JIDDO
(Gidan auren)
By
MAMAN NABEELAMurmushin da har sai da na ji sautinsa ya yi kafin maganarsa ta biyo baya.
“Ke kuwa Maijiddahhh” ya yi maganar yana ƙarasheta da jan sunana.Ji na yi tamkar yayi ta mai-maita sunana saboda yadda ya iya furtashi, cikin son ya faɗa min waye shi na ce “baka fa faɗa min waye kai ba kuma a ina kasan sunana har kasamu number wayata? ”
Murmushi A.Rashid ya kuma saki haɗe da ce wa “ To ranki ya daɗe bari na yi miki bayan ko a taƙaice ne Gimbiya” ya yi maganar sautin murmushinsa har ina jiyoshi.
“Da farko dai sunana Abdurrashid Ahmad Mai nasarah, ni haifafen nan Kaduna ne,Mahaifina asalinsa ɗan Gombe ne, Mahaifiyata kuma Ƴar mai duguri ce, inda kuma na sanki a gidan Tahir, sunanki kuwa da number ki kar kiyi mamaki don na samesu, ina fatan kin gamsu! Kuma ina fatan za'a karɓeni hannu bi-biyu” ya yi maganar cikin murmushi.
Murmushin nima na yi na ce “uhm to na fahimta sai dai zanso ka ɗan bani lokaci”
“Ok babu damuwa zanyi jimrin sauraronki amma da sharaɗi! ” Ya yi maganar cikin da daɗar muryarshi.
“Sharaɗi kuma? ” Na yi maganar ina buɗe idanuna sosai kamar yana gabana.
“Eh mana” Ya yi maganar cikin dariya.
Murmushi na yi na ce“to ina jinka! ”
“Da farko iya adadin lokacin da zaki ɗauka kafin ki bani amsa zaki ringa tura min saƙo a duk safiya da dare na soyayya, sannan ni kuma zan dinga kiranki kamar sau biyar a rana kira uku voice call,kira biyu video call” ya yi maganar yana ƙarasheta da dariya.
Tun bai gama maganar ba na fiddo idanu waje “wai da gaske ka ke? ”
“Eh mana sunyi kaɗan ko? ” ya yi maganar cike da nishaɗi.
“A'a a'a” na bashi amsa ina tashi daga kan gadon da nake kai kwance ganin Anty Maimuna ta shigo.
“Jidda Abbansu Ihsan na son ganinki”Anty Maimuna ta yi maganar ba tare da ta kula da wayar dake manne a kunenta ba.“To Anty” na bata amsa ina miƙewa tsaye.
“Na ji kamar kina da uzuri idon kun gama dare bai yi ba sosai zan kuma kira kinji Ƙoratul aini”
Ya yi maganar cikin wata iriyar murya wadda ke sanya wanda ke sauraro cikin shauƙin cigaba da jinta.“To” na amsa ina cire wayar a kunnena.
“Au Jidda waya ki ke ai ban sani ba” Anty Maimuna ta yi maganar don sam bata kula ba sai lokacin da ta ke cireta daga kunne da kuma maganar da taji ta yi.
“Ko dai munyi sabon kamu ne?” Ta kuma maganar cikin dariya.“Kai Anty sabon kamu kuma! Yaushe na farfaɗo daga wahalar gidan aure!Da zan kuma jefa kaina cikin kula wasu Mazan kuma!” Na yi maganar ina tashi tsaye don duk sanda zan tuna wahalar da nasha a gidan Suwiɗi na kanji sam aure baya gabana.
“Kul Jidda don Suwiɗi bai riƙe ki da kirki ba bashi ke nufin Maza duka haka suke ba, sai kiga Allah ya kawo miki wanda a kansa zaki bam-bance Maza suna suka tara amma kowa da halinsa”
“Anty wai wannan fa da ya kirani ko Abdurrashid sunansa wai a gidan nan ya ganni kuma wai so na ya ke” na yi maganar ina bin bayan Anty Maimuna da ta nufi ƙofa.
“Jidda kina nufin A.Rashid shine ya kiraki? ” Anty Maimuna da har ta buɗe ƙofa ta dakata haɗe da juyowa ta yi maganar fuskarta washe da murmushi.
“Eh ina ga shine”
“Ke taso muje gurin Tahir wata ƙila kiran da ya ke miki kenan idon munje a naji komai” Anty Maimuna ta kama hannunta suka fito daga ɗakin tana fatan Allah yasa shine, don A.Rashid Mutum ne da kowa zaisu haɗa zuri'a dashi Mutum ne da dokiya bata sakashi ya sauka daga layi ba, baya shan giya baya cha-cha ba kuma yq nemqn Matan banza ga ilimin adini dana boko ga kuma uwa uba kyauta da iya mu'amallada jama'a.