INA AMFANIN BARIKI?
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
AKA AUNTY DIVAA
DIVAA_DOVEYSDIARIES GROUP ❤
18th December. 2017
(10)
Baffa ne yace ah aha..ai kuwa kullun se naje karban sadaka.ana fada halin arziki irin na masu gidan.toh Allah ya biya ku da Aljanna.kuma ina ganin ka a masallaci Alhaji.sedai Dan rashin sani..
Kallon gwaggo yayi yace sedai wani hanzari ba gudu ba hajiya ..asubar yau insha Allahu zan daura auren khairiy.a masallaci zan bada sanarwa duk me sonta in bashi.hankalina yafi kwanciya..
Nan take nasiru ya kalli yarinyar da ta dade da yin bacci a jikin baffan ta.a ranshi yake cewa.tab.duk wanda aka kakaba wa wannan an cuce shi.ga dolonchi gashi zaks ya Santa.ga ba kumari.tab.Allah ya tsare.koda yake wanda ze dauka be sani ba.kyau ma kadai ya rufe masu ido.toh Allah yasa kar ta fada abunda take da zaks.shege.kodai na ja mata kunne ne?..
A wannan tunanin ne yaji suna sallama.kenan har anyi magana ma baiji ba?..
Haka kuwa suka fito suka tafi gida.baffa nata zuba godiya har nida nasiru muke mamakin dalilin godiyar.
daman ya kwace wayar ta .saboda haka a kunne ya barta ya shiga da ta daki tunda anan ze kwana.sedai damuwa ta dameshi.yana bukatar ya ya fita ..
******
A bangaren zaks bashi ya dawo ba se sha biyu da rabi. Ana ta hidima.hasali ma se a sannan za a fara partyn.ya samo kwayar da zata saka yar babyn shi a wani yanayi.
Tana aljihu..yana shiga mata suka zagaye shi bashi ya samu kanshi ba seda ya yanka cake suna ta rawa banza suna hauka a tskaiyar fili..
A hankali ya sulale zaije ya samu karamar yarinya (ta Allah ba haka ba).
Linda ya nema ya gan su suna ta bacci sun bugu iya buguwa ga gajiya.
tashin su yayi ya tambaye su ina yarinyar nan.
Aiko ba wanda ya bashi sahihiyar amsa nan ya daga hankalin kowa yana ta fada sun barta ta gudu.
Yanzu haka ma wani ya ruga shi.dakyar suka lallabashi aka fara yawon neman ta amman ba alamun ta..
zaks fa ya shiga tashin hankali ya rasa yadda zeyi.gashi shi ya damu da ita..oho dai inji DIVAA.
*****
Da asuba Alhaji ya fita masallaci da wuri.
Shikuwa nasiru koda ya kwanta kasa bacci yayi.
Seda akai kiran farko sannan ya samu bacci.dan haka bema samu zuwa masallacin ba.
Anko yi babu shi.dan mun shaida daurin auren NASIRU ABDULLAHI WAPA DA KHAIRIYYA MUHAMMAD HUUDU.
Alhaji ranshi Kal ya daura auren jika.ko Abba be sani ba.
Se gwaggo ramatu da tasan me akayi a daren ranar tunda itace me aiki ranan.
Nasiru ne ya tashi gurin 6 yaga ya makara .tsaki yayi. yayi sallah sannan ya koma ya kwanta.bashi ya tashi ba se 12:00.
Koda ya fito yayi wankan sa.boot din motar shi ya daga ya dauko kaya ya saka ya nufi gurin Alhaji.
Yana shiga Alhaji ya tare shi da murnar shi.a lokacin kuwa yayi breakfast suka shiga mota su hudu se gidan Abba.
Nasiru ya dade yana mamakin dalilin da yasa suka taho su hudu.dan Rabon da Alhaji ya shiga cikin gari har ya manta.
Ranar ta kama asabar.babu aiki dan haka suna tsaya wa yace da Alhaji zaije gun abokin shi a asibiti..inya dawo ya shigo.
A hanya ya kira booster yace yana da bukata gashi nan zuwa .ko kafin ya karasa booster ya kira wata daga cikin unguwar nasarawa ta isa guest house din.
Seda yayi wanka yayi tsarabe tsaraben sa sannan ya sa ta tayi wankan itama.ko kafin ta fito Abba ya kira shi a waya .yace mashi ya bashi 10 minutes ya isa gida..
Hankali a tashe ya taho gida.yaga mutane sun dan taru.gaban shi ne ya fadi da Addua ya shiga cikin gidan.sedai duk inda ya wuce Allah sanya alheri ake mai.
Haka dai ya shige ya nufi gurin Abban shi. Alhaji ne kawai a tare da Abba.
A hankali ya zauna ya gaida Abban shi.nan suke tambayar abokin shi.yace yaji sauki an sallame shi ma.Allah ya kara kiyaye wa suka ce sannan.Alhaji yayi gyaran murya.
"Nasiru!..inaso ka bani hankalin ka kaji me zance maka.
Kasan ba yadda Allah ba yayi da bawan sa...Toh ka godewa Allah.
Dan ya maka kyautar da ba wanda zai iya maka ita se ahi da kan S..
A asubar yau Allah ya taimake ka ya baka mata kyakkyawa yar mutunci .
Ni da kaina na nema maka auren ta kuma an bamu har ma an daura auren.
Sannan an bata sadaki dubu 50 lakadan..
Abban ka ma se da nazo yaji na daura maka aure.ina fatan zaka yi Mani biyayya ka rike Matar ka da mutunci da amana kamar yadda Malam Huudu yake so?"
Masu karatu ina so ku hango mun nasiru a lokacin da yaji an daura masa Aure,auren ma wai da khairiyya. .
Wani gumi ne ya rufe shi lokaci guda..zafi biyu ya hadar mashi ga azabar bukata ga auren ganin dama
Shirun da sukaji yayi ne ya sasu kallon shi.koda Abba yaga kamar nasiru be na'am ba yace..
"hakika Alhaji abun da kayi Allah ya saka maka da Alheri..
kuma rike khairiy da amana kamar anyi an gama ne..dan in dai ni na haifi nasiru dole yabi abunda kake so.."
Alhaji ne yayi dariya sannan yace "kayya Abdullahi.ai abunda yasa kaga haka shine.ba wanda yasan irin tsarin sa.ni kuwa na yake hukunci dai dai da ra'ayina ai dole a nemi alfarma a wajen shi..
Abba dai shiru yayi dan baya son yin musu da Alhaji ko kadan.
A nan ne ake shaidawa nasiru yadda tsarin zai tafi.
khairiy zata zauna a hannun gwaggo ramatu har zuwa sanda za'a yi biki tare da na su nana Fatima.sannan ta tare.
Biki kuwa ya rage saura 6 weeks dai dai.tambayar shi akai ko hakan bazai takura shi ba..
A ranshi cewa yayi "dayake ga maye ba.."..
A fili kuwa cewa yayi.."haba Alhaji ai ba komai.ni duk shawarar da aka yanke yayi in dai akaina ne tunda banda iko da kaina. Nagode Alhaji. Allah ya kara girma.."
Da haka ya yaudare su ya tashi ya shiga cikin gida.
Suna ta saka mashi albarka.cikin gidan ma dai hakan take.anan akai maganar kayan lefe wanda za'a kaisu gidan Alhaji dan baffa ya gani.. Nan ake maganar su inners.shikuwa a ranshi cewa yake "yo me zata saka wa wata bra?.."
Rai dai inji ni..
Wunin ranar yau,yan uwa sunta zuwa taya Murna dajin abin alheri.ita ko gwaggo ramatu da anyi magana sai tace gata kamar ita tayi kanta Dan kyau..
Shikuwa nasiru duk tsananin bukatar shi damuwa ta sashi a gaba.
Dole haka ya hakura.gashi an tilasta mashi zuwa yaga khairiy a yau dinnan base gobe ba.
Hakan kuwa akai yawa booster waya yace masa ya sako manyan kaya zai raka shi unguwa .
Shima din nasiru wata rantsatsiyar shadda ya zuba mai mugun tsada da laushi. Kan kace me ya fito ango sak.gashi ya boye komai a ransa..
Hanya suka kama Kai tsaye se gidan su khairiyya. A kofar gidan suka tarar da malam Huudu ana ta mashi Allah sanya alheri.ita kuwa tana cikin gida abun ta.kuma har lokacin bata san me ake ciki ba.
Bayan sun gaisa da malam ne ya kara mai godiya. Kawai se nasiru ya samu kanshi da ganin girman tsohon nan sannan kuma yaji yana jin kunyar sa.
Ciki yasa shi ya shiga shiko booster ya koma mota bayan sun gaida Baffa kafin ai mai iso.dan har lokacin bai mai wani bayani ba.
TBC
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin