INA AMFANIN BARIKI ?
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
AKA AUNTY DIVAA DIVAA_DOVEYSDIARIES NOVELS GROUP ❤
4th February.sunday 2018
Sorry lovelies for keeping y'all guys waiting.. I've been busy busy😂..nyways bare with us p.s..
Loves your love, care and concern..
(14)
_______Da sallamar shi ya shiga dakin ya ganta a kwance.
Dan mayafin da ake rufe fuska dashi na amare ma ita ta cire nata tana kwance tana kwalla.
Chan ta tuno su gwaggo sunce mata ta kwantar da hankalin ta gidan tane ita kadai..
Tasha su madara da Milo ga cornflakes dadi indomie..se kawai ta tsinci kanta da murmushi..
Murmushin ne ya tafi da imanin shi.wanda yayi tunanin musamman dan shi aka yi..
Se daya kara sallamar sannan ta amsa masa tare da tuno nasihar su gwaggo ..
Da sauri ta sauko kasa ta gaishe shi dadi sosai yaji ganin yanda tayi.murmushi yayi tare da cewa amarya khairiyya. Kin wuni lafiya?
A hankali ta amsa cikin muryar ta me Kaman ta yar mage..
Kai tsaye kuma ta tashi ta fara kokarin cire kaya sedai rigar zip dinta irin har saman wuyan nan ne. Haka ne kuma yasa hannun ta ya gaza kaiwa.
Bata bata lokaci ba ta juyo bayan tare da cemai.."uncle yimun zipping dan Allah.."
Kallon ta yayi.yayin da wani abu ke shiga zuciyar shi.
Bedai san ko mene ba.haka ya kama zip din ya is mata shi kasa.
Dan karamin bayan ta ne ya bayyana.ga wasu kwantattun gashi wanda suka taho tundaga kasan keyan ta har tsakiyan bayan ta.
wannan kadai se da ya sa tsikar jikin nasiru tashi..amman kan ya karasa jin dadin kallon da bayan har zaks ya fado masa a rai.nan da nan ranshi ya baci..
Ita kuwa koda ya mata zipping se ta cire rigar ta ta zauna da slit da vest..
A hankali ya samu guri ya zauna sannan yace mata "kinci abinci?"
A hankali ta girgiza Kai alamun bata ci ba.
Da kanshi ya tafi kitchen ya dauko plate da cups..grilled chicken ce da fresh milk se ruwa..
Haka suka sauko suka ci suka koshi. Shidai kallon ta kawai yake.duk wani motsin ta akan idanun shi.gashi komai kara burge shi yake..
Ita kuwa madaran tafi sha se tumatir din cikin kazar.. shirin tashi take ya ruko hannun ta tare da fadin "ina zuwa?"
"Hannuna na zan wanke.. "
"Me kika ci toh?.oya zauna kici abinci da Allah.
"ya fada da dan karfi saboda da ya ganta se zaks ya fado mashi a zuciya.
Vest din ta daga da hannun ta me kyau tace "uncle kalla fa ciki na"
Cikin ya kalla ya ganshi a dame..a ranshi yace "yama za'ai abinci da yawa ya shiga nan?..dama ba maganar daukan ciki ma"
Kallon roban madaran shanun yayi yaga Tasha shi sosai.sai ya kyaleta.hanyar toilet tayi cikin tafiyar ta me daukar hankalin nasiru. Gashi ba wani diri gare ta ba amman Haka nan yaga tafaye mashi sauran matan..
"Khiriyya Kiyi alwala" yace mata bayan ta Kai toilet din.ba musu tayi dan su gwaggo sunce mata ta yi duk abunda ya sa ta.
Tashi yayi ya tartare kayan ya kai kitchen sannan ya dawo ya cire rigar saman kayan shi.
Dai dai lokacin ta fito daga toilet duk ta jika jikin ta.
Kallon ta ya tsaya yi gashi slit din ya manne wa siraran cinyoyin ta.haka ma vest din ta jike sharkaf..
Ga gashin giran ta da na ido tare da na keyan ta da gaban gashi sun kwanta lup.
A take yaji wani abun na taso mashi.."jike wa sukayi wallahi.."
Ta fada da sauri gudun kar ya tuhumeta..Dariya ma ta bashi.amman se ya share kawai yace "chanja kayan toh.sallah zamuyi"
Nan take ta cire rigar ta ta bude wardrobe din da aka dan sa mata yan kayayyakin ta tana neman abun sawa..
"Ikon Allah ".yace a ransa sannan ya jasu Sallah.ya mata Addua sosai ya Dan tanbayeta. A nan ne ma ba duk amsoshi ya samu ba.amman Alhamdulillah
Gadon ta hau ta kwanta abunta ta fara bacci. Koda yaga haka se ya dauki babbar rigar shi da wayoyin shi ya tafi dakin shi ya chanjo kaya ya dawo..
Gadon shima ya hau bayan ya kashe fitila.dake batada nauyin bacci se ta bude ido.a hankali ta matsa jikin shi ta cigaba da baccin ta
TBC
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin