JIDDO(Gidan aurena) Part36

36 0 0
                                    

JIDDO
(Gidan aurena)
      By
MAMAN NABEELA

DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION

________Cikin harshen turanci yake amsa wayar da ya ke cikin takun da ke nuna shi ɗin ingaraman Namiji ne, direct sashin Mamynsa ya nufa bayan Bodyguard ɗin dake bakin ƙofarsa sun karɓi verifcast ɗin dake hanunsa cike da girmamawa.

Da sallama ya tura ƙofar glass ɗin da zata sadashi da falon yana kutsa kansa ciki.

Mamey dake zaune kan dining wanda  itama fitowarta kenan bada jimawa ba  fuskarta cike da tarin fara'a ta juyo tana amsa sallamarshi. Kujerar da ke kusa da ta Mamey Bintu ƙanwarsa ta ja masa ya kai zaune yana kama hannun Mamey ya sumbata kafin cikin muryar mai ɗauke da tarin ladabi da ƙaunar Mahaifiyarsa  ya ce“Mameyna barka da safiya”

“Barkanka dai Son, ka tashi lafiya kuwa? ” Ta yi maganar tana kallon fuskarshi da ta yi wani irin ja cike da damuwa  ga idanunsa da duk suma suka sauya kamar wanda bai samu bacci ba.

“Lafiya lau Mamey jiya ne bansamu bacci ba sosai” ya bata amsar tambayar da ta yi masa haɗe da ɗaukan cup ɗin coffeen  da Bintu ta haɗa masa don shi sam bai iya ƙarya ba duk abinda zai yi yakan faɗi iya gaskiyarsa ne.

Mamey dake kallonsa bata kuma magana ba don tasan mai amsar da ya bata take nufi ta cigaba da yin breakfast ɗinta.

“Yaya Good morning” Bintu ta gaisheshi bayan ta gama haɗa masa kayan breakfast ta koma kujerarta da ta ke ta  zauna.

“Morning Little yau baki da lecture ne  naga Baki tafi ba? ” Ya yi maganar yana kallon Bintu.

“Yaya sai 12:00,yau zamu fara dana gama breakfast zan tafi” ta bashi amsa cikeda ladabi.

“Ok” ya faɗa yana cigaba da cin abincinsa.

Bintu ce ta fara gama cin abincinta ta tashi ta yi musu sallama ta wuce Makaranta ya rage daga shi sai Mamey a dining  ɗin.

“ABDURRASHID! ” Mamey ta kirayi ainahin sunansa dai-dai lokacin da yake kammala cin abinci, cikin sautin da ke baiyyanar da mahimmancin maganar da zata faɗa.

Ɗago fuskarshi ya yi haɗe da bada hankalinsa kacokan gurin Mamey saboda sanin a duk lokacin da ta kira ainahin sunansa to duk maganar da zata fito daga bakinta bata wasa ba ce.

“Na'am Mamey” ya amsa yana fuskantarta.

“Wannan karon bana tunanin zan iya daure  cigaba da zuba idanuwa ina kallonka babu aure , ya kamata ko don lafiyarka ka nemi mata ka yi aure idon kuma wannan karon ma ni zan samu maka to sai na ji! Don bana fatan ka kuma wata ɗaya ko biyu babu Mata na gaji da ganinka haka Mai Nasarah iyali sune cikar kamalar ko wanne Namiji ” Mamey ta yi maganar  babu wasa.

Tunda ta fara maganar ya yi ƙasa da kansa don yasan gaskiya take faɗa masa cikin muryar tausayi don shi yanzu k da ya ganu wacan Yarinyar ta gidan Tahir baya son sanarwa da kowa har sai ya yi bincike a kanta duka da kasancewarta ƙanwar Maimuna amma yana da kyau ya yi bincike ko don ganin da yayi mata na bata yi kama da buduruwa ba yasan komai a kanta kafin ya kawo maganarta garesu.

“Mamey pls... ”

Ɗaga masa hannu ta yi don bata buƙatar jin irin kalaman da ya ke mata duk lokacin da ta yi masa irin wannan maganar wanda dasu yake amfani gurin dakatar da ita ga abinda take son ya yi,  sannan ta cigaba da ce wa “Mai Nasarah wai shin Matan ne idon ka nuna kana sonsu su kuma suke nuna basa sunka ko mai? Mahaifinka fa kansa ya zuba mana ido ne yana kallonmu saboda yasha yi maka magana kana nuna baka ra'ayin aure wancan lokacin, ga kuma Dada da kullum a gaban kowa sai ta ƙaremin tanadi saboda kai, tana faɗin mun zuba idanu muna kallonka babu iyale sai dai daga wacan ƙasa ka haura wacan ƙasa kamar tsuntsu, Jannat da Ammar  da basu  san Mahaifiyarsu  ba ai ya kamata ka sama musu wadda zata maye musu madadinta” Mamey ta ƙare maganar da kallon yadda yake kamar murmushi.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now