part 1

3.1K 147 3
                                    

INA AMFANIN BARIKI?
      
         NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS). AKA DIVAA

Assalam lovelies.. Hope kowa lafiya. Kuyi hakuri na chanjin littafi da aka samu. Da nace Abbood dawoud zan fara. Amman hakan bai samu ba saboda inada dan shirin da nake yi. Kar na barku haka yasa na fara bada wannan. Ina fata zaku biyoni muje..

(1)

6 December .2017

"Wallahi Nasiru ka fita idona na rufe. Yaro dakai amman idonka suna son su rufe, baka ganin gabanka kwata kwata.
Toh wallahi na gaya maka wannan ya zama Karo na karshe da zan maka fada akan yawon dare.
Kai kenan se kace aljani. Kai lokacin da kowa yake bacci, lokacin kake yawon iskancinka?..
Shin kannen ka abunda kake so su koya kenan?.. 
Duk ina tarbiyar da na baka, wallahi nasiru bazaka sa Allah ya kamani da laifi ba. Na Baku tarbiya wadda yan uwa da makota suke alfahari da ita.na baka ilimi both na boko da arabiy. .ko so kake kace mun na Gaza? ..

Cikin in'ina nasiru yace..

"Dad wallahi bana shaye shaye. Duk Wanda ma suke ce maka ina yi suke yi. Dan wallahi ni ko shisha ban taba sha ba. .daman ball ce muke yinta a la sultana. Kuma dad se dare take tashi.. "Cikin natsuwa da sunkui dakai yake magana.kai kace mutumin arziki ne

"Kai dallah rufe mun baki, inbaka shaye shaye ai kana abunda yafi haka..ball in taka ai ta manyan yara ce. wa ya aikeka yin irinta Dan ubanka..toh daga yau na soke ta.zan kuma sa doka naga shegen da ya isa yasa hannu ya shure. .Dan na tabbatar ganina kake munyi kai daya dakai.. Wallahi kaji na rantse ma nasiru. Daga rana irin ta yau karka kara kai mun Tara a waje. .ga mamanka nan zata zama shaida duk randa tara ta Kara maka a waje, sedai ka nema gurin kwana..duk wani abu da kake ji dashi se na kwace..in kana son kanka da arziki kaji da aikin ka kawai.."

Juya wa yayi yace
"Saratu kinaji ko. Sheda kike zan, gaya wa Muda (me gadi). Tara nayi ya kulle gate indai Dan nasiru ne. Kar kuma ya kuskura yabar shi fita ko shiga bayan tara...kinji ko ba kiji ba?.. "

Umma saratu data sauke wata dunkullalliyar ajiyar zuciya ce tace ..
"Naji daddy.. Insha Allahu za'a kiyaye.. "

Hukuri nasiru ya kara bayar wa tare da tabbatar was da iyayen shi baya aikata wani aiki na assha.. Sannan ya tashi yayi bangaren sa..

Umma ce ta matsa ta rungume Dan tsohon mijin ta tare da buga bayan shi.a hankali ta nufi gunda sideboard yake ta bude ta chiro glass. Fridge ta nufa ta zubo ruwa mai matsakaicin sanyi ta nufi mijin ta cikin murmusi ya karba ya sha..

Kwantar mai da hankali ta Shiga yi. Saboda duk da kasancewar shi Dan kimanin shekaru 60 ba abunda ya ragu nadaga son matar shi.. Dan tsoho ne yayi likimo yana receiving current.. Dan dama tun asalinshi yana da yawan bukata. Kusan a iya cewa shi nasiru ya gada shi yasa shi fadawa hanyar da yake bi a yanzu..

Alhaji Abdullahi wapa hamshakin me kudi me Wanda yake da mata daya da yara biyar hudu maza daya mace.

Nasiru shine da na farko dan kimanin shekara 30.se Aliyu Wanda yake bi mai (28). Se hamza (26), imamu (24) se Nana fatimah wadda itace yar autar su me shekaru (22).

Aliyu yayi auren shi da dadewa. Dan da an bari se nasiru ya fara tukun. Tunda ko aka lura bashi da niyyan yin aure a kace duk Wanda ya shirya ya fito. Haka kuwa akai. Kan kace me kuwa akai bikin Aliyu aka kai mai matar shi. Suna nan zaune a lamido crescent dake kano.

Koda Abba ya Kara tuntubar nasiru da maganar aure yace "shi bashi da niyyar yin aure yafiso ya dan tara abun hannun shi". Ya kara da fadin "inda haali ma yafi son se ya gina gidan kanshi tukunna"..
Duk kuwa da cewa Abban su zai bashi gida kuma daman yana aikin shi a NNDC. Aliyu be ma take tare da Abban su a gun chanji.

**********

Koda nasiru ya koma dakin sa abun duniya ne ya ishe shi. Yasan dai ko giyar wake yasha Dole ya hakura ya zauna a gida yay. Dan sarai yasan Abban baya chanja maganar sa.. A ranshi take tunanin ya kamata ya chanja halin sa amman kam akwai wahala. Sau da dama yakan yi  yunkurin barin irin hanyar da yake bi. Amman kan kace meye ya koma ruwa. Shi kansa har mamakin kansa yake yi.

A Daren ranar ne umma na zaune da Nana suna hirar su cikin jin dadi take cewa ita fa tafison ta fara aiki kan tayi are. Tunda daman gaba dayan su mazan suna da aikin yinsu tunda duk sun yi karatunsu.. Hamza dama yana daily trust abuja. Shi kuwa imamu business dinshi yakeyi. Kuma Alhamdullilahi ya kafu sosai.. Duk dai yayan Alhaji Abdullahi wapa ba na banza se nasiru. Shima kuma shi yasa kanshi.

Haka dai nasiru ya daure wa ransa ya kwanta tun yana tunani har bacci ya kwashe shi..

Washe gari da safe ya shirya tsaf dashi ya nufi bangaren iyayen shi yayi matukar kyau yana ta zabga kamshi. Kamar dai yadda al'adar maza take..

Cikin girmamawa ya gaishe da iyayrmen shi kannen shi ma suka gaishe shi.

Haka suka kammala breakfast. Nasiru ne ya fara fita dan shike Riga kowa fita. Shikuwa Abba dama Aliyu ne ke daukar shi karfe goma su tafi wapa. Sannan insun taso ma ya dawo dashi sannan ya wuce gidan shi. Suna da office dinsu kato.

TBC

Ga me neman shawara akan duk wani Abu da ya shafi mata.. A iya samun mu akan wannan lambar ta whasapp.. 08165992806.

Ladies only!

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now