part 41

639 44 0
                                    

*INA AMFANIN BARIKI??*

                   *NA*

*UMMKULTHUM AHMAD  (MRS)*


AKA AUNTY DIVAA

*DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ONE❤*

October 14 ,2018
Sunday.

________

41

Assalaamu alaikum readers da doveys..da fatan kowa yana lafiya,bayan dogon hutu da na samu gani na dawo insha Allah da ya karfi na wanda zamu dora daga inda muka tsaya..

Ina fatan zan samu goyon baya da soyayya kamar yadda aka saba.da bazar ku muke taka rawa..ku cigaba da binmu a cikin wannan labari me suna INA AMFANIN BARIKI.wanda yake duba akan rayuwar matasan zamani har ma da wasu maza da matan auren. Allah kasa mu fi karfin zuciyoyin mu ,masu irin wannan halin kuma Allah yasa su gane.

_______

Aminu kano international airport 05:45 pm ..matafiyan suka sauko wanda suka taho daga Ireland.cikin matafiyan kuwa harda Adriana wadda ke dauke da cikin Nasiru.
Tana sauka ta kira abokin nasiru ta fada mai sunyi landing.nan ya ce mata ta samu wani a Airport ta tambaye shi yadda zatayi da inda zata .A cikin wayan da suka sauka ta samu wani.da alama jira yake a zo daukan shi.nan ta mai bayanin office din Da take nema yace mata ai yasan office din .yace mata in anzo daukan shi se ta samu  taxi ta bi bayan shi zai nuna mata .hakan akayi kuwa har NNDC .anan ta shiga tayi bayanin wanda take nema.sabo da yanayi na tsaro suka ki bata wani information akan Shi.

Nan ta kara kiran adamu ta fasa mashi yadda sukayi da yan office dinsu .daman yasan haka .shi yace mata tace matar shi ce ta kawo mashi surprise visit ne.hakan ta fada musu kuwa nan danan suka bata information me kyau akan shi.a paper tace a ruguta mata saboda bayanin baze yiyu ba..

Ta musu godiya ta fito inda taxi driver dinta ke jiran ta.address din da suka bata ta mika wa me taxi din ya karba.Kallon shi ta tsaya yi inda ya ga yasan gurin .nan ya tuka taxi ba bata lokaci suka iso gidan su Nasiru..

_____

Love birds kenan ana ta tabka soyayya ..wato wani irin kallo da Murmushi da suke sakar wa junan su abun se wanda ya gani..

"I love you soo much kissy .."
Ya fada tare da sakin ajiyar zuciya me nauyin gaske.

"Tsakanin ka da Allah?"
Ta tambaya tana dariya

Shima dariyar yayi dan irin tambayar yarinta tai masa.

Tsam ya tashi daga inda yake yaje gunta ya tsugunna, kirjin shi ya dafa da hannun ta yace "meyasa ko muna tare bana gajiya dake ne,kullun bakya isata.na mallake ki amma har yanzu banda nutsuwa..."

Kafin ya karasa magana ta dafe mai baki."yi shiru mine ,abunda nakeji har tsoro yake bani..amma fa nasan zan iya rayuwa ba kai.."

Haka suka cigaba da wasa da dariya suna ta tsokanar junan su cikin soyayya .kai abunfa ya burge divaa..

_____

Taxi driver ne ya wa me gadin gidan su nasiru magana .ya kuma mai bayanin cewa farar mata na neman nasiru.Koda yaji haka yace ai nan dinne .anan me gadin ya shiga gidan ya fado wa su umma maganar.Abba ma na nan,dan haka yana jin haka  da kanshi ya fito waje ya ga Adriana bahdt girl..nan take farin ciki ya kamata dan ganin fuskar nasiru a ta abba.shiko abba kanshi ne ya daure na ganin baturiyar budurwa kuma tana neman nasiru..Nan ya mata magana ya tabbatar da cewa nasiru take nema .nan ya sallami taxi driver din suka shiga ciki..

A nutse umma ta karbi Adriana wadda izuwa yanzu ta basu labarin rayuwar su da nasiru a kasar Ireland. wanda ta ruka Murmushi wanda yake nuna farin cikin da take ciki.ita bata wani kawo tayi ba dai dai ba..

Abba da umma kuwa sun shiga tashin hankali mara misaltuwa Amma basu nuna mata ba..dan karfin hali har daki umma ta kaita ta shiga toilet sannan umma ta yi mata chips da egg da sausage ta bata da tea..har a lokacin Adriana se tambayar ina nasiru yake take yi.

Abba zaune cikin bacin rai ne ya daga waya ya kira wata number.shin number wa ya kira ?

_______

Cikin shaukin kauna nasiru ya tsinkayi wayar shi na ringing.kin tashi yayi ya dubata .ko kafin wani motsin wayar khairiyya ta fara kadawa .dubawa tayi tace Abba ne.dauka tayi cikin sallama da kamun kai ..

"Assalaamu alaikum.."

"Wa'alaikissalaam .khairiyya ,ina nasiru?.."

"Uhm uhm gashi nan.."
Ta fada cike da kunya.

"Hello Abba.."
Nasiru ya fada cike da girmama wa .katse shi yayi da fadin.."ina neman ku kai da matar ka yanzu.."
Be tsaya jiran komai ba ya kashe wayar sa .ba shakka nasiru ya shiga rudani .gaban sa ya fadi .ya shiga wasi wasin anya lafiya..tashi sukayi tare .shi ya chanja kayan shi zuwa wanda ya cire sannan suka fita suka nufi gidan.

Tbc

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now