part 26

771 45 0
                                    

INA AMFANIN BARIKI?

              NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

AKA AUNTY DIVA.

Divaa_doveys_diaries group one ❤

Divaa_doveys_diaries group two ❤

3rd March.2018

__________

(26)

Booster ne kwance a cikin motar shi yana tunanin kiran khairiyya..dan tsaki yayi kawai ya kira wayar.har ta karaci ringing inta ba'ayi picking ba..A lokacin kuwa khairiyya na zaune tana kallon wani film din Korea me dadi.ga wata soyayya da akeyi a cikin film din.haka kawai se taji dama itace...daki ta tafi ta dauki wayar ta .se taga missed call.da murnar ta ta kira dan tayi tunanin pinky ko wali ne suka kirata..

Dialling number din tayi kai tsaye da murnar ta..

Booster ne yake ta faman kallon waya yana tsaki.yana mamakin dalilin da yasa Bata dauki call din nata ba..Kallon wayar ya sake yi tare da jan wani siririn tsakin..kan ya dire wayar ta fara ringing..bai jira wasa ba ya daga yana cewa

"Haba heart beat..ina kika shiga haka?"

Dan duum tayi tare da Kallon wayar ta kara ganin number din..cikin sauri tace.."ohh sorry wrong number".kan ya sake magana ma ta kashe wayan...

Kallon ta maida wa hankali ta cigaba ba tare da da tunanin komi ba..dan dai tasan Bata kira wata bakuwar number ba.ko su pinky wayar school suke using in zasuyi waya..daga kafadun ta tayi cikin nuna halin ko a jiki na..

Shikuwa kara dialing yayi.harta yi cutting shiru..text yayi mata kamar haka.."heart beat in ba ki so na mutu ki picking call dinnan..mijin ki ne fa.."

Message din na shiga ta duba..tana gani tayi smiling tace "hmm uncle kenan.."

Wayar ce dai ta kara shigowa .."hello .."
Tace tana daga wa.

Dan duniya booster wani kasaitaccen murmushi yayi yana fadin "aww yanzu da bance nine ba.da se ki share ni ko..kina son na rasa raina ne?"..

A hankali tace.."Ah ah..kuma ai nasan ba wanda na kira.shi yasa nayi tunanin wrong number ne..ina yini.."

Dariya yayi sannan ya kara kwantar da kujerar motar shi da cika da kamshin turare ga hayakin cigarett ga sanyin Ac. . Yar waka yake ji ta hausa wadda musamman saboda soyayyar khairiyya yake ji yake mugun sonta..akan haka yasa dole seda divaa ta koyi gurin..

Be samu damar amsa gaisuwar ba .se kawai ya tsinci kansa da fara cewa.."ka duba girma irin na duniya..ta taru da sanadi na soyayya.kanta akan rasa lafiya ai fada ai rasa rai harda dukiya. nima na fito koma na bubbugo kar inzama rago a soyayya.kece na hango na biyo ta bango soyayya jigo ku bani hanya.gani a kogo ku bani bargo na sonki na shigo ya zamo na fara..zan rayu dake zan mutu dake .abadan dani dake zamu zauna.."

Har zuwa inda ta fara.itadai khairiyya shiru tayi tana nitso acikin soyayya.ashe dai itama uncle dinta ya iya irin soyayyar su walida da gee boy.dan yadda walida ke basu labari waka suke da saurayin ta a waya..abun ko yayi mata sugar indai haka ne

Kawai se ta tsinci kan ta da fara cewa.."uhh uhh zuciya ta da taka abokan juna.dan basu basu rabuwa ko agun kwana.ina a farke ko a cikin barci na.kai nake tunani cikin kwakwalwa na.da wani zaya tsaga jinin dake jikina da zayaga naka yana ta kwarara akan kauna na manta kaina..."

Chak ta tsaya kuma dip ta kashe wayar.hakanan taji tana sha'awar ganin shi..wayar ta ce tayi ringing tana duba wa taga uncle.A ranta take fadin "uncle kenan.."

Kin dauka tayi saboda kunya duk ya kamata.kara kira yayi sannan ta dauka tayi shiru. .

"Yan matan boarding.."
Ya fada cikin zolaya.

"Hmm" kawai tace tayi shiru ..

"Kin dawo lafiya?.."
"Lafiya Lau. ."
"Ya kika baro su walida?"
"Duk lafiyan su kalau.har ma kuka nayi da Muka rabu.."

Smiling yayi yace. ."aww yanzu kuma kin daina kukan gidan se nasu ?"..
Cewa tayi "ah ah.duk inayi mana.."

Anan dai dariya ta bashi sosai.."yar magena kenan..ina bukatar jin wata a kusa dani..kisser na na bukatar jin wasu a kanshi ..sannan kirjina na bukatar jin dan nauyin nan a kanshi.."

Itadai bata gane duk ba..se kawai tace hmm.."

A haka hirar tasu ta kasance inya debo kaaatotuwar magana se tace "hmm"..A haka ya kyaleta tare da alkawarin kiranta da dare..

A bangaren booster tana kashe wayar ya cigaba da wakar..wato wata irin murya ce da khairiyya me dadin saurare..cikin shauki da jin dadi ya kunna motar shi ya shiga gari..dama lokacin yamma tayi..

_________

Bayan yan tunane tunane taga gwara ta tafi gun su gwaggo..A tsakar gidan da ya raba bangarorin su ta same su a zaune suna gyaran zogale..zama tayi tadan jinginu da jikin gwaggo ramatu..tana kallon yadda suke gyarawa. Ajiyar zuciya tayi sannan ta gaishe su..gwaggo A ce tace mata.."har kin gama kallon ne?.."

"Ah ah wallah gwaggo.gajiya nayi shine na fito.."

Gwaggo R ce tace.."gajiya kuma kamar wadda tayi wani aikin?.."

Murmushi tayi sannan ta mike..sanye take da riga da skirt masu kyau ash .da yar hular ta a kan ta..A hankali ta nufi bangaren Alhaji .tana shiga ta same shi yana karatu. Kusa dashi ta koma ta kalli inda yake karantawa ta tsaya tana sauraren shi.yana kaiwa karshen Ayar.ya tsaya ya shafa sannan yace .."khairiy ta ya ake ciki.."

"Ba komai tace"..sannan tace "ina yini.."

Murmushi yayi sannan yace lafiya.."ina madara?.."
"Tana nan amman dai yau bana son nasha.."

Mamaki ta bashi saboda yasan yadda take da madara..se yace "toh se ne kike so"..tana rabe a jikin shi tace .."ummmm"..na gaya maka?
"Kwarai kuwa.kinga inkin gaya mun se nasa a siyo maki.."
"Tohm inason tsiren kan kwana irin wanda baffa yake siyo mana.."
"Dame kuma?.."
"Da ice cream irin wanda uncle yake kawo mun..amman ba na kofi ba.."

Alhaji yana mamakin irin son da yakewa khairiyya.jinta yake kamar Abdullahi ko sa'idu.dan a zahiri duk cikin jikokin sa dama yafi shakuwa da nasiru.toh kuwa a yadda yake jin son khairiyya a ranshi ya zarce  na nasirun..

TBC

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now