JIDDO (Gidan aurena) Part 29

8 0 0
                                    

*JIDDO*
(Gidan Aurena)

_Story by_

*MAMAN NABEELA*

(_TEAM JAJURTATU 6_)
*BAYAN RAI (KHADIJA ISHAQ)*
*JIDDO GIDAN AURENA(MAMAN NABEELA)*
*JINANE(ZAITUN MAMAN FAUZAN)*
*IN BA KAI(OUM AFREEN)*
*SAIFUL ISLAM(OUM AMRA)*
*NURHAAN(SHUATY)*

*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*HAƊAKA PALACE GROUP*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

*PAGE* 2️⃣9️⃣
Ɗaki guda Anty Maimuna ta bani wanda yake kusa da na ta a saman bene kasantuwar gidan irin ginin nan ne na masu hannu da shoni,  sashen mai gidan daban yake amma  manne yake da jikin sashenta wanda da ƙofa wadda zata sadaka da cikin sashen ta ɓangarenta.

Tamkar wata baƙauyiya haka na koma saboda na jima rabona da gidanta zan iya ce wa ma bayan aurena da Suwiɗi bai fi sau uku naje gidanta ba saboda baya  barina.

Sosai na ga gidan ya sauya ɗakin da na ke ciki nake ta bi da kallo a rai na ina faɗin ita dai Anty Maimuna  ta dace da gidan aure.

Jaririn da yake hannuna ne ya fara kuka wanda tun iso wata dana ɗaukeshi nake maƙale dashi hatta da abinci  yana hannuna na ci  duk kuwa da yadda Anty Maimuna taso na ajiyeshi saboda naji daɗin cin abincin amma ban ajiyeshi ba yana cinyata har na gama ci,  hura kunensa na fara yi ina jijigashi sai ga Anty Maimuna da ta fita ba daɗewa ta shigo.

“Jidda baki shiga wankan ba?  Ni da na ce ki kwantar dashi ki shiga kan na dawo ai dana jiyo kukanshi na ɗauka ma kin shiga ne shi kuma ya fara  rigima! ” Ta yi maganar tana zama kusa dani.

“A'a ban shiga ba ina jiran ko Ihsan ce idan ta shigo sai na bata shi na shiga,  ai yanzu ya fara ma kukan” na yi maganar ina miƙa mata shi ganin yaƙi yin shiru.

“Yauwa ki shiga wankan zaki fi jin daɗin jikinki, idan kin fito Dadyn su Ihsan ya dawo sai ku gaisa yanzu yake tambayata kin iso?  Na ce eh baki jima da isowa ba. Anty Maimuna ta yi maganar tana ɗora jaririn  a kafadarta.

“Toh!  Ba na shiga” na yi maganar ina tashi na nufi banɗaki.

Bayan na yi wanka na fito ban samu Anty Maimuna a ɗakin ba maya-mayan da suke kan dressing mirow na ɗauka na shafe jikina dasu ɗaya daga cikin dogayen rigunan da na tahu dasu na ɗauko baƙa  mara nauyi na saka haɗe da ɗaura ɗankwalin rigar a kaina,  saka hijab na yi na shimfiɗa darduma na ta da sallar magriba da naji ana yi  sanda na shiga banɗaki.

Ina zaman tahiya Anty Maimuna ta kuma shigowa tana cewa idan na idar na fito ta kuma fita bayan na yi sallama sai da na yi Addu'o'i na na shafa sannan na naɗe  darduma na mai da ita inda na ɗauka, ban cire hijabin jikina ba na nufi ƙofa na fita falon dake saman na nufa jin sautin magana daga ciki.

Sallama na yi  ina shiga ciki.
“Amin wa alaiki salam shigo mana Jidda”Anty Maimuna dake kusa da Tahir Mai gidanta ta yi maganar.

Tahir ma da ya gama shan ruwan da Anty Maimuna ta zuba masa amsa sallamata ya yi yana faɗin “ranki ya daɗe barka da isowa ai na ɗauka ko gajiyar hanya baza ta bari mu gaisa ba sai zuwa gobe! ” ya yi maganar cike da zolaya yana dariya.
 
“Wa ce ni na iso na kasa gaida ranka ya daɗe Honorable  guda! Ina wuni na sameku lafiya? ”
Na yi maganar ina dariya nima.

“Lafiya lau Alhamdulilah ai yanzu ke ce Honorabiyar Hajiya Hauwa'u ki ka sani ko bana mutanen Kaduna su fitar dake ki tsaya takara!” Tahir ya kuma maganar cike da barkwanci.

“Rufa min asiri ni a suwa? Ai wannan sai ku manya-manya, ansamu ƙaruwa kuma Allah ya raya” na yi maganar idanuna waje ina riƙe baki haɗe da dariyar wannan zolaya sannan na haɗa da yi masa barkar haihuwar Anty Maimuna .

“Amin amin ya mutan gidan da kuma yaranki? ”

“Lafiya lau,  duk suna gaida ku suna yi maka barka kuma” na bashi amsa.

“ Assalamu alaikum oyoyo my Ammey na yanzu ina shigowa Ihsan ke faɗa min kin zo” Haidar ya yi sallamar haɗe da maganar yana shigowa.

“Oyoyo ɗana na kaina ka dawo? ” Na yi maganar ina dariya.

“Washh! Eh wallahi Ammey ina wuni ya hanya ina kakus Anna?” ya yi maganar yana faɗawa saman kujera haɗe da zube kayan dake  hanunsa Labcoat da verifcase suma a kujerar.

“Lafiya lau tana gaisheku, sannu ya aikin? ” Na amsa shi ina tambayarsa.

“Lafiya lau Ammey aiki ba daɗi sai wahala Dady Momy barka da gida”ya yi maganar yana ɓata fuska kamar zai yi kuka.

Dariya duka suka kwashe da ita
“Kai Yaya Haidar ga ka da sunan jarumai amma kullum kana gudun aiki na fa je naga ba wani aikin wuya ka ke ba banda duba marasa lafiya amma kullum kamar wanda yake aikin dako sai ka ringa kiran wahala!” Ihsan ta yi maganar tana daga kusa da Dady Tahir tana dariya.

“Ke ni sa an ki ne? Yauwa Ammey ki shiga tsakanina  da ita ta saka min ido da yawa  haka ran nan Hajiya  tazo take yin gulmata saboda ta rai nani Momy  kuma ta hanani hukunta ta” Haidar ya yi maganar yana wurga mata harara.

“To ai laifinka ne da ka ke yin raki a gabanta hope dai yau kayi aiki sosai?  Don zan bincika! ” Dady ya yi maganar fuskarsa cike da fara'a yana dubanshi ganin yadda ya lafe jikin kujera kamar wanda yasha duka.

“Allah Dady kwana biyun nan aikin da nake yi yana da yawa, yau ma fa duk Dr-Jabir ni ya ringa turowa marasa lafiya bai barni na huta ba sai da lokacin sallah ya yi shima ina dawo wa daga sallah abinci kawai na ci naga ya kuma turon wasu” Haidar ya kuma yin maganar da ƙyar tamakar zai fashe da kuka.

“Kai! Na kuwa godewa Dr-Jabir ai temakon ka ya yi domin ta haka ne zaka saba ka kuma daɗa gogewa a aikin ka”Dady ya yi maganar yana ɗaukar wayarsa da ake kira ya kara a kunne.

“Son ai yanzu kamata ya yi ka je ka yi wanka sai ka fito ka ci abinci kazo ka bani labarin Asibitin naku” na yi maganar ina dubanshi.

“To Ammey bari na shiga ciki”ya yi maganar yana tashi ya nufi wata ƙofar glass dake cikin falon yana zabgawa Ihsan harara.

Hira muka fara yi da Anty Maimuna ya yin da haka kawai naji gabana yana faɗowa Bebynta da yake hannuna nake ɗauka hoto a wayarta dake hannun.
“Ammey kawo na ɗauke ku tare” Ihsan da ta dawo kusa dani ta yi maganar.

Miƙa mata na yi  ta  ɗaukemu  tare da Babyn na karɓa ina duba wayar,  dake babba ce sosai hoton ya yi matuƙar kyau.

“Maimun A. Rashid yana yi miki barka, gobe zai zo  shi da Dada” Dady ya yi maganar bayan a gama wayar.

“Ina amsawa ka ce muyi shiri muna da manyan baƙi! ” Anty Maimuna ta yi maganar tana dariya.

“ƙwarai kuwa ai tunda ga Jidda nan ta zo sai ta shige gaba gurin yin komai ke kuma sai ki nuna mata”ya yi maganar yana murmushi haɗe da yin wani tunani a cikin ranshi yana fatan tabbatarsa.

Gaba nane ya kuma faɗuwa lokacin da Tahir Mijin Anty Maimuna ya fara magana a cikin raina na fara mai-maita sunan da ya ambata  ina jin gaba na na kuma faɗuwa, abinda ban taɓɓa ji ba duk tsahun rayuwata don an ambaci wani.

Duk maganar da Tahir ya yi ba jinsa nake ba domin na faɗa duniyar tuna nin da ban san ma mai nake tuna nin ba, dafa ni da Anty Maimuna ta yi tana magana yasa ni dawo wa daga duniyar tuna nin da na lula.

“Lafiyarki ƙalau kuwa Jidda? Muna ta magana kinyi shiru! ” Anty Maimuna ta yi maganar tana zama kusa dani.

A jiyar zuciya na sauke ina kallonta na ce......


_Pls share & share_ 🙏🙏🙏

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now