INA AMFANIN BARIKI?
NAUMMKULTHUM AHMAD (MRS).AKA AUNTY DIVAA
divaa_doveysdiaries
9th December. 2017
Sorry lovelies..auto correct ke chanja mun wasu kalmomi inna yi typing.ban gani ba kuma saida na ruga nayi posting.bare with me p.s..
(4)
Da sallamar shi ya shigo dakin tare da murnar shi ya samu iyayen shi da maganar da imamu yazo mashi da ita..
Aiko abba kamar jira yake.tuni ya fara yi wa nasiru hannunka me sanda..shidai nasiru kamar kullun shiru yayi kuma fuskar shi bata nuna ya damu ba.
A kasan zuciyar shi yake tunanin anya bazai nema transfer ba.yadan barsu dan acika mai mara yayi fitsari..
Abba ne ya katse shi da fadin..
"Nidai da ka ganni bazan gaji da maka maganar aure ba.sanda kuma na gaji da binka kuma sai dai kawai kaji na daura maka aure..""Abba Dan Allah ayi hakuri.insha Allahu zanyi magana nan bada dadewa ba.akwai wadda nake jira amman kwanan nan zan yi mata magana "
"Allah dai yasa.aikai kullun baka rasa abin fadi.."
Inji Umma da sai yanzu tayi magana.nan kuma suka saka ranar zuwa suka ce a fadawa iyayen mariyan aji ko hakan yayi masu..Bayan nasiru yayi wa kannen shi bayani ne ya wuce ya tafi dakin sa yabar imamu da Murna.shiko yana zuwa ya chanja kayan shi ya fito ya nufi bangaren iyayen sa.da mamakin shi sai yaga kawu sani a palon. Smiling yayi yawa iyayen sa da kawun sallama ..
Motar shi ya nufa. A hankali ya fita ya hau titi yana tafiya.kawu ma bai tsaya bata lokaci ba ya fito ya hau motarsa ya bishi a baya.
La sultana nasiru ya nufa .parking yayi ya fito ya bude boot din motar shi ya dauki kaya .koda kawu yaga haka se ya zata kayan ball nasiru ya dauka.shikuwa nasiru kaya ne ya dauka wanda zai chanja ya batda kama.
Parking kawu yayi da tunanin shi bazai shiga ba kafin a dauke mutumin shi banza.tunda ya lura harda mata ma.
Dan saurayi ne yazo yayi parking daidai kawu.har zai shige kawu yayi mai sallama .yace mashi
"Kanina indan tambaye ka mana.."
Dan matashin saurayin ne ya tsaya da yar jakar kaya a hannun shi yace..
"Wa'alaikassalam ..ina ninja.. "
Kawu ya sake ce mashi ..
"Ball nakeson yi amman nayi wa amarya alkawarin bazan zo inda yanmata suke ba..nan kuma naga kamar da yar mata a ciki.."Dariya saurayin yayi sannan yace ..
"Da gaskiyar ta kuma.saidai wannan karsu dame ka kallon ball kawai ke kawosu. Wasu ma da mijin su suke zuwa wasu kuma yayyen su suke biyowa.."Godiya kawu yayi mashi yace toh zan kirata na Gaya mata sannan na shiga..
Suna cikin wannan maganan nasiru ya wuce bayan ya chanja kayan shi ya daura jacket akan kayan shi yayi wucewan shi sai nasarawa GRA. Tun a hanya ya kira booster yace gashinan zuwa amma bazai dade ba saboda Abban shi.
Dadi kamar ya kashe booster..waya naga booster ya daga ya kira wata waya.nidai bansan wa ya kira ba haka kuma ban san me suka ce ba..booster ne naga ya tashi ya fita se guest house din nasiru.a gate din gidan naga ya shiga da yanmata su hudu cikin gidan.daman tuni nasiru ya isa duk da a adaidaita sahu yaje.ko a lokacin pass 8
Su booster na shiga naga yayi tsalle ya rungume nasiru.kaina ne ya daure na kasa gane me nake gani.toh gadai mata nan har hudu zabga zabga an tara ..daya ma daga cikin su ta kusan haifar shi ..amman dai gatanan itama.bari mu jira muga wani irin karatu zasu dauka..
Booster ne yake cewa "nayi missing dinka guy. Komai yafi daidai inkana kusa "..
Murmushi kawai naga nasiru yayi..ta kasaita wadda ta kara mashi kwarjini.
Wai shin ya kammanin nasiru take?
Shidai nasiru irin dogayen mazan nan ne masu fadin gaske.cikakken namiji ne ta ko ina.jikin nan a murde yake kamar dan dambe. Cikin nan nashi a manne da bayan shi .wuyan shi kuwa kai ka rantse cobra ne ya fasa Kai.. sai dai kuma fuskar shi bata cika kyau ba.irin kai tsaye baza'a kira shi da ne kyau ba.sannan kuma baya layin munana.dai dai dai dai.saidai da ka ganshi kasan hutu ya ratsa shi,shi chocolate color ne.fatar shi da gashin kanshi kadai abun kallon ne..bari mu bari haka kar gaban shi yayi ta faduwa.TBC
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin