*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABILA**Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
_Chat me on_ :07042808467
*Page* 1️⃣6️⃣
Dai-dai wani ƙaton get mai Motar da ya ɗauko mu ya perker yana danna horn, idanu na ƙara buɗewa ina daɗa kallon inda mai Motar ke ƙoƙarin shiga na buɗe baki zanyi magana Ummansu Harisu ta rigani da cewa“bawan Allah ko dai baka gane inda zaka kaimu bane naga kana ƙoƙarin shiga wannan tsalelan gidan? ” Lubabatu tayi maganar tana muzurai. Kar dai mai Motar nan sace su zaiyi ya kaisu a fille musu kai, ta kuma rayawa a ranta.
“Abinda nake son faɗa kenan kika riga ni" nayi maganar nima ina duban mai Motar.
“Hajiya nan ne gidan da aka faɗan na kawo ku! ”
mai Motar yayi maganar yana shigar da Motar cikin gidan da mai gadi ya buɗe.Drivern be gama magana ba cikin Lubabatu ya bada wani sautin ƙuuuuuu hankali tashe ta yaye facemack ɗin dake fuskarta tana damƙar hannun Salma dake kusa da ita tana muzurai.
Muna fitowa daga Motar muka hango Ƴan uwan Suwiɗi dake zaune kan wata babbar tabarma muka nufi gurin, duk irin yadda nake jin labari na irin farin cikin da ake ji idan anyi gidan kai ni sai ya zamana na rasa me nake ji akan wannan gida. Har cikin zuciya da ruhina abinda nake ji beyi kama da farin ciki ba, sai wani irin faɗowar gaba ma da nake ji addu'ar duk da tazo bakina nake yi akan Allah ya kawo min sasaucin abinda nake ji.
Jikina a sanyaye muka fara bin gidan muna gani tuni Ummansu Harisu ta ware ta shige gaba gurin ganin ko ina na gidan.
Ni da Ummansu Harisu ɗakunan mu ciki da falo ne sai ɗakinsu Asma'u da Salma sai kuma wasu ɗakuna uku da muka jisu a rufe wanda muke kyauta zaton ɗaya nasu harisu ne sai kuma ɗakin Suwiɗi, dukanin ɗakunan a cikin wani falo suke mai girma da aka saka masa wasu kujeru masu kyau.
Gaba ɗaya yaran banda murna babu abinda suke na su ma sunyi gida irin na ƴan gayu.
Ƴan uwan Suwiɗi da muka tahu dasu sai zuba santi suke wasu suna faɗin ai kawai nan zasu dawo da zama tunda Allah yasa ɗan uwansu yayi kuɗi!._Bayan wata biyu_
Wata biyun da muka yi a cikin sabon gidan da Suwiɗi ya siya mun ci gaba da rayuwa ne kamar yadda muke a wancan gidan, babu wani canje dan kayan abinci da nazo dasu daga gida suna ƙarewa muka koma gidan jiya.
Sana'ar ma da na keyi unguwar da muka koma sam bata yiyuwa dan gidaje ne manya-manya ba wanda ke fitowa neman wani abu da alama komai mazajensu na siya musu su ajiye, shiyasa ko sana'ar ma mutum yayi ba ciniki yake ba sai dai in talla zai ɗorawa Ƴaƴansa su fita da ita can bakin hanya.Yau ma haka muka tashi bamu da wani abin sakawa a bakin salati ga wani irin haɓo da ya sarƙeni kwana kin nan wanda na rasa ko na menene dan ni a rayuwata da wayona ban taɓa yin haɓo ba sai a wannan lokacin.
Gaba ɗaya na rame na ƙara fari tamkar jikina babu jini, fitowa nayi daga banɗaki bayan na samu haɓon ya ɗan tsaya. Zama nayi gefen gado na wanda yayi dai-dai da shigowar Asma'u hannunta riƙe da ma dai-dai cin flas ɗin abinci su Zainab na biye da ita. “Ammey gashi Maman Nawal da naje na yiwa kitso ce ta aiko min dashi” Asma'u tayi min maganar tana ajiye flas ɗin tana kallona.“Toh Allah ya saka mata da alkairi, ki zubawa su Zainab da Abdull sai ki cinye sauran! " Nayi maganar ina duban Asma'u.
“Ammey ai abincin zai ishe mu”Asma'u tayi min maganar tana buɗe flas ɗin.
Fried rice ce shaƙe da flas ɗin wadda tasha naman kaza da kayan lambo, take ta cika ɗakin da ƙamshi albarka na fara sawa Maman Nawal ina ta shi mata albarka, tun bayan zuwan mu unguwar muke mutunci da ita don ma ni ina baya-baya da ita saboda sanin halin Suwiɗi da nayi. Da farko da ta fuskanci halin da muke ciki taso ta fara temaka mana da abinci idan ta dafa amma na nuna mata bazan ringa karɓa ba, daga baya da taji Asma'u ta iya kitso shine ta fara kiranta tana yi mata ita da yaranta tana biyanta sannan ta bata abinci.
Farantin da Asma'u ta ɗauko ta juye mana gaba ɗaya abincin a ciki muka yi bissmilah muka fara ci.
Bayan mun gama cin abincin Asma'u ta ciro kuɗin da aka bata na kitso ta miƙo min karɓar su nayi naga dubu uku ne har da ɗari biyar “Asma'u kuɗin nan ai sunyi yawa ga abinci ga kuɗi har dubu uku da ɗari biyar! ” nayi maganar ina jujuya kuɗin a hannuna.
“Ammey nima sai da nace mata sunyi yawa tace ai ita ta bani, Ammey kinga sai mu siyi ko garin kwaki ne da ƙuli da man gyaɗa mu ringa ci ” Asma'u tayi min maganar tana murmushi.
“Eh amma ba duka kuɗin ba dubu ɗaya da ɗari biyar ki je ki biya muku kuɗin wata na islamiyya,sai ki ajiye ɗari biyar ko wani abun zai tasu sauran sai ki siyo garin kwakin” nayi maganar ina miƙa mata kuɗin.
“Ammey ki ajiye a gurinki in mun tashi tafiya ma karɓa yanzu ki bada kuɗin siyan garin sai naje na siyo”
Bata kuɗin nayi suka tafi ita da Abdull.
“Ammey wai yaushe su Anty Salma zasu dawo daga bikin da suka je? ” Zainab tayi min tambayar tana dawo wa kusa dani.
“Sai ranar Litinin ina tunanin zasu dawo”
“Ammey muma ai zamu biki ko? kuma baza mu da su ba tunda basu tafi dani ba ko?” Zainab ta kuma jefu min maganar.
Murmushi nayi ina cewa “eh mana wa zai je dasu tunda basu tafi da Auta ba! "
Dariya ta ƙyal-ƙyale da ita tana cewa “Ammey ai da bikin Anty Azima sai nafi kowa kyau ko? ”
“eh mana Zainabu ai ko sarauniyar kyau baza ta nuna miki kyawu ba” nayi maganar ina dariya.
“Yeas yauwa Ammeyna” tayi maganar tana rungumu ni.
★★★★★★★★
Da dadare ƙarfe 12:30 na farka dan yin sallah kamar yadda na saba bayan nayi alwala na tashi Asma'u da tunda su Salma suka tafi biki da Ummansu ta dawo kwana a ɗaki na itama taje ta ɗauro alwala muka fara sallah,bayan mun idar da sallah Asma'u komawa tayi ta kwanta lokacin ƙarfe biyu saura.
Sai da na shafe kusan minti talatin ina addu'o'i sannan na shafa ƙishiruwar dake damuna tasa na tashi na ɗau fitila na fito falo don ɗebo ruwa.Ƙofar da tunda muka zo gidan bamu taɓɓa ganin an buɗe ta ba idanuna suka sauka a kanta, ganinta a buɗe, ɗakin da Lubabatu sanadinsa sai da tasha marukan da har ya kaita ga kwanciya a Asibiti bayan dawo warmu saboda tace sai an buɗe taga menene a ciki saboda yadda Suwiɗi ya hana ko zuwa ƙofar ɗakin!.
Murza idanuna nayi ina daɗa waresu dan ganin abinda nake hanguwa daga inda nake, jikina ne ya fara rawa hango kamar mutum tsirara ta cikin ɗan hasken da ya haska ɗakin. Ganin kamar ma ba mutum ɗaya bane a ɗakin yasa jikina ya kuma ɗaukar mazari zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito dan tashin hankali na abinda nake hangowa daga cikin ɗakin, na fara takawa ina nufar ƙofar.
Duk ɗaga ƙafar da zanyi tashin hankali na ƙara ninkuwa yake da abinda idanuna suke hanguwa sautin murya kamar ta Suwiɗi nake jiyuwa da wasu muryoyi da ban san ko nasu waye ba da maganar da ta doki dodon kunnena yasa fitilar da take hannuna faɗuwa, wanda shi yaja hankulansu suka juyo...... ✍️_Pls share & comments_
*MAMAN NABEELA CE* ✍️
