part 50-55

877 42 0
                                    

*INA AMFANIN BARIKI??*

*NA*

*UMMKULTHUM AHMAD (MRS)*


*AKA AUNTY DIVAA*

*DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ❤*

Novemberber 18,2018
Sunday

__________

50

Mamaki ya kasa barin fuskar kissy dan ganin cewa ita yake share wa amma yanzu ya juya akalar laifin shariyar ta koma kanta. Lallai ma

Hannun shi ya dauka ya rufe dan karamin bakin ta da ta bude tare da idanun ta da waro su dan tsananin mamakin da ya kamata.

Shagwabe fuska yayi cikin cewa.."baki yadda bane ba kissy ?.."

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara girgiza kai hawaye na zubo wa ,a hankali kuma tace mishi.."ni wallahi ban san ina shareka ba.ni na zata ma kaine kake shareni saboda baturiyar ka.."

Tausayin ta ne ya kamashi matuka dan haka kwalla ta taru a idon shi .ji dai har ya juya zuciyar ta ta koma sak itace me laifi.zuciyar sa ta karaya kwarai da gaske ..rungumota yayi cikin karaya da tausayin kanshi .toh tausayin kanshi mana .dan dai shi ne me matsala ba ita ba.ita ba hakkin shi a kanta.itako tana da hakki akanshi .hakki ko wanda ma baze iya neman gafarar ta ba ..sake kankame ta yayi .amman duk da haka iya nan aka tsaya.wanda hakan ma ya kara yawan damuwar da kissy take a da.

Mudai je zuwa...

_______

Kissy da her man sun shirya tsaf domin zuwa gidan Abba da a yanzu yake wa Nasiru wahala ko kuma nace nauyin zuwa.shiyasa yasa khairiyya ta shirya suje tare tunda ko banza yafi samun fara'a a gunsu in sunga harda khairiyya..

Suna fitowa suka shiga sufi mart suka yi shopping sosai wanda seda kan khairiyya ya kulle ..ita dai tasan sunyi shopping dinsu na gidan su ko week ba'ayi ba.sannan yasa ta daukar wa su Abba abubuwan bukata .sannan kuma shi yana nashi daban .kome ne hakan oho??

Ita dai batace komai ba ta tula wa su Abba kaya suka je suka biya duk.nasu Abba aka sa a back seat sannan wanda yayi daban aka saka a boot din motar.

Se a mota ne khairiyya ta tuno da dayar matar shi.nan da nan ranta ya baci .tuni ta dauke wuta ta sha kunu.ita badan ya siya wa baturiya bane take jin haushi.me yasa baze bari se shi kadai ba ya siya mata .se sanda suke tare ..

Da murnar shi ya shigo motar ya tashe ta ya wulla da su titi .se a sannan ya waigo ya kalle ta dan yaji bata mai magana ba .ya saba kome yayi zata ce ta mishi "sannu da aikin.." amma yau shiru.shi yasa ya kalle ta da kyau..Murmushi yayi yace.."wa kuma ya bata ran princess dita?.."

Ya tsammaci magana daga gareta se yaga sabannin haka .dan yi tayi kamar bata jiba ..A ranshi yake cewa "To fa..anzo burin.."

Gyaran murya yayi ya sake cewa.."awhoo nasan me ya faru..gani kikai me abayar nan tana ta kallo na ko ?..kai khairiyya da kishi kike .."

Ai nan kuwa taji haushi ya kamata. Wato har ya kula wata tana kallon shi.dan tsabar ya kalle ta shima har a ya ruke cewar abaya ta saka..lallai yau Nasiru ya debo ruwan dahuwar kansa.

Kallon shi tayi na yan dakiku ta juya ta ci gaba da kallon gaban ta.shi da kanshi ze iya cewa be taba ganin wanna face din tata ba .Tab .lallai ran mata ya baci .

Haka yayi ta magana ko ci kanka bata ce ba .lallai ya tsorata da lamarin kissy a yau.da wannan suka iso gidan Abba .suna parkin ta balle murfin kofa zata fita sannan ta kalle shi tace .."zan dauki kayan su Abba amma na baturiyar ka dauko da kanka.ita kuma me Abaya in ba kallon ta kake ba ya akai kasan tana kallon ka ?.."
Nan ta rufe kofa ta ta dauki leda daya ta wuce ta barshi da baki a sake..

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now