part 43

636 43 0
                                    

*INA AMFANIN BARIKI??*

                   *NA*

*UMMKULTHUM AHMAD  (MRS)*


*AKA AUNTY DIVAA*

*DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ❤*

October 16,2018
Tuesday.

_______

43

Baya baya umma tayi ta zauna a kan kujera ta rafka tagumi..bata so ta zubda hawaye wa yaron nata ..amman kam ya sosa mata zuciyar ta.

Wato duk irin tarbiyar da suka bawa yaran su seda aka samu wanda ya jawo masu abun kunya.nasirun ta shine da aika aika irin wannan.ko shakka babu zuciyar ta tayi nauyi kamar an kulle ta.tunani yawa kanta yawa.ya zasuyi yanzu .gashi da matar shi da komai amman ya rufe ido ya sheka wata katuwar karuwa ciki..toh wai ma in sonta yake kuma yana niyyar auren ta kamar yadda ta fada musu me yasa be fada ba.ai gara ya aure ta akan wannan dabbacin da yayi..
Wannan duk umma ce take saqa da warwara .cikin haka taji Abba na fadin.."wallahi nasiru ka bani kunya.kaci amanar da take tsakani na dakai.kamun abunda ban taba tunanin ko da abu me kaman shi ba.amma ka sani wallahi ko a gaban Allah na fita ,na baku tarbiyya wadda ta isa ta hanaka bin irin wannan hanyar.amman ka kauce ka zabi ka bita .bazan maka baki ba .amman Allah da kanshi yasan yadda zaiyi da kai.sannan ka shirya fuskantar hukuncin da ya hau kan ka wanda kana musulmi kuma ma'auraci kaje kayi *zina* (wa'iyazubillah).bayan haka a yanzu ba sai anjima ba zaka bani duk wani credit cards dinka ,zaka ban motar ka ,passports dinka ,da takardun duk wata kadara har  mukullin sabon gidan ka da na nasarawa sannan a karshe zaka bani takardar khairiyya...
Abba ya gama cikin kuka me kashe zuciya

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun..Abba ,Abba kayi hakuri" ita ce kalmar da nasiru yake ta furta wa cikin matsanan cin kuka .

umma ma zuciyar ta ta karye saboda haka kukan take ita na.se Adriana da take ta zare ido tana kallon su.ita dai bata san me ake cewa ba.amman ko tasan ba lafiya kuma ta gane cewa ita tajawo wannan conflict din .

A hankali taje gun abba ta riqe hannun shi cikin turancin ta take cewa .."what's happening,please tell me what's wrong.."
A hankali ya raba hannayen su sannan ya fada mata cewar  akwai cultures,norms da values na ko wane society,therefore abunda Nasirun yayi is a don't of our society (taboo).

Tabbas ta gane abunda yake nufi tunda suma suna da do's and don't's dinsu ..amman se tace dashi .."he made a mistake,but it was out of love ,I mean we love ourselves and we're ready to set things straight.right babe?.."

Wani tukukin bakin ciki ne ya kama shi a zuciyar shi yace "I'll deal with you .."

Cikin haka umma ta shiga daki dan wani irin Abu da taji kanta na manta.Abba na ganin haka ya bita ciki dan ana dadewa kan ranta ya baci .amman in ya baci kuma har faduwa take yi..

Nasiru ne ya fara wa Adriana magana a sanyaye.."you see what you've caused,why did you have to do come all the way here?

Ko daga kallon fuskarar Adriana kasan maganganun nasiru sun bata mamaki..

"Babe,are you serious?,.no wait, do you mean to say you're done with me?,what about our baby?.." ta fada tana matsawa gun shi ..

"Baby you said ?,did we agreed on having a baby? Don't tell me bull shit.I'm not the one responsible for it and I won't take any responsibility.."

Cikin hawaye da mamaki a fuskar Adriana tace..
"But babe I love you,and I thought you loved me too.."

Ko kan ta karasa ya katse ta da fadin "what,me ?..no way I never loved you and I will never ..you were just a play boy and never will you be my baby mama..the child you're carrying in there got nothing to do with me. .don't be late and find that bitch you open your inn to.."

Tsugunnawa tayi ta fara kuka tare da chusa hannayen ta a cikin gashin ta abunka da baturiya daman daga gunsu ake kwafo wannan styles din .toh wannan na asalin kenan .

Abba na shiga ya kamo umma ya rungumota tare da fadin .."saratu kiyi hakuri dan Allah kar abun ya mun yawa.ki kwantar da hankalin ki.jarabawa ce kuma in Allah ya yarda zamu cinye ta .."

Ita dai shiru tayi mashi take kukan ta tana jin ciwo mafi tsanani a ranta .hmm uwa kenan.ta haife shi be san kanshi ba yana ta wutsil wutsil da kafa ,ya girma ya san kanshi.shine har ya iya yiwa mace cikin zina. Hmm kawai take cewa saboda tsananin mamakin da ya ishe ta.

TBC

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now