*JIDDO*
(Gidan Aurena)_Story by_
*MAMAN NABEELA*
(_TEAM JAJURTATU 6_)
*BAYAN RAI (KHADIJA ISHAQ)*
*JIDDO GIDAN AURENA(MAMAN NABEELA)*
*JINANE(ZAITUN MAMAN FAUZAN)*
*IN BA KAI(OUM AFREEN)*
*SAIFUL ISLAM(OUM AMRA)*
*NURHAAN(SHUATY)**DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*
*HAƊAKA PALACE GROUP*
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*
_We buy Data from the afoderble price._
*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500**MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE DATA BLNC: *228#*'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
*BARKA DA JUMA'A ALLAH YA KARƁI IBADUNMU AMIN SUMMA AMIN*
*PAGE* 3️⃣0️⃣
________“Lafiya lau Anty mai ku ka ce? Wallahi ban jiba” na yi maganar ina kallonta ganin yadda take kallona.
“Ban yarda babu komai ba, ga! Yadda ki ka yi magana a sanyaye fa! ” Anty Maimuna ta kuma maganar cike da damuwa da lamarin ƙanwar tata.
“Allah Anty babu komai ban ma san hankalina ina ya tafi ba fa da kuna maganar” na yi maganar ina dariya.
“Uhm to ai shikenan tunda ba komai, dama baƙi za muyi gobe shine Dadyn su Ihsan ya ce ke zaki jagoranci yi musu abinda za'a tarbesu dashi” ta yi maganar yana yinta na nuna bata yarda da abinda na faɗa ba.
“To Allah ya kawo su lafiya”na yi maganar ina murmushi.
“Amin” suka haɗa baki suna faɗe ita da Tahir.
“Ni ma dai dole na ce wani abu! ” Tahir ya yi maganar yana dariya.
Kallonshi ni da Anty Maimuna muka yi.
“Jidda kar dai tunanin gida ki ke yi daga zuwanki yau! Ni da nake son ce wa ki bari har sai ta yi arba'in sannan ki tafi ko ya ki ka ce Maimun? ” Ya yi maganar yana kallon mu ni da Anty Maimuna haɗe da ƙareta da dariya ganin yadda na zaro ido lokacin da yake maganar.
“Eh wallahi kamar ka shiga zuciyata Hubby don nima tunanin da nake kenan wallahi” Anty Maimuna ta yi maganar ita ma cike da fara'a.
“Au kema haka zaki ce!”
Na yi maganar ina kallonta.“Eh mana dama lokacin da ki ke auren wan can mai zubi da kwaɗin ai ba barin ki yake ki shiga dangi ba kinga yanzu kuwa tunda Allah ya yanke miki rayuwa dashi ba sai ki wa ta ya ba, bari ma kiga na yi arba'in tare zamu zaga dangi dake don wasu ma sun fara manta ki” Anty Maimuna ta yi maganar cike da haushin Suwiɗi na yadda ya mayar mata da Ƴar uwa.
“Haba Maimun ya ya kuma haɗa mutum da kwaɗo babu kyau fa ki bari ko don darajar Ƴa ƴan da suka haifa ki dena faɗar haka”Tahir da ya sanya glass ya na danna laptop ya yi maganar.
“Shi kenan na dena faɗa Hubby wallahi mutmin ne bashi da kirki ko kaɗan ka duba kaga halin da ya jefa ta fa! ” ta yi maganar cike da ƙara jin tsanarsa.
“Duk da haka Maimun yanzu ba gashi ta rabo da shi ba sai muyi mata fatan wani mijin na gari”
Tahir ya kuma maganar yana ci gaba da danna laptop ɗinsa.
