JIDDO
(Gidan aurena)
By
MAMAN NABEELADASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
BARKA DA JUMA'A TO YOUR ALL MUSLIM UMMA
A. RASHED
Direct perking lot ɗin harabar babban companin jerin gwanon Motocin suka nufa, suna gama perkin Bodyguard ɗin suka firfito cike da zafin nama ɗaya daga cikinsu ne ya buɗe ƙofar Motar da ya ke ciki yana sara masa.
Ƙafafunshi da ke cikin cover shose ya fara zurowa yana diresu ƙasan gurin kafin cike da zafin nama ya yinƙuru gaba ɗayan gangar jikinsa ta fito daga cikin Motar.
Kafatanin ilahirin ma'aikatan dake harabar companin da dama tun da suka ga shigowar Motocin da ya ke ciki duk suka bar abinda suke suka nufu gurin, cike da tarin girmamawa suke gaishe shi yana amsa musu fuskarsa cike da murmushi.
Direct babban meeting hole ɗin da ke companin ya nufa wanda tuni kowa ya hallara shi kaɗai ake jira, cikin taku irin na ingarman Namiji ya shiga cikin hole ɗin wanda shigarsa sai da tasa waɗɗan da zuciyarsu babu gaskiya, babu kuma Allah a cikinta, daga cikin ƴan zaman meeting ɗin faɗowar gaba.
Gaba ki ɗaya waɗɗan da ke a meeting hole ɗin Ƴan kasuwa ne waɗɗan da companuninsu ke harkar sarrafa abinci danginsu:shinkafa, fulawa, taliya, makaroni, kuskus, alkama, d.s,
Zamane wanda suke son tatauna abinda zai kawo ƙarshen abinda ke addabar ƙasarmu Nigeria a halin yanzu musamman ma yankinmu na Arewa wato tsadar kayan abinci da suke hauhawa tamkar tashin fulawar da tasha yeast.Sosai zaman yajasu lokaci mai tsahu sakamakon wasu daga cikin ƴan zaman da ra'ayinsu yasha ban-bam da na wasu.
Wanda tsiraru daga cikinsu babu abinda suka sani sai son kansu da rashin tausayin talaka, inda suka nuna su baza su bada goyun baya ba gurin ceto al-umma daga halin da suke ciki.
Daga ƙarshe dai Manyan jagorurin companunin da ke zaune gurin waɗɗan da suka bada goyun baya ga tsarin tuni suka zaftare farashin kayansu da kasu 40%100 inda aka tashi ran wasu duk ba haka yaso ba.Ko da ya fito daga meeting hole ɗin direct katafaren masallacin dake cikin companin ya nufa wanda zuwa lokacin har an fara kiran sallah, alwala ya fara yi kafin daga bisani ya nufi cikin masallacin.
Kamar yadda suka saba muddin yana nan shi ya ke yi musu limanci, a yanzu ma shi ya shige gaba yajasu sallar azahar, bayan sun idar ya ɗau kimanin minti 20 a cikin masallacin yana Addu'o'i kafin ya shafa.
Ko da ya fito office ya nufa inda nan ya fara aikin saka hannu a wasu file-fil, ƙofar Office ɗin akayi noking ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya ce“yeas come in”
Turo ƙofar Tahir da ke tsaye ya yi yana shiga cikin office ɗin bakinsa ɗauke da sallama.
Zama ya yi ɗaya daga cikin kujerun da ke office ɗin haɗe da ce wa“Barka da aiki M.D ya kuka je gida? Yanzu na ke samun saƙon nemana da kake gurin Lukuman” ya yi maganar yana dubanshi.
Files ɗin da ke gabanshi ya ture haɗe da duban Tahir ya ce“ Uhm T.K baƙowar Yarinyar nan ta gidanka na gani nake so, ina so ka yi min bayanin iya abinda ka sani game da ita” A. RASHED ya yi maganar yana kallon Tahir da ya kafe shi da ido fuskarsa ɗauke da murmushi.
“Allah yasa abinda na ke ji ba mafarki na ke ba da gaske ne, A.R da gaske yau kai ka ke faɗin kaga wata kana so? Watan ma kuma a gidana? Kai Alhamdulilah Allah mun gode maka”
Tahir ya yi maganar cike da tsan-tsan farin cikin jin maganar abokinsa.Murmushin gefen baki ya yi wanda yasa beuty point ɗin kumatunsa na lotsawa haɗe da shafa sumar kansa, ba tun yau ba ya san Tahir na ɗaya daga cikin masu son ganin ya yi aure, don tun kafin ya yi auren farko Tahir na daga cikin waɗɗan da Mameynshi ta haɗa kai dasu gurin nema masa auren Sakina, haka kuma bayan rasuwarta yana ɗaya daga cikin masu damunshi da batun sake aure lokaci zuwa lokaci.
