INA AMFANIN BARIKI?
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS) AKA AUNTY DIVAA
divaa_doveysdiaries group
Sorry for keeping y'all guys waiting..
16th December. 2017
(8)
A shiryen shi Alhaji ya ganshi.tare suka rankaya masallaci sukai Sallah.ko a nan saida nasiru ya runga rokon Allah ya yaye mashi kuma ya yafe mashi..sannan ya roki Allah ya rufa mashi asiri..saboda dai bayi da niyyan dainawa .
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya..wasa wasa dokan karfe taran da Abba yasa ya kau.dan kullun dare se yaje ungogo. Daga chan kuwa zai wuce guest house insa ya Shakata.sannan ya wuce gida. Duk kuwa randa bazai je ungogo ba.ko randa Abban zaije da dare se ya tafi ball dinshi.sai ya shiga ya chanjo kaya se ya sulale ya wuce harkar sa ya bar kawu sani da jira a mota.har dai kawu sani yaga ba amfanin binshi tunda dai ba wani aikin banza yake yi ba.da haka ya samu ya kwantar da hankalin iyayen shi yake cin Karen shi babu babbaka shi da booster.
*******
Kamar kullum tare yake da wata.wayar shi ce ta kada. Koda ya duba se yaga Aliyu ke kiran shi. shaida mashi yayi Abban su ba lafiya.ya taho yanzu amman kar ya sanar da Alhaji..tunda duk iya sanin su yana ungogo.
Hankalin shi ne ya tashi kwarai haka ya tashi ya yi wanka da sauri sauri ya nufi gida.yana isa har sun fito.a motar shi aka saka Abba.se Malam Aminu kano.
Gwajin farko aka gane cewa jinin shi ne yayi mugun shooting..har 200..aiko nan da nan aka basu daki shi kadai.akayi duk abinda ya dace.
Abun tambayar anan shine mene ne ya jawo mishi wannan abun?..
Haka dai suka cigaba da jiyyan shi har tsawon kwana 7 sannan aka sallame su..
A gida bayan ya huta ya tara iyalan shi yake ce masu su kwantar da hankalin su.shi ba abunda ya same shi amman yana so Nana Fatima ta fitar da miji a hada auren su da imamu da hamza..
Gaban nasiru seda ya fadi Dan yasan sabon fada ne ze shiga tsakanin su da Abban shi.gashi kuma baya son tashin hankali yanzu da ba wata lafiya gare shi ba .
Hamdala akai tare da fatan alheri sannan duk suka yunkura zasu tashi.Abba ne yayi saurin dakatar da nasiru.
Nana wadda da murnar ta ta tafi dakin ta ta dauki waya ta kira Faisal dinta ta Gaya masa yadda Abba yace.aiko shima haka ya fada wa iyayen shi .dama an hada lefe jira kawai ake.aiko wata biyu aka sa ranan.su Umma suka Kai lefe biyu.su kuma aka kawo musu daya.
Bayan su Aliyu sun fito ne Abba yayi gyara murya yace..
"Nasiru Kai har yanzu da saura ko?.."A hankali nasiru ya kada kanshi yace "eh amma ba yawa..bayan nasu se nawa insha Allah Abba.."
Kawu sani ne yayi sallama ya shigo cikin kulawa da yayan nashi..
Abba kece wa..
"Yauwa sani gaka ga danka.kuje ku tattauna kaji ko da matsalar da baze iya gaya mana ba.."Dariya kawu yayi bayan ya zauna. Ya duba jikin Yayan shi,suka gaisa da umma sannan nasiru ya gaida shi.
Abba ne ya kara cewa suje yaji Dan in magani ne yake bukata a nema mashi.
Koda suka je compound suka zauna kawu sani yace
"Nasiru!"A hankali ya amsa mashi.sannan kawu ya cigaba
"Nasiru kaga Yaya bashi da lafiya yanzu.s
Saboda haka dole ne duk wani Abu da zai sa mashi damuwa a saka shi gefe.
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin