JIDDO (Gidan aurena) Part 19

10 0 0
                                    


            _*JIDDO*_
    *GIDAN AURE NA*
               *BY*
  *MAMAN NABEELA*

*Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y

*MAMAN NABEELA DATA SERVICE*

'''Nazo muku da DATA cikin farashi mai sauƙi da rahusa ga inganci. Domin ƙarin bayani sai ku tuntuɓeni ta:07042808467'''

*Page* 1️⃣9️⃣

_________“Innalilahi wa' inna ilaihirraji'un, Allah mun tuba Allah ka kawo mana ɗauki, wannan wace iriyar musifa ce haka!  Daga wannan sai wannan!  Salma kamata mu maida ita kan kujera” Lubabatu tayi maganar cike da tashin hankali tana kamo Asma'u.

“Toh Umma” Salma tayi maganar tana share hawayen da ya fara ambaliya a fuskarta.

Kama ta suka yi suka mayar kan kujera suka kwantar Salma ta fara tufa mata Addu'o'i...

“Umma Anty Salma kuzu ku ga ɗakin Ammey komai a hargitsi kamar anyi faɗa, kuma naga wata Mage a kusa da gadonta tana shure-shure zata mutu jikinta duk jini..." Abdull da ya fito da gudu daga ɗakin Ammeynsu saboda abinda ya gani yayi maganar yana nuna musu ɗakin.

Da gudu dukansu su kayi ɗakin suna zare idanuwan ganin abinda Abdull ya faɗa.

Ɗakin suka gani suma a hargitse ga Mage  a kwance na shure-shure dai-dai gurin da kufin da aka zubawa Jiddo magani yake babu komai a ciki ya ɓare“La'ila ha'illa anta subahanaka inni kuntu mina zzalumin, mun shiga uku Mage kuma a gidan nan ta ina ta shi....” Lubabatu ta fara  maganar cike da tashin hankali tana yin baya. Sauran  maganar da take ce ta maƙale a maƙoshi ba tare da ta ƙarasa fitowa ba ganin magen ta ɓace ɓat daga inda take.

Salma da ta  shiga kusan tsakiyar ɗakin tana kallon Magen ce ta buga uban tsalle ganin Magen ta ɓace  tayi baya tana  ruƙon-ƙome Ummanta tana kurma uban ihu tana cewa “Wayyo!! Umma wallahi Aljana ce”

Gaba ɗayansu hanyar fita  daga ɗakin  suka nufa har suna gware kai da bango tsabar tsuro da tashin hankali.
Suna fitowa daga ɗakin idanunsu ya sauka kan Asma'u dake ta zabga atishawa idanunta sunyi jajir kamar garwashi.

Lubabatu ya ki ce riƙon da Salma tayi mata tayi tana zare idano haɗe da maƙalewa jikin bango tana faɗin “ wala ya uduhu hifzu huma wa huwal aliyil azim” tana fashewa da kuka ta rufe idanunta gam.

Salma  da Zainab kukan suka kece dashi suma suna kallon gurin da Asma'u ke kwance tana ta zuba atishawa.

Sai da tayi atishawa ta kai goma sannan ta dena ta fara ƙoƙarin tashi zaune.

Dukansu gurinta su kayi ganin ta tashi zaune tana dafe kai “Anty Sannu! " Zainab tayi maganar tana ƙara matsawa kusa da ita.

Cire hannunta tayi da ta dafe kai tana kallonsu cike da mamaki tace “mai ya sameni? Ina Ammeyna! Ba kuga  wata baƙar Mage zata shiga  ɗakinta ba? Nima da na fito daga kicin na ganta zata shiga,   Kuzu muje karda ta cotar min da Ammeyna!” tayi maganar tana miƙewa tsaye da sauri tana  waige-waige haɗe da dafe kanta da yake sara mata .

Rasa wanda zai bata amsa a kayi sai tashi suka yi Salma na ƙoƙarin tarota ganin tana neman faɗuwa suka nufi ɗakin.

Suna shiga wani irin juyewa idanunta suka yi suna  sauya launi tana ƙarewa ɗakin kallo tayi gurin Ammey tana jijigata idanunta ne suka ƙara rikiɗewa da wani irin ja cikin kakausar murya ta fara magana da wata  iriyar murya da a tarihin rayuwarsu basu taɓɓa saninta da ita ba cike da gar-gaɗi haɗi da alwashi tana cewa
“duk randa kuka kuma gigin zuwa ku cotar da ita sai munga ƙarshenku azzalumai.

Ƙwalalo idano Lubabatu da Salma harma da su Zainab suka yi suna kallonta kafin su fara kallon-kallo  tsakaninsu
“kar dai Asma'u Aljanu gareta” Lubabatu da ta fara ja baya ta riya a ranta.

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now