part 9

1K 61 0
                                    

INA AMFANIN BARIKI?

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

AKA AUNTY DIVAA

DIVAA_DOVEYSDIARIES GROUP ❤

17TH December. 2017

(9 )

A kunnen nasiru wannan magana ta sauka. .su booster suka tashi dan raya daren su .Nan Linda ta Kamo hannun yarinyar zaks suka Mike.

Ganin haka yasa nasiru ya mike ya bisu sama. Dakin daya suka shiga.nasiru ne ya samu kujera daya ya zauna akai..haka wannan yarinya ma ta zauna a kasa ta takure guri daya.

Mamakin duniya ya kama shi. Tsaya wa yayi yaga yaya take ita kuma.wayar shi yake dan dannawa yana kallon ta lokaci lokaci.

Su Linda ne suka fara shirme a junan su.yarinyar na ganin haka ta rufe fuskar ta.surutan su kuma ne ya kara rudata ta toshe kunnuwan ta.duk abunnan yana sane da ita.

Yana ganin haka ya tashi yaje kusa da ita.yana taba ta ta firgita.kallon shi tayi da dara daran idanuwan ta wanda kwalla take niyyar gangarowa..

Zare mata ido yayi tuni ta ladabta.babba ma nasiru na masu kwarjini bare yar yarinya.

Hijab dinta ya cire mata.sannan yasa ta cire doguwar rigar ta ta uniform.ya rage daga ita se pencil jeans da vest.

Lunke kayanta yayi yasa a cikin sa .har ya ja hannun ta sun fara tafiya.a hankali ya juyo ya kalli kanta da yake da dankwali ga wani acuci maza da ta kima.

Zare dan kwalin yayi sannan  ya tube ribbon dinta.barin da gashin kanta yayi seda ya tsorata.

Hannun ta yaja suka fita.suna zuwa dai dai bene ya kamo kugunta suka fita a haka .motar shi suka shiga. Kayan ta ya miko mata ta saka sannan yace mata "inace unguwar ku?"

A hankali tace mashi.."ungogo "

Kai dajin muryar ta ai kasan danya ce jagwab.haushi yaji ya kama shi.dan yaji yana tunanin me zaks zeci da wannan yar yarinyar wadda ta Isa zama yar shi

"Kwatanta mun gidan ku na kaiki.."

Cikin sauri tace
"Baffa na ya hana ni Kai maghrib a waje.ze mun bulala inna je yanzu."

Ta fada tana duba agogon wayar da yake hannuta.lokaci ko ya nuna mata 11:30.

"Toh ki kira shi a waya mana.."

Bude baki tayi sannan tace
"Ai Baffa besan inada waya ba.kuma yaya  zaks yace kar na bari ya ganta.kuma yace shi kadai zai runga kirana a ciki.."

Shiru yayi dai dai sanda suka shiga gate din guest house insa .binshi tayi a hankali suka shiga gidan.a parlor suka zauna.sannan yace ..

"Toh yanzu in baki koma gida ba yau yakike ganin su Baffa zasu ji?.."

Shiru tayi bata ce komi ba.ko kan ya kara  magana wayar ta ta fara haske..

"Wake kiranki kuma?.."

A hankali tace.."yaya zaks ne.."

Smiling yayi yace ashe zamu sha hira.sa a speaker nima ayi hirar dani.

A speaker tasa kuwa..
Muryar zaks ce ta ratso cikin muryar banza.yace.."baby nah.."
nasiru najin muryar sa yasan tare da mace yake..

Tsaki yayi a hankali.ita kuma tace
"Uhm.."

Zaks ne ya cigaba da fadin..
"Kinga har yanzu ban dawo ba ko baby.."

Kallon nasiru tayi.daga mata Kai yayi se tace..
"Uhm.."

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now