JIDDO (Gidan aurena) Part 22

9 0 0
                                        


            *JIDDO*
    *GIDAN AURE NA*
               _*BY*_
  *MAMAN NABEELA*

 
*DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION*

*TALLA!  TALLA!! TALLA!!!*

*MAMAN NABEELA DATA SERVECES*

_We buy Data from the afoderble price._

*MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE;*
*500 MB➡️150*
*1.GB ➡️300*
*2.GB➡️600*
*3.GB➡️900*
*4.GB➡️1200*
*5.GB➡️1500*

*MTN DATA BLNC:*461*4# or *310#*
*AIRTEL DATA BLNC: *140#*
*GLO DATA BLNC: *127*0#*
*9MOBILE  DATA BLNC: *228#*
_Sannan da  akwaI airtime   na;MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE_

'''7042808467 Firdausi Rabi'u Abubakar Opay bank
Or 0203632498 Firdausi Rabiu Abubakar Union bank
Sai shedar biya ta 07042808467'''

*Page* 2️⃣2️⃣

“Da....da....dama sai a...an nemi i....i....izini in za'a ne...ne...nemawa mutum la...la...lafiya! Toh...toh ni....ni...ba wanda za....za...zan nemi  i....izinisa,don ha...ha...haka ka...ka...bata ha...hanya ta wuce” Jazuli yayi maganar yana   kallon Suwiɗi daya ƙi matsawa daga bakin ƙofar Salma ta wuce.

“Dan ubanka toh ba inda zaka kai ta, nace ba inda zaka kai ta,  idan kuma kai ne Uban nine Ɗan sai na gani”
Suwiɗi yayi maganar yana ƙara gyara tsayuwarsa a bakin ƙofa.

“Oh!...Oh Toh...toh na...na...naji Old man, a....amma ka....kaga kuwa ji....ji....jikinta! Ka...ka...kayi ha....haƙuri toh a....a....faɗawa ƴan gi....gi...gidansu” Jazuli yayiwa Suwiɗi Babansa maganar cikin lallashi.

“Wai kai dan tsohuwarka maye naka a ciki da kabi ka tadda hankalinka!  In da ba'a yi mata magani ai  da baka sameta a haka ba, dan haka ban amince a faɗawa kowa ba ni nafi dacewa nayi mata magani da kai.....”

Tamkar saukar walƙiya haka suka ga Suwiɗi da yake magana yayi baya kamar wanda guguwa ta ɗiba yayi cikin falo ji kake gwajab ya faɗa cikin kujera haɗi da  wani wawan mari ya sauka kan fuskarsa luuu  ya kwanta  cikin kujerar  kamar mai baci.

Gaba ɗayansu da suke tsaye ganin yana magana yayi baya tamkar wanda aka fuzga suka fara leƙen cikin falon cike da al'ajabi amma basu ga kowa ba sai shi da yake zube kan kujera kamar mai baci, cikin falon  Jazuli yake ƙoƙarin  shiga dan ganin  mai yaja Babansa Suwiɗi haka tamkar a film Asma'u da take daga bayansu idanunta sun sauya kala tayi saurin cewa“ka temaka mana muyi saurin fita da ita dan ceto rayuwarta in ba haka ba yau komai zai iya faruwa da ita”

Juyowa yayi dan ganin waye yake magana dan bai sheda muryar ba sai yaga Asma'u a tsaye a bayanshi, “ke...ke ki ka....kayi magana? ”Yayi maganar yana kallonta kai ta kaɗa masa alamar ita tayi maganar.

Mamaki ne ya kamashi jin da wata iriyar murya tayi magana bai tsaya yaci gaba da tambaya ba ya fita yasa yasa Yaronsa ya taro Mota, bai ɗau lokaci ba sai gashi da Keke napep.

Jiddo duk abinda ke faruwa ina kwance ina jinsu har lokacin da aka samu keke napep ɗin da zai ɗaukeni.
Jazuli da kansa ya ciciɓeni ya fitar dani ya sani a cikin keke napep ɗin yana faman yi min sannu.   Da zamu tafi ina jin jazuli na cewa  Yaronsa ya saki Karnukan a tsakar gidan har ya dawo ya amsa masa da toh'.

Muna fara tafiya Asma'u da kai na ke kan cinyarta na kalla naga ta lumshe idanunta cikin muryata da bata fita har sannan nace “ku kai ni gidan mu cotata bata Asibiti bace” nayi maganar ina duban Salma da naga hankalinta na kain.

“Toh Ammey amma da kin bari anje Asibitin ko da temakon da zasu baki” Salma tayi maganar tana kama hannuna a lokacin Asma'u ta buɗe idanunta tana kallona itama.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now