SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
FRIDAY,12TH NOVEMBER,2021
MY BIRTHDAY
(1)
----------------Bismillahir- rahmanir-rahim
Da sunan Allah me rahama me jinkai.Salati da daukaka abisa Shugaban mu Annabi Muhammad (S.A.W)..Sabon littafi zan fara,Ina rokon Allah ya bamu ikon farawa lafiya tare da gamawa lafiya.Amin
(1)
Zaune take a tsakar gidan ta tana tsince shinkafar da a yanzu ta gama Yar murya gurin Baban Abul ya samu ya auno Mata ya bata
zuciyar ta tayi nisa cikin tunanin halin dan adam tare da kalolin sauyi na rayuwa da kan zowa dan adam a rayuwar sa
A kullum tana sake Gode wa Allah a game da ni'imomin da ya Mata duk kuwa da irin kangin wahalar da take ganin tana ciki ,in ta duba yayan ta guda hudu da ta Haifa,se taji ko wacce damuwa ta yaye Mata,musamman yadda tun yaran ta na kanana Allah ya Sanya musu tausayin ta a cikin zukatan su,musamman na ganin halin fadi tashin da take a kansu .
wannan tausayin shi ya haddasa Masu soyyayar Mahaifiyar su me karfi a zuciyoyin su..
Duk da tana cikin zuzzurfan tunani,hakan be Hana ta yin kokarin yin sauri ba wurin ganin ta karasa sanwa ba tun kan yan makaranta su dawo don tasan da yunwa suke dawowa dan ba ko yaushe bane take samun basu Karin safe ba.
musamman ma irin yau da basu ci komai ba suka fice gashi ko kudin break Bata iya basu ba,toh Ina ma tagan su? da da akwai ma da tuni ta yafa mayafin ta ta nufi shago ta siyo musu gari da sun Sha tun a safen, da a dam zasu tafi makaranta suje su dawo tunda shi Gari dama hayayyafa yake yi a cikin mutum in aka ci shi.
Shi yasa in mutum yaci gari yake rabuwa da yunwa nan take ..
Sauri sauri take Yi tana kokarin kunna gawayin ta,ta dai samu to dora shinkafar wadda zasu ci da gishiri da Mai ,don ma wai in da sabo ai sun Saba da yunwa ga uwar wahala..ba Dade wa wuta ta kamu tayi jazir, dan Maman Abul kam ta iya kunna gawayi da icce sosai ba maganar kalanzir sabo da tsabar sabo da amfani da gawayin,yau da gobe ta wuce wasa..
tuni ta dora shinkafar ita Kuma ta koma gefe ta doka tagumi yayin da ta sake fadawa duniyar tunani Wanda Daman yanzu da shi take rayuwa matukar aka ce su Abul basa nan.
kullum cikin tunani take Wanda a har ko da yaushe tana ta kokarin ganin ta samo inda matsalar take,daga Ina ne ma wai ta kwafsa,Amman kullun har ta gama yawo a duniyar tunanin ta Bata taba gane wa ba ko ma cin karo da amsar tambayoyin ta.Ba kutse take wa Allah ba,Amman Wani lokacin se taga cewar ai bawa baya taba wuce wa kaddarar sa .
Baban Abul ne a tsaye Yana daura Agogon sa a bakin kofar dakin shi,se zabga kamshi yake Yi tunda ko ba komai yau ta kama juma'ahtu babbar rana,yayi wankan shi yayi kwalliyar sa Kai baka ce ma shi bane,dama Kam ba gardama Baban Abul akwai iya gayu,Kuma cikin hikima ta Ubangiji duk kayan da ze Saka a jikin sa se fa sun amshe shi..
tun da ya fito daga dakin shi yake ta magana Amman Maman Abul Bata ji ba,toh ta fada duniyar tata ta tunani,a chan cikin zuzzurfan tunanin nata ne ma taji wani tsawa da ya buga Mata,ta razana Kam,Wanda ma yaci ace ta daina razana a game da irin wannan hargagin nashi tunda dai wannan ya zame masa kamar daily routine.
musamman ma Kuma in akayi la'akari da halin da take ciki na juna biyu dan watanni shida hade Kuma da lafiyar ta ita ma .A gun maman Abul kam tunani be dace ba
Tsaki yayi Yana cewa "ki zauna kiyi ta faman tunani akan abunda be shafe ki ba ,kije ma a garin tunani ki illatar da kanki da dan cikin ki. .ni na fita se na dawo insha Allah..akwai wani abun ne?,kar se na fita a fara mun waya"..ya fada cikin halin ko in kula.
YOU ARE READING
INA AMFANIN BARIKI ??✅
RomanceLabari akan nasiru wanda ya ta'allaka rayuwa shi da BARIKI.se daga baya zai ga rashin AMFANIN barikin