JIDDO (Gidan aurena) Part 10

10 0 0
                                    


          *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

_*PAGE*_ 🔟

________Ɗauke jinjirin yayi ya sauya masa guri, yana faman lasar baki  tamkar wani maye.
Rigar jikinshi ya cire tare da dogun wando, yayi  saura daga shi sai gajeran wando. Ƙaton cikinsa har rawa yake tsabar abinda ke fizgarsa. Lalaɓawa yayi ya kwanta gurin da ya ɗauke jaririn yana kashe fitilar hannunsa ya rungumuta yana shafa abinda ya tafi da dukanin tunanisa watu dukiyar fulaninta da suka ƙara laushi da santsi yana saɓole rigar jikinta duka yana yamutsasu.

Jiddo cikin baci kawai na fara jin ana shafa ni abu kamar wasa na gyara kwanciya ta sai naji ana matsa min dukiyar fulanina da suka cika har suke ɗan min ciwo, dan kafin na kwanta ma sai da nasha paracitamol saboda zazaɓin da ya fara kama ni. Jin dai ana kuma matsa minsu yasa na fara ƙoƙarin buɗe idanuna, hanci nane ya fara shaƙo min tsamin jikinsa dake tashi.

Ƙoƙarin tashi na fara yi, ina laluben fitila duk da na fahimci Babansu Asma'u ne.
Sake mamuƙeni yayi yana kuma matsasu har suka fara zuba,  cikin sauri na tureshi na tashi ina laluben fitila.

“Ke! Jidda menene haka? Ko kinso Allah ya tsine miki ne? ” Suwiɗi yayi maganar da muryarsa da take a shaƙe sakamakon yanayin da yake ciki.

Fitilar da na ɗauko na kuna ina gyara rigata nace“Babansu me ya kawo zancen tsinuwar Allah kuma? Ni da rabo na da kai an dushi wata guda” nayi maganar cike da takaici, ina duba inda ya mayar min da jariri.

“Ni ba wannan ya kawo ni ba haƙina nazo ki bani, bana son dogun zance”

Idano na zaro ina cewa “wane irin haƙi kake magana?   ko ka manta haihuwa nayi ne, na tuna maka! ”

“Karki faɗa min zanchan banza, ai nasan aiki aka yi miki ba da kanki kika haihu ba dan haka ki bani haƙina kawai dan a buƙace nake”

“Sai aka ce maka mace in anyi mata aiki bata jini? Haba Babansu ka ringa abinda ƙoda zai bi mana. An fita dani rai hannun Allah baka damu da halin da nake ciki ba ka hana kowa zuwa anyi min aiki ko dan darajar ɗanka ka leƙa mu,  amma  baka ko je inda muke ba bare wani naka. Duk wannan ba haƙi bane sai yanzu kazo kana cewa na baka haƙinka. Wallahi na gaji da abinda kake min haƙuri na yana gab da ƙarewa” na ƙarashi maganar cikin ɗacin zuciya ina jin sabuwar tsanarsa na bijirowa daga zuciyata.

Suwiɗi dake dafe da mararsa mamaki ke neman kasheshi jin Jiddo na sa'insa dashi yau, karfa wannan karon iyayenta sun ruguza masa aikin da yayi shekara da shekaru be sani ba akanta. Ganin alamar jan ido ko muzurai baza su saka ya samu abinda yakeso ba. Muryarsa na rawa cike da magiya yace “dan Allah Jidda ki taimaka ki bani nayi wallahi ina cikin wani hali, nayi miki alƙawarin duk abinda nake yi miki zan dena kinji..... "

“Nima ina haɗaka da girman ya Rasululahi kaje gurin Ummansu Harisu” na katse masa maganar da yake cikin ƙofula ina juyawa zan koma inda ya mayar min da jaririna Hussain.
Ban aune ba naji ya fizgoni nayu baya na faɗa kansa kokawa muka fara yi, yana faɗin wallahi ban isa ba ai an faɗa masa macen da aka yiwa tiyata bata jini dan haka sai ya ƙwaci haƙinsa ko ta tsiya ko ta tsiya-tsiya.

Cikin ikon Allah, Allah ya bani sa'a na gantsara masa cizo na hankaɗa shi ya faɗa gadon, abinka da shirgege mutum kan ya yinƙuro na suri Hussain nayi waje.

Ɗakin kusa da nawa na faɗa wanda shirgi ne a ciki na banko ƙofar ina jijiga Hussain dake neman tashi, wata iriyar tsanar Suwiɗi na bijiromin. Yanzu wannan shine Malami? Taya mutane ke iya zuwa gurinshi neman temako? Bayanshi duk wani abu da ya dace da faɗar Allah, da Manzon rahama(S. A. W)  bayi yake ba anya mutane sun san halin Suwiɗi kuwa?  Gaskiya ina kokwanto! Malamin ƙwarai taya zai tahu neman macen da yasan tana jini,  har ya dinga iƙirarin sai ya kusanceta?   Duk a zuciyata nake wannan maganar da babu me bani amsa.

Suwiɗi ganin wankin hula na neman kaishi dare, ga mararsa dake daɗa ɗaurewa mai da rigarshi yayi yana ƙwafa. wandonsa ya ɗauka a hannu ya fito yana layi yayi ɗakin  Lubabatu.

Ina jin motsin fitarsa daga ɗakina,  bayan wuce war yan sakanni na buɗe ɗakin da na shiga na koma nawa ina danna sakata. Kwantar da Hussain nayi na kuma tufa masa adu'a, rubar wankan Hussain na ɗauka na kuma ɗaura alwala na nufi gadon da nufin kuma kwanciya. Jin na taka abu yasa na haska fitila gaban gadon ina ɗauke ƙafata daga gurin,  wani zobe na gani kamar azurfa kafin daga baya na ga ya koma ja.   Idanuna na kuma buɗewa ina ganin ikon Allah rikiɗa zoben yake sai ya koma kalar farar a zurufa sai ya koma ja, adu'a na fara karantuwa duk wadda tazo bakina cikin zuciyata kuwa tsorune fal.

Ganin zoben na ƙara girma kuma yana cigaba da sawaya tambarin kan wata dabba ya fito a jikinsa yasa na zabura na rarumu ɗaya daga cikin ruwan rubutun da nake sha,  ina daɗa karantu adu'a na buɗe na juye ruwan kan zoben.
Kafin kiftawar wasu sakanni ya ɓace ɓat waige-waige na suma yi  ina haska ko ina amma banga ko alamar zoben ba saurin hayewa gado nayi zuciyata fal tsoru bacin da nake ji ma tuni ya bar idona. Ga gurin da aka yimin tiyata Sai zafi yake min ɗaga rigata nayi na haska gurin, naga jini ne yake tsa-tsafuwa.  Yadda naga rana haka naga dare dan na kasa komawa baci sai gabannin asuba sannan barci ɓarawo ya sace ni.....

*Chat me On;* 07042808467

*MAMAN NABEELA CE...*  ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now