JIDDO (Gidan aurena) Part 25

11 0 0
                                        

*JIDDO*
(ɢɪᴅᴀɴ ᴀᴜʀᴇɴᴀ)

_sᴛᴏʀʏ ʙʏ_

*MAMAN NABEELA*
( _SAHIBAR  D. A. W. A_ )

(_ᴛᴇᴀᴍ ᴊᴀᴊᴜʀᴛᴀᴛᴜ 6_)

*ʙᴀʏᴀɴ ʀᴀɪ (ᴋʜᴀᴅɪᴊᴀ ɪsʜᴀǫ)*

*ᴊɪᴅᴅᴏ ɢɪᴅᴀɴ ᴀᴜʀᴇɴᴀ(ᴍᴀᴍᴀɴ ɴᴀʙᴇᴇʟᴀ)*

*ᴊɪɴᴀɴᴇ(ᴢᴀɪᴛᴜɴ ᴍᴀᴍᴀɴ ғᴀᴜᴢᴀɴ)*

*ɪɴ ʙᴀ ᴋᴀɪ(ᴏᴜᴍ ᴀғʀᴇᴇɴ)*

*sᴀɪғᴜʟ ɪsʟᴀᴍ(ᴏᴜᴍ ᴀᴍʀᴀ)*

*ɴᴜʀʜᴀᴀɴ(sʜᴜᴀᴛʏ)*

*ᴅᴀsʜᴇɴ ᴀʟʟᴀʜ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*

*ʜᴀƊᴀᴋᴀ ᴘᴀʟᴀᴄᴇ ɢʀᴏᴜᴘ*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''
https://chat.whatsapp.com/Cl5xn2qD4wF24JErear0iF

*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y

*ᴘᴀɢᴇ* 2️⃣5️⃣

Cikin sati ɗaya da dawo wa ta gida jikina ya fara sauƙi sosai,  don tunda Baba Ƙaura abokin Kakanmu ya bada maganin da za'a ringa yi min.
Anna sosai ta dage take yi min duk da da farko ta tsorata lokacin da ta fara  yi min don ina shan wanda ya ce a sha na fara zuba wani baƙin amai wanda har sai da na galabaita, a ranar duk hankalin ƴan gidan sai da ya tashi Yaya Ahmad kuwa  sosai ya kafa nacin sai an kai ni Asibiti amma Anna da Baba suka hana  saboda suma sun ga alamar cotar bata Asibiti bace. Abu kamar wasa sai  amai na tsayawa sai ga gudawa ta ɓarke min take jikina ya fara ƙadandanewa babu shiri Yaya Ahmad yayi waje. Su Asma'u kuwa banda kuka babu abinda suke Anna ma duk dauriyarta sai ga hawaye na fita daga idanunta.
Kama ni su Azima suka yi suka kai ni banɗaki Anna ta gyara min jikina.  A falo kuwa su Azima da Asma'u su suka gyara gurin da ya ɓaci da gudawar suka saka turaren wuta, ana dawo dani falo ba jimawa  sai ga Yaya Ahmad da wani Likita ganin yanayin jikina take Likitan ya jona min ruwa haɗe da zuba allurai a cikinsa ba'a jima da jona min ruwan ba baci ya ɗaukeni.   

“Kamar tayi baci ko? ” Yaya Ahmad yayi maganar yana duban Anna da ta zubawa guri ɗaya ido,  bayan ya dawo daga raka Likitan waje.

“Eh tayi baci Amadu”
Anna tayi maganar cike da damuwa tana kallon gurin da Jiddo take kwance fuskarta tayi fayau.

Zama yayi kusa da ƙafar Babansu da yake zaune yayi jigum tarin tausayin Ƴarshi na adabarsa, damuwa tasa ya gaza faɗin komai.

“Baba ku gafarceni kai da Anna na kira Likita ba tare da izininku ba wallahi bazan iya haƙurin ganin Jadda na shan irin wannan wahalar ba!” Yaya Ahmad yayi maganar cike da ladabi.
Numfashi Baba ya sauke yana ce wa
“Ahmad ai abinda kayi shine dai-dai, in banda Allah yasa kai ɗin mai zafin nama ne ka yi saurin nemo Likita ai da bamu san irin halin da zata kuma shiga ba.
Baka yi mana laifin komai ba sai dai ma mu ƙara yi muku Addu'ar Allah ya ƙara sanya muku tausayin junanku da ƙauna yadda ko da bayan ran mu ƙanenka baza suyi kukan maraici ba”.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now