part 56-70

810 38 0
                                    

*INA AMFANIN BARIKI??*

                   *NA*

*UMMKULTHUM AHMAD  (MRS)*


*AKA AUNTY DIVAA*

*DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ❤*

November 24,2018
Tuesday

__________

56-70

Nasiru ne zaune cikin tunani da mamaki mara misaltuwa.wato shi booster yayi wa haka .lallai bariki batada tabbas.lallai Abokin bariki ba abokin yarda bane.ba kuma na amana ba .lallai bariki Alalar gero ce in ka iya ayi da kai in baka iya ba ta kwabe maka .tabbas badaban booster yana cikin wannan halin ba wallahi da se ya ci ubansa ..dan ya masa Abunda be taba tsammani.ya dauki qazamin jikin sa ya hada da na matar sa..qkk

Alhaji ne ya dafa Nasiru cikin yanayin lallashi ..."kayi hakuri Nasiru.tunda ya wuce kabar komai a hannun Allah.kuma ai godiya zaka wa Allah da be bawa Aminu damar aikata abunda yayi niyya ba.sannan kuma duk abunda kayi se an maka.shima ze gani a gaba dan Allah ba ruwanshi .."

Cikin nasiru ya bada kulululul..

Amman duk da haka
Cikin kuka nasiru yace.."ashe ba amana a yanzu ?..ni Aminu zeyi wa haka?,duk yaddar da nayi dashi.ni ze yaudara yaci amana ?..wallahi Allah ya isa tsakanina da ya shi kuma bazan yafe wannan cin dunduniyar da yayi mun ba..."

"Kayi hakuri nasiru.komai ya wuce .kai banda abunka ma.ai tun a ranar  yaga sakamako gashi har yanzu ..saboda haka kayi hakuri.wannan maganar kar a sake dagata.tunda ba wanda ya sani.ko su gwaggo ma bazan fada musu ba.itama mahaifiyar Aminun nace suyi shiru da bakin su dan in ba haka ba zasu batawa dansu suna.."

Ajiyar zuciya nasiru ya sauke sannan yace .."Abunne da damuwa amma ba komai Allah ne ze saka mun.."

"Ameen" Alhaji yace..

Nasiru ne yace "Alhaji dama matsala ce dani wallahi..ni hankalina ya ki kwanciya se naga kamar su Abba basu yafe mun ba.basa mun magana ko kadan .nima inna musu basa amsani sosai wallahi.gashi kuma nabi dokar da Abba ya kafa mun amman ba chanji.."
Nasiru ke fadar haka a marairaice

"Doka ,doka kuma?.."
Inji Alhaji cikin mamaki

"Eh amman ni ban damu ba ma .."

"Wace dokar wai kake nufi kenan.."
Alhaji ya tambaya a kage

"Ah ah ai ba ma komai Alhaji mid.."

"Zaka fada ko se na kira uban naka ya fada da kanshi..?.."

Dan sosa keya munafuki nasiru yayi sannan yace .."da ma,dama An bani khairiyya amma an hanamun ita.."

Wani salati da Alhaji ya hau yi se me karatu yaji.."yace wannan ai shashanci ne .ungo wayar ka kira mun uban naka .."
Ya fada yana mika wa nasiru wayar shi .nasiru na karba ya danna number Abba ya kira .dama shi Alhaji a speaker yake waya..

Bugu daya Abba ya daga cikin sallama

Alhaji ya amsa suka gaisa .sannan Alhaji yace.."niko ya nasiru da khairiyya?..kwana biyu shiru be zo mun ba.ince dai ba laifi muka mai ba yake fushi damu.."

Cikin girmamawa Abba ya amsa da .."Allah ya kara girma laifin me za'ai mishi.bayan shine me laifi .."

"Me laifi kuma?,na zata magana ta wuce ai.kardai ma ince ka hana shi matar shi ko ka kafa mai wata dokar ko kuma ka kara kwace mai kayan shi?.."

"Wane ni.Allah ya taimake ka,ai tun ranar suka koma gida .."

"Masha Allah .dan haka yanzu dai komai ya wuce ko,kuma yana da damar zuwa nan gidan sannan kuma matar shi ma yana da ikon sauke hakkokin ta?.."

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now