*JIDDO*
(Gidan aurena)
By
*MAMAN NABEELA**DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATIONS*
*Page* 31
___________kyakyawar dattijowar Matar da suka zo da Yaran ce zaune kan kujerar da ke cikin falon, fara ce tas sanye take cikin wani danƙareran less wanda daga ganinsa kasan ansha kuɗi, hannayenta duka sanye suke da war-waro wanda nake kyauta zaton na zinare ne. Murmushin fuskarta ne ya ƙaru wanda ya ƙara bayyanar da zallan kyaunta haɗe da tarin kamaninta da Yaran har haƙurin makkan da ke bakinta na bayyana lokacin da muka ƙarasa cikin falon. Har lokacin Anty Maimuna tana riƙe da hannuna yayin da Jinjirinta kuma yake saɓe a kafaɗarta.
"Mame sannunku da isowa"Anty Maimuna ta yi maganar cikin girmamawa tana sakin hannuna ta ƙarasa gurin Matar.
"Yauwa Maimuna ashe kuma an samu ƙaruwa? "
"Eh Mame ina wuni" Anty Maimuna ta gaisheta tana murmushi haɗe da miƙa mata jaririn.
"Masha'Allah! Masha'Allah!! Lafiya lau Maimuna kin sauka lafiya?"
Matar da ta kira da Mame ta yi maganar fuskarta cike da tarin fara'a tana duban jaririn."Lafiya lau Mame Alhamdulilah"
Maimuna ta yi maganar tana murmushi.Nima gaishe da Matar na yi ta amsa min cike da fara'a tana ce wa.
"Lafiya lau Ƴata, Maimuna dama ku twins ne?" ta yi maganar tana kallona tana kallon Anty Maimuna."A'a ƙanwata ce ita take bina" Anty Maimuna ta bata amsa tana murmushi.
"Masha'Allah"
Mame ta faɗa tana kuma kallona.
Haka kawai naji matar ta shiga rai na tun daga kallonta da na yi. Ga wani irin nauyinta da haka kawai na fara ji wanda yasa na kasa sakewa, Ƴar Macen da suka zo tare mai ɗan karen surutu wanda tunda muka shigo take yiwa namijin da suka zo tare magana, ita ta dawo gurin da na ke tana chu no baki gaba na jin haushin ƙin kulata da ya yi."Anty Preety good afternoon" ta gaishe ni tana hayewa kan cinya ta, duk da a ƙalla za ta yi sa'a da Zainab ɗina.
"Lafiya lau Ƴan mata ya sunanki? " Na amsa gaisuwar da ta yi min haɗe da tambayarta ina murmushi."Sunana Jannatul Firdausi! Dady na yana ce min sweetheart baya faɗin sunana saboda ya ce sunan Mamen shi ne da ni, Mame kuma tana ce min Firdausi Ammar kuma yana ce min Jannat shi da su Anty Bintu" ta yi maganar tana nuna Matar da suka zo da ita, haɗe da nuna Yaron da ta kira da Ammar wanda suke mugun kama dashi tana juya idanu kamar wata Babba.
Dariya sosai yadda Yarinyar ta yi ya bani na kuwa dara, ina dariyar na ce "ai kuwa sunan naki mai daɗi ne sosai."
Washe baki ta yi tana ce wa "da gaske Anty! Haka su Ra'is ma suke ce wa wai yana da daɗi, ni dai bana sunshi.
Dada fa sai ta ringa wani cemin Fiddau! Na faɗawa Dady ya sauya min suna ya ce wai ba'a sauyawa, kuma babu kyau a sakawa mutum suna ya ce baya so Allah zai kamashi, ita kuma Dada taƙi ta dena faɗa min haka! "
Ta yi maganar tana wani ya mutsa fuska tana kyaɓe ɗan ƙaramin bakinta.Dariya sosai Yarinyar ta kuma bani cikin dariyar na ce "to ke ya ki ke so ta ringa kiranki? "
"Firdausi mana ko Jannat, amma baza ta faɗa ba ita kowa sai ta ɓata masa suna!" Ta yi maganar tana ƙara kyaɓe baki kamar za ta yi kuka.
"To yanzu kiyi haƙuri gaskiya dole a kuma yiwa Dada magana" na yi maganar ina dariya.
"Anty in zamu tafi mu tafi da ke kiyi mata magana" ta yi maganar cike da yarinta.
Tashi na yi ina dariya na nufi
Dining tana biye da ni, na ɗauko ruwa da lemo haɗe da kayan snacks na jeresu kan Babban faranti na kawo kan table ɗin dake gaban Mamen na ajiye, suna ta hirarsu da Anty Maimun.
"Sannu Ɗiyata Allah ya yi albarka"
Mame ta yi maganar bayan na ajiye kayan da na ɗauko.
"Amin" na amsa kai na a ƙasa na koma Dining na ɗauko farantai da chokula haɗi da kufuna.
"Anty ke ya sunanki? " Maganar Jannat da ta kuma biyoni ta shiga cikin kunnuwana, dariya na yi na ce"sunana Anty Jidda."
"Waw Anty Jidda kema sunanki da daɗi" ta yi maganar tana dariya.
