JIDDO(Gidan aurena) PART 39

30 2 0
                                    

   JIDDO
(Gidan aurena)
       By
MAMAN NABEELA

Sosai idanuna ke jin bacci take na fara zuba hamma wanda yasa shi kuma yana jin haka ya yi min sallama haɗe da  fatan tashi lafiya, da amin na amsa  ina cire wayar daga kunnena.

Tashi na yi na shiga banɗaki na kama ruwa cikin ikon Allah jinin da nake sa ran ɗaukewarsa dama a yau naga ya tsaya wankan tsarki na yi tare da shiga ruwan ganyen magarya da na ɗiba gurin Anty maimuna sannan na yi  amfani da miski  towel naja na ɗaura sannan  na fito, doguwar rigar bacci na saka haɗe da hijabi  sannan na kabarta sallar isha'i.
Bayan na idar nafila na yi raka'a hudu sannan na yi shafa'i da wutiri, sosai na yi Addu'a musamman kan abinda ke tunkaroni inda na mika dukan lamurana ga Allah kan ya zaɓa min abinda yafi alkairi,  ban kwanta ba sai gurin 12 na dare duk kuwa da yadda idanuna ke buƙatar bacci.
Addu'ar kwanciya bacci na yi na shafe ko ina na jikina ban jima ba kuwa dadaɗan bacci ya kwasheni.

★★★★★★★★

A. Rashid sosai wayar da ya yi ta sanyashi farin ciki wanda ko da ya ajiye wayar jin alamar bacci take ji annurin fuskarsa bai kau ba ƙarasa aikin da ya keyi a laptop ɗinsa  ya yi cike da nutsuwa lokaci zuwa lokaci yakan saki murmushi wanda ke ƙara baiyyanar da zallar kyawunsa. Ture laptop ɗin ya yi daga gabansa haɗe da miƙewa ya nufi Bathroom direct shower ya buɗewa kansa take ta jiƙe gaba ɗaya ilahirin kayan da ke jikinshi cike da nishaɗi ya ke cire jiƙaƙon kayan jikinshi ya yin da ruwan har sannan ke zuba jikinshi ya ɗau tsahun lokaci yana a ƙasan shower kafin daga bisani ya kasheta yajawu bathrobe ya sanya a jinkin shi alwala ya ɗauro haɗe da ɗaukan towel ya fara goge sumar kansa mai kama  da ta Salman khan.
Fitowa ya yi daga Bathroom ɗin ya nufi clothes ɗinshi ya ɗauko  pajmas fari ya sanya jallabiya ya ɗako ya zura haɗe da shimfiɗa pray mat kamar yadda  ya zame masa jiki yin sallah ko wane dare muddin ba wata larura ta hana shi yi ba haka wannan daren ma ya raya shi da bautar Ubangiji ma ɗaukakin Sarki, buwayi gagara misali. Wanda bashi ya kwanta ba sai gurin ƙarfe uku na dare   bayan ya gama Addu'o'insa haɗe da cire jallabiyar jikinshi cike da nutsuwa haɗi da kwanciyar hankali ya kwanta a kan makeken gadonsa haɗe da jan blanket ya rufe jikinsa dashi fuskarsa har sannan ɗauke da tarin murmushi, kashe fitilar ɗakin ya yi yana karanto Addu'ar kwanciya bacci bai ɗau lokaci ba  daddaɗan bacci mai cike da ɗombin daɗi ya ɗauke shi.

★★★★★★★★

Washe gari: ina farkawa daga bacci  banɗaki na shiga na kama ruwa sannan na ɗauro alwala,  fitowa na yi na  kabarta sallah, bayan na idar kamar yadda na saba Azkar na yi kafin na tashi na gyara ɗakin fes na wanko banɗakin shima sannan na fito.

Gyaran gidan muka soma yi  ni da mai aikinta cikin ƙanƙanin lokaci muka gyare ko ina tsaf sai tashin ƙamshi ya ke, kitchen yau ma na nufa na fara haɗa musu abin kari tare da taimakon Dije mai aikinta shima bamu jima ba muka kammala.

Gyara Kitchen ɗin na bar Dije na yi ni kuma na ɗauki wermas ɗin da muka zu-zuba abinci na fara fitar dasu ina kai wa dining, sai lokacin Anty Maimuna ta fito.
“Jidda yau ma baki koma bacci ba ki ka fito kina bawa kanki wahala tun sanyin safiya! ” Anty Maimuna ta yi maganar tana ƙarasuwa gurin dining ɗin.

“Kai Anty wace wahala kuma a aikin gida?  Ni wallahi sam bana iya baccin safe da ake yi ne fa Anty, ko na kwanta ma bana iyawa wallahi” na yi maganar cikin murmushi ina kallonta  ganin yadda ta saki baki.

“Jidda ai kuwa koya zaki yi don ni so na ke ki huta hankalinki ya ƙara kwanciya, ki ƙara mur-murewa bari dai ayi suna ki gani ai bama zan barki ki koma yanzu ba sai kin ƙara kwana biyu” Anty Maimuna ta yi maganar tana ƙarasheta da dariya.

Dariya maganarta ta bani na kowa dara kafin na ce“Anty ai ko ke da Anna da Baba don nasan ana yin suna zaki ga sun fara ce wa yaushe zan tahu? ” Na yi maganar cikin dariya.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now