part 35

825 42 0
                                    

INA AMFANIN BARIKI?

               NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

AKA AUNTY DIVA

DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP ONE ❤

DIVAADOVEYSDIARIES NOVEL GROUP TWO ❤

12th April.2018

_________

(35)

Kallon shi duk suka yi..A hankali kuma yace .."ina ma wai suka je?.."

A ranshi yake cewa yama za'ai ta fita bayan ze dawo..

Shidai ji yayi kawai ance .."ai batasan zaka and dawo ba.kuma jin cewa maza ne zasu zo shi yasa ma ta gudu abunta.."

Maganar da yayi a zuciya ce ta fito bai sani ba..

Sudai gwaggo cewa sukai bari a hada mai kayan abinci yaci ..yace "tohm amman se yayi wanka .."

Kai tsaye ya tafi kawu sa'id wanda ake gyara shi duk bayan 3 days dan kar ya kasan ce an barshi ba mutum kuma ba'a dan shigan shi..wanka ya fesa ya sake kaya ya sha turare dan ya ruga ya gama sawa ranshi yana gama cin abinci ze kira nanan yaji inda ta kai mashi mata..

Duk wannan sha'anin da ake kuwa khairiyya tace bazata leko ba.in kai abincin ne ma part din Alhaji ga baba me tuwo ga su habu duk zasu kai ..hakan ne yasa tayi kwanciyar ta cikin tunani da muradin kasancewa da uncle dinta a dai dai wannan lokacin.

Shikuwa Nasiru bayan ya fito ne kowa ya tambaye shi wannan gayun kuma ina zashi..se yace zeje yaga Aminun sa wanda ya kasan ce bashi da lafiya . .cikin haka Alhaji ke cewa "haba ashe shi yasa naga baya zuwa kwana biyu ..Allah ya bashi lafiya ka duba shi kafin na samu naje nima .."

Da haka dai Aliyu ya bude flasks din abincin ..yana son masa Amman kama cous cous din da ya gani da miyar casserole wadda ta amsa sunan ta ya dada shi da kasa..ga wata kaza wadda take dan kauri kaurin gashi kuma amman dafa ta akai .idon shi yakai kan juice din water melon wanda yake ta tiririn sanyi .ai se cewa yayi shi baze ci wata Masa ba..

Nan kuwa ya zuba cous cous dinnan yaci yayi nak yasha lemo yana ta zuba Santi sannan ya tashi bayan ya diga miya a wandon farin kayan daya saka..ana cikin cin abincin gwaggo Amarya ta tashi dan tasan inyaga bata palon zeje ya mata sallama.Ai kuwa se binta daki yayi dan inya tafi ma ko dawowa baze ba .da ya dauke ta se gida zasu wuce abunsu..

Gwaggo kuwa na tashi ta tafi gurin khairiyya tace mata wai tazo ta gyara mata kanta ..su yar mage anji abunda ake so ba musu ta taso..se gwaggo take ce mata gwamma taci abinci sannan se ayi.wannan uban gashin da aka ware kam a haka aka barshi ..Masan ta zubo guda one abinta da miya se dan kazan da tayi .ta zauna zata fara ci kenan....

Wannan dalilin yasa shi shiga yawa gwaggo sallama da nufin cewa ya yi gida daga chan ..se me?

Se ga wata tsaleliyar budurwa a zaune tana cin abinci ta watsa gashin nan nata a gefe daya..itama sallamar namiji yasa ta tsorata zata gudu..gwaggo da tasan ta hada wannan abun sum sum tayi ta fice ta kofar kitchen abunta..

Tsaya wa yayi chak yana kallon khairiyya..sarai yasan itace amman ko a mafarki bai taba tunanin zega yar magensa ta zama haka ba..itama chak ta tsaya da cinyan kaza a hannu tana mamakin ganin shi bayan batasan yana nan ba..idanunta sunfi komai daga mai hankali .dan yanda tai dasu ba duk kai ba..

Itadai da Allah yasa ta motsa da gudu ta shige daki bayan ta yarda cinyar ta a tsakiyar palon..hijab din sallar ta ta dauka take kokarin saka wa .wai a dole kunya take ji..(niko diva nace abun ya dawo kenan )

Kai tsaye ya tafi dakin ya iske ta tana dambe da hijab. .A hankali ya taka zuwa inda take ya kama hijab din.ba musu ta cika masa .ajiye shi shima yayi sannan yace .."khairiyyah .."

Wannan idanun nata ta dago ta watsa masa ..aikuwa kamar an harbe shi haka yaji..

"Khairiyyah.."
Ya sake kiran sunan nata

Se a sannan tace .."uhmm .."

In me karatu be manta ba nace muku daman tunanin shi take tayi.saboda haka jikin ta a mace yake murus! ..A dai dai nan kuma hirar su da Aminan ta ya fado mata a rai..

A hankali ya matso daf da ita ya rungumota..haba malam zoka ji rige rigen sauke ajiyar zuciya ..bata bata lokaci ba itama tasa yan hannayen ta ta rike bayan shi ..sun dade a haka kafin ya dago ta ya kalleta..jan hannun ta yayi ya kaisu kan couch din dake dakin suka zauna..

"Khairiyya..."
Ya kirata a hankali yana kallon idonta tare da hannayen ta a cikin nashi..

"Uncle..ina yini.."
Ta fada kanta a kasa

Dariya yayi saboda haka gaisuwar ta take tunda se an dan dade sannan ta tuno..ba shakka kuwa dariyar da yayi ta tafi da imanin ta..ga pink lips dinsa sun dada turuwa kuma sunyi subul Subul ga wani uban kamshin turare da yake zubawa..ga gashinan yana ta kyalli .ya sha gyara tsaf!

Hakan ne yasa ta shagala da kallon shi ..har se da ya busa mata ido sannan ta buya a jikin shi .dan wallahi bata san tana masa irin wannan kallon ba..

Shikuwa a ranshi yake cewa lallai yar magen sa tayi wayo ta girma..Dago ta yayi dan ma ya kara kare mata kallo ..idonta ya kalla sannan yakai duba kirjin ta..A nan ne yake kokarin bata lokaci wajan son tantance gaskiyar abunda idonsa ya gane masa ..Be Bata lokaci ba kuwa wajen bawa kansa amsar cewa padded bra ce aka saka.da wannan amsar ya saki tunanin shi.dan ko akwai ko babu yana son matar sa.

"Kai uncle..."
Ta fada tana kara kwanciya a jikin sa..toh dama kun san mage da son jiki ..shine dalilin da yasa shi sa mata yar magen sa..

A hankali ya rike ta sannan yace mata .."Ai laifin ki ne..keda na dawo ma baki damu da ganina ba.daman ance mun kin ce ke bakya sona yanzu.."

Da sauri ta dago kanta tace.."wallahi ina Sonka.."

Tabbas wannan magana ta mashi dadi.Dan jin shi yayi kamar wani sarki.kai Masha Allah.shidai kam boarding ta mashi babban taimako ..

Ita kuwa kunya ce ta kamata gaba daya .tama rasa me zatayi..lura da hakan da yayi be yasa yace .."kai my girl kin burge ni sosai sosai..ba abunda nake son ji daga wannan dan bakin naki kamar wannan kalmar.."

Se sannan ta saki jikin ta suke shan hirar su..cikin hirar ce yake ce mata tai mishi wakar da take mishi a waya..sannan ta saka mai ita a waya dan yana son wakar tunda ta koya mai jinta..

Sannan ya kara da fadin .."mene ma sunan ta ne ?"

Dum gabanta ya kara fadi..bayan shi ya koya mata son wakan kuma sannan yace be san sunan ta ba?

Kawai se tasa a ranta tsokanan ta yake yi..A hankali kuwa ta fara mashi suna dariyar su abunsu..

Chan ya tuno abinci take ci ya iske ta..se ya tashi ya dauko abincin ya dawo yana fadin "oh yar mage daga ganina kuma se a manta da batun abinci?.."

Itadai dariya tayi a ranta kuwa take cewa..(Indai dan kaine komai ma mantawa nake dashi..)

Kusa da ita ya karaso ya zauna a kasa sannan itama ta sauko ta lape a jikin sa cikin shagwaba kuma take cewa "nifa naa kooshi.."

Murmushi yayi a ranshi yake cewa tabbas me hali baya fasa halinsa..

Be Kula ta ba ya tattaro gashin ta da yake ruda shi yasa a gefe daya sannan ya gutsuro masan ya bata.."saura ni zaki bawa .."amman fa ni bada hannu nake so ba.."

Seda ta kalli hannun nata sannan tace.."toh bari na dauko spoon na dawo.."

Kamar wani karamin yaro ya makale kafadan shi yace.."tsaya na koya maki yadda nake so .."

Itakam dariya ma ya bata sannan kuma ya kara burge ta ..haka nan kuma take mamakin irin shi ..bata karasa tunanin ta ba ya gutsuro Masan ya sa mata a baki yana fadin.."karfa ki ci mun kayana..ehen oya bani naci.."

Ai da ta gane me yake nufi se ta tsaya chak da masa a bakin ta..

"Karkici ko kadan wallahi..duk nawa ne..oYa ki bani naci.."

Aiko maganar su pinky ce ta kara dawo mata..se ta matsa a hankali tana kokarin bashi bayan ta rufe idon nan ruf!

Seda ya bata mata lokaci sannan ya karba yaci abinshi .a cikin soyayya dai aka karasa cin abinci wanda sallah ta tashe su badan sunso ba..

Nima kuwan sallan na tashi nayi ..in mun idar kuma se muga mene zezo a gaba..

TBC

INA AMFANIN BARIKI ??✅Where stories live. Discover now