INA AMFANIN BARIKI?
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS).AKA DIVAA
divaa_doveysdiaries
group. ❤7 December. 2017
(2)
A office dinsu Abba. Abba ne zaune da kanin shi kawu Sani.. Suna tattauna wa akan matsalar nasiru. Sun kasa game kanshi. A takaice ma sun kasa game me yake aikatawa. Su dai sun San baya shaye shaye.shikuma yace baya aikata wani aiki na assha.Amman sun kasa gane me yake aikatawa. Gashi duk iya binciken su sun San baya zuwa club.toh ina yake zuwa da daddare?...
Wannan tunani shi yafi komai daga musu hankali..Amman sun dau aniyar binciko me yake aikatawa da yake fita da dare. Sannan kuma Dole a mashi magani. Saboda indai kana son kaga bacin ran nasiru toh kamai zancen aure.
Kawu sani ne ya kwantar wa da yayan shi hankali yace mashi zai samu yadda zaiyi ya gane me nasiru take ciki.
Karfe shida na yamma nasiru ya bar office dinshi.hanyar gida ya dauka kai tsaye.. Cikin tafiya yake a hankali saboda tunani da yamai yawa. Yana son ya zauna a gida kwanan nan saboda ya cire shakkun da iyayen shi suke dashi akanshi. Hanyar gida ya dauka. Wayar shi ce tayi kara yana dubawa yaga Booster.
Booster abokin nasiru ne Wanda suka hadu a barikin sojoji na kaduna. Kankace meye suka kulla abota tunda all together..
"Booster!.. "
Yace cikin isaBooster ya amsa
"How far.. Jiya shiru ba labari. Ina missing naka anab fa. Harkan nan nafi sonyi dakai kafi kowa sani. Amman saika na basar wa.. "
Dariya yayi sannan yace..
"Wallahi Nida Abba ne. Shiyasa kaji no tsit. Amman no worries Nina a dame nake wallahi. Kawai dai kasan ni ba'abun da banaso irin naga na bata ran Abba.. ""Wheewe.. Aishi yasa kake samun problem. Shi Abba bazai gane irin dadin harkan nan ba. Kaima kasa shi a ranka ne shiyasa. Amman kacire wani tsoro muji dadin my kawai.. "
"Yo yo yo yo... Easy, we are talking about my dad here!.. So Maintain. "
Hakuri booster ya bashi dan yasan yanzu zasu haura. Dan duk abun nasiru yaki jinin a taba mashi iyaye.Shikuwa booster baya son nasiru yabar shi shiyasa yake mai biyayya dandai su cigaba da tsula tsiyar su yadda suka saba.
"Toh yanzu kana ina?.. "
Booster ya tambaye shi"Na shiga gida ne. Se kuma gobe in Allah ya yadda.. "
Booster baiji dadi ba. Amman yafi kowa sanin halin nasiru. Magana daya yakeyi.. Haka ba dan booster yaso ba ya hakura ya sauke wayar bayan ya yi sallama da abokin nasa.
********
Kawu sani yana ganin yamma tayi ya samu machine din megadin gidan su nasiru. office din nasiru ya tafi bayan yayi parking motan shi a gidan. Daidai sanda nasiru ya fito daga office dinsu. Ba bata lokaci yabi bayan shi a nesa nesa. Saida yaga ya shiga gida yayi parking ya shige side dinsu sannan shima ya shigo ya ajiye machine din ya shige gun su Abba..
Ba jimawa nasiru ya shigo Palon cikin natsuwa da girmama iyayen shi. Gaishe su yayi cikin jin dadi da nuna ba abunda ya faru su abba suka amasa gaisuwan sa..
Yar hira suka taba. Nasiru ya tashi yayi dakin shi.. Kwanciya yayi yacigaba da tunani.. Booster ne ya kara kiran shi sukayi year hirar su daban san me suke cewa ba.
Ko kafin karfe goma booster ya kira nasiru yafi sau biyar. Nidai na rasa wannan waya ta me sukeyi haka duk minti.Dole in Sa ido nima dan gano wani irin shakuwa ce tsakanin nasiru da booster. Zamu samu amsan abubuwan da suka shige mana duhu. Amman fa said naji shin menene tunanin ki akan iron shakuwar nasiru da booster. Sai kuma menene aikin da nasiru yake aikata wa a ban kasa..
Ga me neman shawara kan duk Wani Abu da ya shafi mata,ko magani ,yar tanbaya akanki . Da sauran abubuwa. A iya neman mu akan wannan lambar ta whatsapp.
08165992806.Aunty divaa..
Ladies only!
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin