part 47

687 33 0
                                    

*INA AMFANIN BARIKI??*

                   *NA*

*UMMKULTHUM AHMAD  (MRS)*


*AKA AUNTY DIVAA*

*DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ❤*

November 12,2018
Monday

__________my birthday_______
                             🎂

47

Sannan yaci gaba da cewa .."yawwa toh kinsan irin son da nake maki ,wallahi har gizo kike mun ni kadai ma sanda nake Ireland.haka muka ci gaba da zama tare ita kanta bata sona bama magana ma da ita.toh kullum ma tana chan yawon neman visa ina ta zauna a gidan ..kawai wata rana ina gida tunanin ki da azabar son ki ya dameni .ina ta kuka nikadai har taji tazo yake tambaya ta .." dan shiru yayi sannan yaci gaba da fadin.."tana tambayata damuwa ta .sonki ya rudeni idanuna sun rufe se kawai na runga ganin kamar ke .na kusance ta ashe wannan banzar ce ..aiko da na gane zane ta nayi na koreta dan taci amana ta bata kyauta mun ba.kuma dan rashin hankali har ciki gareta tasa na aikata abunda banyi niyyar yi ba..Allah ya isa na wallahi..kuma amma laifin son da nake miki ne.."

Anan ya kai aya tare da sauke ajiyar zuciya dan yasan yayi gini me inganci ..

Shiru bata ce komai ba .se yace.."inaga bari na barki dan na miki laifi da yawa kuma naga alaamun baki gamsu da bayanina ba.se da safe khairiyya amman kiyi hakuri ki yafe mu..."

"Ah ah ah ah..na yadda mine,kawai dai ina kishin ta ne tunda ita baturiya ce .."

Cikin sauri ya katse ta yana fadin .."baturiya ,baturiya kuma.ai ni kin fi ko wacce mace a duniya .nifa kowa ma namiji ne a guna ke kadai nake gani a mace.."

Woo hoo hoo ..dadi kashe khairiyya nan ta saki murmushi na jin dadi da kayatuwa ..nan kuma aka cigaba da shan hira yana kara bata hakuri akan tsautsayin da ya faru dasu .nan ya samu ya hure mata kunne wai koda za'a raba su da gaske kar ta yadda aikuwa ta hau da kyau..

Da wannan nasiru ya juya ya sha Baccin shi abun shi.

__________

Kawu sani ne a gaban Alhaji da gwaggon su yake cewa "toh kaji abunda yake faruwa ,ni ina ganin da yaya ya hakura ya karbi wannan kaddarar ya maidawa nasiru matar shi ya bishi da addu'a tunda mai faruwa ta faru .in kuma ingancin auren ne bai yadda dashi ba a sake daura musu wani kawai.."

Shi dai Alhaji yayi shiru saboda tausayin gadon azabbabiyar sha'awa da nasiru yayi .yasan tabbas ita ta haddasa mai wannan abun.shi baima ga laifin nasirun ba dan yasan baza su barshi ya auri baturiyar ba.amma tunda ya ruga yayi ai sai a hakura kawai..

Bayan dogon tunani da yayi yace .."karfe nawa yanzu ?.."

Kawu sani ne yace .."daya saura .."

Alhaji ne yace .."amarya zanje gidan dan naku na dawo insha Allah.."

Dariya gwaggo tayi dan tasan tsokanar ta yake ..taimaka mai tayi ya shirya sannan suka fito.Gidan baffan khairiyya suka je suka dauko shi shima se gidan su nasiru.

A hanya dama Alhaji yasa aka kira nasiru .dan haka a zaune a gate din gidan suka ganshi kamar me gadi yana jiran su..yana ganin su ya tashi .tare suka shiga ciki .kai da ganin nasiru kasan akwai damuwa .dan ya rame lokaci guda .

Cikin nauyi ya gaida baffa a matsayin surukin shi sannan ga laifin da yayi  ..haka ma suka gaisa da Alhaji yana mai tsiya da fadin .."me mata biyu.." amman a hankali yayi yadda ba wanda yaji se nasiru.shiko nasiru dan shafa kai yayi yana fadin.."tuba nake .."

A ran nasiru ya kuwa yasan matsalar shi ta zo karshe in banda Abba da umma da suka san gaskiyar lamari .sune be san ya zeyi dasu ba..Allah na nan ya fada tare da binsu cikin gidan yana dar dar..

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now