidda kin duba wayarki kuwa!  Kinga misscall kusan ashirin ina tunanin ma tun muna zaune ana yin ƙonshi ake kira! ” Ta yi maganar tana miƙo min wayar.

“Anty to ki gama saita min  sai na bi kiran daga baya tunda magriba ma ta ƙarato”

“To shikenan na buɗe miki email ga pswd ɗinki nan na rubutashi a takarda, ba na buɗe miki Whatsapp Amma da wane layi zan buɗe miki da tsohun ko sabon? ” ta yi maganar tana kallona.

“Anty ki buɗe kawai ko ma da wanne ne a ciki ”

“To bari kawai na buɗe miki da sabon don hankalina yafi kwanciya dashi ” ta yi maganar tana cigaba da danna wayar.

“To” na amsa ina dariya don nasan ba don komai ta faɗi haka ba sai don tsohun layina layi ne da na yi rayuwa dashi  tun a gidan Suwiɗi.

Ko da ta gama saita min komai ce wa na yi  ta riƙe wayar a hannunta ni kuma na koma gurinsu Anty Hajju
muna cikin yin aikin aka kawo Kaji masu uban yawa da za'ayi amfani da su a abincin suna.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now