part 34

745 41 0
                                    

INA AMFANIN BARIKI?

NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

AKA AUNTY DIVA

Divaa doveys diaries novel group one ❤

Divaa doveys diaries novel group two ❤

@divaadoveysdiaries03.on wattpad

10th April.2018

_________

(34)

Bayan sun dawo gida .kowa ka gani cikin farin ciki yake ga graduation din yar mage sannan ga dawowar nasiru..bayan sun huta ne gwaggo Amarya ke cewa .."ohh ni khairiyya wannan girma naki na ban mamaki.wai shin Mene sirrin ne.."

Yar mage wadda take lape a jikin gwaggo ramatu murmushi kawai tayi.kuma taki cewa komai..se chan tace.."wai se yaushe su umma zasu dawo?"

Umma da Abban su nasiru sun tafi umrah..

Gwaggo ramatu ce tace "sauran sati daya insha Allah"

A haka suka ci gaba da hirar su kafin ta gudu gurin Alhaji da baffanta abunta..

*******

Tun daren ranar ake ta yan shirye shirye .an jika shinkafa anyi miyan taushe anyi stew ..itadai bata ce komai ba..wayar gwaggo ramatu ma ta dauka ta kira pinky da wali suka sha hirar su sannan taje ta kwanta abunta ..

________

Booster ya samu labarin grad dinsu khairiyya.ga tarin kyaututtuka da ta samu ..aiko ba shiri ya sa nasiru siyo mishi sabuwar laptop din daze bawa yar mage a matsayin gift dinta. .shidai nasiru da ya yarda da booster se yaji Dadi sosai.kuma yana fatan Allah ya kawo auren booster saboda dai shima yayi rawar gani .ya nuna mata kulawa kamar yadda booster kewa khairiyya..masu iya magana sunce.."rashin sani yafi dare duhu"

Dan kuwa da nasiru yasan dalilin da yasa booster ya ke yiwa khairiyya hidima da ya yi kisan kai..

*******

Da wuri su gwaggo suka tashi suka shiga hidima.haka ma khairiyya.ta tambayi wannan aikin da suke wai na mene..

Ce mata sukai baki Alhaji zaiyi..da jin haka se tace toh Indai haka ne bari ta taya su da abincin zamani..littafi ta dauko wanda musamman yan magunguna ne da girke girke a ciki.dan kam wali tana kawo masu maganin gyara suna sha.shine dalilin damuwar su ma atakaice..tunda ita wali bikin ta dama ya kusa..su kuwa yan abi yarima asha kida sha suka ruka yi suma ..

Da wannan littafin ta tsara girki masu kyau tayi juice masu dadi..lallai kam ta burge su gwaggo.su kuwa masa suka buga da miya se spaghetti da soyayyan miyan kaji..

Bayan sun gama aiki suka yi wankan su .itama wankan tayi amman batayi kwalliya ba.tadai saka dogon riga mara hannu abunta .tayi kwanciyar ta a daki tana tunanin uncle da tsayin dadewar da sukai basu ga juna ba kuma basu yi waya ba.kamar wadda aka wa allura ta tashi ta dauko wayar gwaggo Amarya .number shi ta nemo ta kira..ba karamin haushi taji ba da ta samu jin wayar shi akashe take..

Haka ta kwanta ta ci gaba da trying time to time.amman kam har ta gaji wayar shi a kashe take..

Aliyu shine ya dauko nasiru daga airport ai straight Ungoggo suka wuce..suna ta yar hirar su a mota tare da murnar ganin juna..

Gogo nasiru ya kasa boye Murna da zumudin son kasancewa da yar magen sa..shiko Aliyu dariya yake ta yi abunsa..chan dai da abun ya ishe shi se yace .."hap ashe na manta tun tafiyar ka ya khairiyya ce kawai baka gani ba.."

Nasiru daya san gatse ne aka masa se ya tsaya chak daga tambaye tambayen lafiyar ta da yadda ta koma..(ba wai yana son jin cewa jikin ta ya girma ba ko wani abun.kawai yana son yaga yadda behavior dinta suke yanzu a fili ba a waya ba..)

Shin ko ya manta ma chan suka nufa yanzu ??

Seda Aliyu yayi magana sannan yayi dariya yadan daki Aliyun kadan yace.."ka bari se kayi tafiyan shekara kai kadai sannan munyi magana ..yanzu bazaka gane ba.."

Adaidai wannan maganar sukayi parking acikin gidan Alhaji ..nasiru kam har ya kai parlon Alhaji..tabbas sunyi kewar juna .haka sukai ta murnar haduwa sannan su gwaggo ma suka shigo akai dasu ..

Duk zuba ido dai da yake bai ga khairiyya ba..se cewa yayi

"wai gwaggo ina yar taku take ne?"

Shidai Alhaji murmushi yayi abunsa.ko ba komai shi tausayi ma nasirun ke bashi.dan yasan gadon ubanshi yayi .to kuwa indai haka ne nasiru abun a tausaya wa ne..A ganin Alhaji da ya hakikan ce nasiru kama kanshi yayi a garin masu jan kunne .

Alhaji be san in yayi wasa ba har in law zeyu me suna "Adriana".

Gwaggo ramatu ce tace.."har ka gaji da ganin fuskokin mu haka da wuri?..tab akwai aiki kenan tunda dai khairiyya bata nan ma.sun fita da Nana da minal (minal babyn Nana).

"Whattt?"..shine abunda nasiru ya fada a hargitse..

Ku biyo ni muji ina kuma su khairiyya suka tafi

TBC

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now