part 13

978 53 0
                                    

INA AMFANIN BARIKI?

NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

AKA AUNTY DIVAA

DIVAA_DOVEYSDIARIES NOVELS GROUP ❤

Starts on the 25TH DECEMBER. 2017.finished on the 16th JANUARY 2018.

(13 )

Shiko nasiru yana fita ya fada mota yana cewa a ina ma taga nonon sawa a bra.sai dai panties,slits, da vest.

Yana fita nana Fatima ta biyo shi da gudu take fadin "yaya dan Allah inason kudi zanje na biya mana kudin gyaran jiki ni da yaya khairiy.."

Ba musu ya mika mata Atm card dinshi tare da fadin 7898..

Godiya tayi sannan ta koma ciki.shi kuwa fice wa yayi daga nan be wuce ko ina ba se gidan shi na hutawa.

Koda yaje gidan be kira booster ba ya haye dakin sa ya kwanta yana tunanin dalilin daya sa yake ta damuwa da khairiy..

Be Kai ga karasa tunanin ba ya ji wayar shi na bugawa ..booster ne ya kira shi yana masa iskanci wai shi ango ..

Yana nan kwance yana tunani .abun duniya ya ishe shi tattara wa yayi ya nufi ungogo.

Yana zuwa ya iske su gwaggo da baki .

zama yayi bayan sun gaisa yana ta zuba ido ko zaiga khairiy amman shiru.

Dan ko sanda yazo pass 2.ana dai ta Dan hira baigan ta ba ..

Gashi baya son ya tambaya saboda baki.

Tsam ya tashi ya shige uwar dakin gwaggo da tunanin bacci take tunda ita uwar son jiki ce .

Ya ko duba ta amma bata a dakin.chan dai ya fito yace "gwaggo ni khairiy bata nan ne?.."

"Eh ai Fatima ta dauke ta sun tafi unguwa.."

Shiru yayi na dan lokaci sannan yace "amman ita bata san ta tambaya ba kan ta fita?"

Gwaggo amarya ce ta kama baki take fadin.. "mu da ta tambaya bai isa ba kenan ko se har ta tambaye ka?..sannu me mata."

"Ah ah gwaggo. Amman da nima na sani da na dan basu dan abun da ba'a rasa ba.."

Gwaggo tace.."shikuma katin wajen Fatima waya bayar?..

Inace nan da Alhaji yace ze bayar Fatima tace ka ruga ka basu katin bankin ka?"

Wayance wa yayi da fadin..

"aww haka ne fa.na manta ne kwata kwata..toh Allah dai yasa kar suyi dare.dan nasan halin nana Fatima sarai.."

Nan dai yaci abinci bayan bakin su gwaggo sun tafi.a takaice dai har ya karaci Zaman shi basu dawo ba.

----------------------

Biki ya rage saura sati biyu cif cif.

Nasiru kam yawo ya same shi tsakanin gidan su da ungogo ko ganin nisan gun baya yi.

Gashi har yanzu ya kasa taba ta yadda yake so.dan da ya yi tunanin taba ta se ya tuni zaks ya ruga.

Bakin ciki ne ke kama shi se yayi zuciya ya kyaleta...

Ita ko hakan yafi komai mata dadi dan bata son yin wannan abubuwa,duk da ba wai ta sa komai ma a ranta bane ba..

Shima zaks dan yana hada mata da barazana ne shiyasa..

Shirye shirye ake faman yi ta ko ina.su khairiy jikin nan yayi luwai luwai itada nana Fatima.se sheki kawai suke yi da santsi (me bukatar gurin gyaran jiki na usul ya neme ni a number na..08165992806 a whatsapp )

Haka ma bangaren mugunguna su gwaggo suna kan gyara khairiy.ga kunun alkama da na gero da take sha.tayi bulbul da ita amman fa kirjin nan har yanzu ba magana..

Bangaren nasiru da bukata.tun yana daurewa har dai ya gaza ya koma ruwa abun shi..

Bikin shi saura kwana biyu.amman duk da haka chan na gano shi da wata asararriyar suna aikin banza.

Ita ko khairiy tana chan shakuwa sosai da Alhaji dasu gwaggo..

Haka duk sanda take son ganin baffan ta take ganin shi.

--------------

Ran juma'ah aka daura auren Imamu da Mariya..
Se Fatima da faisal.

A daren ranar akayi dinner ta gaba dayan su shida.

Dinner ce wadda ta kayatar Abba ya kashe kudi sosai...

Ran Saturday akai kamun su kuma aka sake dinner.haka anyi dinner bangaren mariya da faisal.

Biki dai ya dauki a kalla one week ana hidima.

Dan se da aka gama komai sannan suka tare.

Imamu gidan shi na kaduna.fatima ko tana rijiyar zaki.

Shiko nasiru sabon gida ya kama haya a Hotoro GRA. Flat ne 3 bed rooms me kyau .

Anyiwa khairiy kaya Kai kace iyayen ta sukai.

Gida yayi kyau sosai.gashi an hada mata lefen ta na yan gata.

Wanda fatima ta Kai mata dinki masu kyau da tsada .

Ran Kai amarya salin alin aka dauki khairiy tana dan kukan ta a hankali.

Nasihar da iyaye kewa yayan su su gwaggo sunyiwa khairiy.

Se dai tun a lokacin suka gane za'a sha fama da ita.

Saboda rashin wayon ta yafi karfin na goyon kaka.

Dan wasu goyon kakannin ma basu da rashin wayo.

Amman kam na khairiy daban ne.dan koda zata shirya a gaban su gwaggo ta tube kirjin ta ta sa riga ba tare da damuwa ba.daman ba maganar bra.se ko gaba in Allah ya hore.

Haka ma Baffa ya mata nasiha sosai.suka sha kusan su suka koshi.shidai Baffa ya roki nasiru alfarmar ya rike masa gudan jinin sa da amana..

Karfe 10 gidan amarya khairiyya yayi tsit.

Se tsoro ya kamata dan dama khairiy badai tsoro ba.

Dan ko da take kwana da gwaggo shigewa jikin ta take ta makale ta.

Hakan ne ma yasa gwaggo tausayin ta dan tasan bata san dumin jikin uwa ba.

***

Karan inji kawai kake ji a gidan.tana kwance a daki ta takure taji motsi.

Ango nasiru ne ya shigo da sallama..

TBC

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now