*INA AMFANIN BARIKI??*
*NA*
*UMMKULTHUM AHMAD (MRS)*
*AKA AUNTY DIVAA**DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ❤*
October 17,2018
Tuesday__________
44
Hakuri dai Abba ya riqa bawa umma. Shirun dai shi tayi ta nemi guri ta zabga tagumi.shiko Abba gun nasiru ya koma ya karbe credit cards dinsa da car key dinsa.ana haka se ga kawu sani ya yo sallama .
Yana shigo wa ya san cewa ba lafiya ba .Abba kuma be so kawu yazo a lokacin ba..aiko kamar baki se ya fara cewa..
"Toh,yaya barka da dare.nasiru lafiya,yaya lafiya ?.."
Duk a tsaye yake tambayan fuskar shi da mamaki."Yo ina fa lafiya,danka ya auro mana baturiya ba tare da sanin mu ba?.." Abba ya ya fadi
"Subhanallahi ..nasiru garin yaya haka?.." kawu sani ya tambaya yana matsawa kusada nasiru.
Shi dai nasiru be ce komai ba.Se Abba ya kara da fadin ..."ai se ka tambaye shi nasan kai watakila ya gaya maka .."
Abba yayi kokarin boye gaskiyar al'amarin tunda ko ba komai sirri sirri ne.kuma kawu sani nada mata duk inda ya gaya mata magana ta bazu.wannan shine dalilin boye masa gaskiya.
"Nasiru kaje ka kawo mun takardun yanzu yanzu.."
Haka babban yaro nasiru ya tashi jiki ba kwari ya tafi debo abunda aka ce ya bayar.
Yana fita yayi tunanin kiran booster ya gaya mai halin da ake ciki .se yayi tunanin ya kyale shi kawai.niko tunda nasiru zaije dauko sako ai gwamma na tafi gun booster muga ya nashi bangaren.
_____
A sama booster ya shirya wa wannan yarinya mugunta dan yace fa duk a kanta zai fanshe tsawon lokacin da yayi missing harkoki..
Tsaleliyar budurwar me suna maryam kamar dai yadda ta sanar wa booster tana zaune a kan kujera tsaf da kayan ta a jikin ta ..ganin haka yasa booster yace .."maryam Mene na jan aji bayan duk mun riga mun san me ya hada mu a nan gun..kar kiji kunya ta kinji koh. .."
Bata amsa ba amman dai ta tashi ta cire kayan nata .amman me?..da zarar ya kalleta se yaga wani zindiqin kato da wata irin halitta me ban tsoro ..murmushi yayi ya goge idanun shi yace .."not now please.."
Dake wa yayi ya kara Kallon ta. Ko shakka babu abunda ya gani ba karya bane,ba kuma gizo ba.
A hankali ta fara tunkaro shi. Se gashi yana baya baya a hankali har dai ya fara gudu tana bin shi .haka ya riqa zunduma ihu a dakin.ya kai ga kofa amma ko kusa kofa taki buduwa har wannan yarinya tayi nasarar kamashi .aiko ba ta bata lokaci ba wajen bashi abunda yake nema.se gashi booster man yana ihu yana shure shure yana kuka na neman taimako amman kamar hadin baki se sanda ta gama da shi ta bace bat.sannan mutanen gefen dakunan suka ji ihun shi suka shigo suka ganshi yayi wani irin gumi .
Tanbayar shi ake me ya faru amma inaa ba bakin magana haka sukai ta mamaki da tambayar yarinyar da suka shigo tare. Kowa yace be ganshi da kowa ba.se wata yarinyar da me suna tina tace shi kadai ne ya hawo ya shiga dakin sedai ta ganshi yana ta magana shi kadai ..
Mamaki fa ya kama mutane ba dan kadan ba.kamal wani abokin su ne a nan club din .shi ya dauki wayar booster yaci sa'a ba password nan da nan ya kira number nasiru..
Bugu daya ya dauka tare da fadin .."hello Aminu.." kai daji ka san a gajiye yake
"Ba shi bane ba,Kamal hadejia ne.." kamal ya fadi
"Okay ..kamal ya ake ciki.ina yake?.."
Nan kamal ya labarta wa nasiru halin da ake ciki.ai hankalin nasiru ya kai kololuwa wajen tashi..salati kawai yake yi.shi ba abun ya tafi ba yana cikin rashin natsuwa shima.
"Uhm kamal ku kawo shi Aminu kano mu hadu a chan yanzu insha Allah.."
Nasiru ya fada cikin sauri ya katse wayarDai dai nan ya isa gidan ya dauko wani briefcase wanda duk wasu documents suna ciki.
shi yanzu a halin yanzu matar shi kawai yake so a bashi ko ya rungumeta yaji sanyi a ransa..(zaka ga matar ka ganin idon ka)
A gida khairiyya ta tashi daga bacci tayi sallah tana jiran taga ta ina her man zai billo.dan tayi wani irin mafarki wanda ta tabbataar da da hali se ta hukunta kanta nayin wannan mummunan mafarkin akan her man..
Ita kuwa Adriana tana nan a zaune cikin tsoro da mamakin kalaman nasiru a gareta..
Abba da kawu sani kuma suna tattaunawa akan laifin da nasiru ya aikata.shi kawu yace ..
"Yaya dan Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka,kuma ka sassauta wa yaron nan .tunda ma har yayi tunanin yin auren ai ya ma yi tunani mai kyau.kuma yaya kasan gado fa girman 'da' .ai kasan yaya zaiyi wuya ya jure zaman kadaici shi yasa yayi wannan auren .kuma fa yaya da a lokacin ya fada baza a barshi ba.dan Allah yaya a yafe mashi a sassauta mashi .."
A zuciyar Abba fadi yake dama auren yayi da nima nafi son haka.. A fili kuwa cewa yayi .."toh me da kazo ka tsareni kana mun bayani harda ba'a ko bakar magana..ni banyi fushi dashi ba amma dole na nuna mashi kuskuren shi dan gaba ya kiyaye yasan cewa mu dinnan muna da amfani a rayuwar shi.."
Cikin haka nasiru yayi sallama, har ya zuqe lokaci daya.Abba ya nufa ya mika mashi briefcase hade da makullin gida da mota .
Ko kallon shi Abba beyi ba yace ina takaddar khairiyya?
A rikice kawu sani da nasiru suka kalli Abba ..tuni har nasiru ya fara kuka a kasaw ya fadi ya fara kuka ya hade hannayen sa yana fadin ..
"Abba dan Allah kayi hakuri kar ka rabani da ita ,dan Allah Abba.."
Abba ne yace.."da ka san baka san ka rabu da ita ka auro baturiya ?,ai kaga ko a haka ka nuna mana auren dole muka maka,toh se ka bar mana ita ka dauki baturiyar ka ka bace mun da gani.."
"Abba dan Allah dan Annabi ka H
Yafe man wallahi sharrin shaidan ne ,wallahi Abba nayi nadama da da nasani,wallahi Abba abun ya dameni nima wallahi sharrin zuciya ne dan Allah kar ka raba ni da ita Abba, wallahi bazata iya rayuwa me dadi bani a kusa da ita..kayi wa Allah kamun duk wani hukunci Abba amman banda rabani da khairiyya.."Adriana kam ta kasa daure wa itama kukan ta cigaba tare da dawo wa ta. Kwanta a jikin nasiru tana taya shi bawa Abba hakuri cikin turancin ta.yanda nasiru keyi da hannu yasa ta gane me yake yi ..
Sama sama khairiyya taji hayaniya.nan da nan ta fito parlor.ai tana fito wa gaban ta ya fadi ganin her man na kuka ga wata a kwance a jikin sa ..
Da sauri ta taho kusa da shi dan sanin dalilin shigar shi wannan halin. Ganin Abba da kawu sani ne yasa ta tsaya wa daga gefen shi tace a hankali da kwalla a idonta ..
"Mene yake faruwa?.."Ko bin takan Adriana batayi ba ta masoyin ta kawai take.ita kuma Adriana ganin khairiyya ne yasa ta dagowa daga jikin nasiru tana mamakin ganin ta,tadai tsorata da ganin kyau irin na khairiyya.ba bata lokaci ta fahimce koma wace tana da alaka da nasiru.alaka ma me karfin gaske. Ai so ba karya bane .A idonsu zaka fahimce hakan .nan take taji kishi a ranta .ta kasa kuma yin shiru seda tace ..
"Hi..who are you?.."
Khairiyya ma bata ko fahimce inda ta dosa ba.burinta kawai tasan menene ke damun her man..
"KHAIRIYYA!"
Abba ya kirata*"na'am Abba .." Ta amsa a hankali tana goge kwalla .
"Shiga ciki ki kyale shi kinji.laifi yayi mana muke mai hukunci.."
Bataso ta shiga ciki tabar mijin ta a wannan halin Amma kuma baza ta iya yiwa Abba musu ba..
A hankali ta tashi zata tafi .ganin haka yasa nasiru ya ruqota da sauri ta fado jikin sa.cikin matsanancin kuka yake fadin ..
"Abba ka rufa mun asiri ka kyale mun mata ta.wallahi Abba Ina son mata ta.."..
Ko kissy?..TBC
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin