INA AMFANIN BARIKI
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
AKA AUNTY DIVAA
DIVAA_DOVEYSDIARIES GROUP ❤
21st December. 2017.
(11)
Da sallama ya shiga tsakar gidan.shara take yi ta sunkuya.amma ba irin alamar komai a kirjin nan.flat!..tsaki yayi a ranshi yake cewa wallahi Alhaji ya cuce ni..
Amsa masa sallama tayi sannan ta shimfida mashi tabarma.dankwali ne a kanta.amman kamar babu Dan kwalin.gashin nan yayi him a sama an cunkushe shi.se wanda suka dan zaro ta saman dan kwalin suna reto.
Zama tayi a hankali tace mai
"Yaya ina kwana .."Wani bakin ciki ne ya kamashi da ya tuna yaya take cema zaks..
Kallon ta yayi yace "kar na kara ji kince mun yaya.kice mun uncle"
Daga Kai kawai tayi sannan tace..
"Uncle ina kwana.."A hankali ya amsa cikin nazarin ta.tashi tayi ta samo masa ruwa ya sha. Se sannan yace mata zai shigo da bako su gaisa.
Neman guri tayi ta zauna itama a kasa. Tunani yayi yace mata taje ta sako hijab dinta dan yana gudun kar booster ya ga kirjin nata shabal.
Kiran booster yayi a waya yace mashi ya shigo.koda ya shigo fuskar nasiru a sake.dan baze ma nuna mai ba'a son ranshi akai mar wannan auren ba.
Cikin sakin fuska nasiru yace
"Aminu..da farko dai ina mai baka hakuri dan wallahi nayi maka laifi.. "Khairiy ya kalla wadda take a tsorace a kasa..wasan ta ma take yi.sannan kuma hankalin ta baya tare da su..
"Wannan itace khairiyya. My bride.."
Booster da tunda yaji nasiru ya kira shi da Aminu ya cika da mamaki ne ya zabura ya kara kallon khairiy wadda ita bata san ma abunda ake yi ba.tana chan tana tunani.
Yace"your bride?"
Yana kallon nasiruNasiru kuwa dan ya saukaka wa booster se yace masa "my legal wife..my love "
Booster dai yaja bakin shi yayi shiru.yana so sai sunje mota sayi maganar.
***
A gida su Alhaji sun shirya bayan an aiki nana Fatima ta siyo mata tsadaddun abayoyi da riguna masu kyau kan ayi mata dinki.su gwaggo ne suka taho da kayan .
Basu zame ko ina ba se gidan su khairiyya.bayan sun sauke Alhaji a gida.
Su kuwa su nasiru lokacin sun wuce gidan Alhaji dan Alhaji yace su same shi anan.Basu dade ba suka dauko khairiyya sukai wa baffa sallama dan dama ya san yadda suka ce..
Su gwaggo basu san baffa be gaya mata ya daura auren ta ba.
Dan haka ba wani bayani sukai mata me yawa ba.aka wuce da ita se bayan layi.
A bangaren Alhaji su nasiru zaune shi da booster. Alhaji ke cewa
"Nasiru tunani nayi na tambayeka ba idon Abdullahi..kana ganin rike maka mata har na tsawon wani lokaci bazai dame ka ba?.."
Shiru nasiru yayi .A ranshi yake cewa.."ni ina zai wani dameni?.."
Booster ma ranshi cewa yayi.."wallahi da gaske nasiru yayi aure.."
Maganar Alhaji ce duk ta katse su daga maganar zucin su..cewa yayi
"Kar kaji kunya ta dana.."A hankali nasiru yace "ba komai Alhaji zamu jira.in sha Allah.. "
Albarka ya sanya masu sannan ya koma kan booster dan dama ya san abokin nasiru ne tun da dadewa .yace "Aminu Kai sai yaushe?.."
Booster ne ya kalli kasa cikin girmama wa yace
"Ai Alhaji duk sanda Allah ya kawo a shirye muke.."Dan dariya Alhaji yayi irin tasu ta tsoffi.sannan yace
"Hakan ma ba laifi.amman kasa a ranka a kwana kusa zaka yi insha Allah. Zaman haka bashi da amfani.kaji ko?..""Insha Allah.."
Itace amsar da booster ya bawa Alhaji.
Nan ya rike su su tsaya suci abinci tare.nasiru kuwa cewa yayi yana zuwa.
Bangaren su gwaggo ya tafi duk suna tare.gwaggo amarya ce take taje wa khairiy dogon gashin kanta.duk yayi wani curling gashi baki wuluk gashi da cika.ita kanta me gashin damun ta yake yi.
Gwaggo da taga ya tsaya. Kallo yaki ya kare ne tace..
"Ango karaso mana.."Ita kuwa khairiyya kamshi taji wanda ta saba ji duk sanda yaya zaks ya ke guri..
A hankali ya karasa shiga ciki ya zauna kusa da gwaggo yana kara kallon gashin kan khairiy..ita kuma khairiy ta damu Dan dama in baffa ze gyara mata Kai se anyi ta yin daru.dan lokaci zuwa lokaci ma yanke wa take da almakashi..
Da yar muryar ta tace
"gwaggo ki dan rage mun dan Allah"..gwaggo da bata gane ba tace "me za'a rage miki?"
Har ranta tace "yanke wa za'a danyi .."
Dariya gwaggo tayi tace "ina kika taba ganin an yake gashi?"
"A gida Baffa yake yanke wa in ya taru irin haka.."
Nasiru da fada yace
"Toh daga yau kar na sake jin zancen yanke gashi a bakin ki.."A tsorace tace
"Toh yaya.."
Da sauri ta gyara tace toh uncle.."Haka kawai se ya kasa tashi .
Nan ya zauna yana kallon yadda ake gyara kan nata.tsintar kanshi yayi da son shafa gashin ..ya Lula duniyar kallon gashi yaji gwaggo amarya na cewa..
"Oh khairiyya na rasa yadda zan kama maki wannan gashin.."Cewa tayi "nima Baffa ne ya iya kama mun"..ko kafin ta dire na tsinci nasiru na cewa .."zo nan muga.."
Gwaggo kam tashi tayi da dryer da comb da su manta ta shige uwar daka..sannan ta wuce ta barsu ta tafi gun gwaggo ramatu dan zuwa cin abinci da Alhaji..
Dadi yaji da yaga ta fita daga bangaren ..zama tayi kamar wadda zaiyi wa kitso ..ta mika mai ribbon dinta ..
A hankali ya karba yana kallon gashin..kai hannu yayi ya shafi gashin da ya Kai mazaunan ta .ga tsayi ga cika..
"Yaya kama mun.."
Ta fada tare da dawo wa dashi daga tunanin da ya shiga..Wani haushi yaji da yayi tunanin yanzu haka fa zaks yasan gashin nan..
A hankali ya saki wani siririn tsaki..kishi ne ya turnuke shi.ji yake kamar yayi ihu.kamar ya shake ta na kowa ya huta..
"Ashe nima abun yafi karfi na.."
Ya fada yana bata ribbon dinA parlon Alhaji kuwa su gwaggo sun hada abinci amman ba ango bare amaryar sa .Aminu aka aika ya kira su a part din gwaggo amarya..
Saboda haka Kai tsaye ya bude kofar palon ya shigo.
Ai nasiru na ganin booster ya sau baki yana kallon gashin Matar sa yace.."yadai?.."
Waske wa yayi yace "ku ake jira fa.."
Yaga kishi karara a idon nasiru saboda haka da sauri ya juya ya fice..a ranshi yake cewa "ina nasiru ya samu wannan zukekiyar wai?."
TBC
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin