💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙03
***da dare yayi yarinyan bata farka ba ,maa ne tace duk su koma gida ita zata kwana da yarinyan...
amma Sam yasir yaqi yadda yace saidai ita ta koma shi zai kwana,maa bazata iya barin shalelenta cikin tashin hankali ba,don haka su Ahmad ne suka koma gida ya kawo musu duk wani abun da zasu bukata....
Dakyar maa tasa yasir yasha tea,nan ma kadan ya taba, abun sallah maa ta shimfida ta hau jero salloli, shi kuma kujera yaja ya zauna a gaban gadon yarinyan yanata mata addu'o'i...Misalin karfe biyu bacci yafara daukan maa,shikam ko kadan bacci baya idon shi,
fuskar yarinyan yakurawa ido yana kare mata kallo, yarinyan farasol ce siririya duk da idonta a rufe ne bazai hana mutun gane tanada manyan idanu ba, ga eyelashes dinta kamar samata akayi saboda tsayinsu,gashin kanta kuwa me yauki har gadon bayan ta daga kaganta kasan er Fulani ce,haka kawai yasir ya tsinci kanshi dajin tausayinta duk tunanin shi ina za'a samu iyayenta don yasan duk inda suke suna cikin tashin hankali.
Ana fara kiran sallah ya mike ya dauro alwala sannan ya tada maa shi kuma yawuce masallaci…
*GARIN JAJERE*
Wata matashiyar mata ce da bazata wuce shekara 35 zuwa 38 ba, share barandan ta takeyi,wasu matan dake aiki a ta gefe ne suka sa dariya tare da tafa hannu,dayar tace ahaye mudai namu ido daga boko an buge da yawon bariki,dayar tace atoh ai daman kinibibi ne da karyan arziki gida ba danga… haka Ammie takasa karasa sharan nan don duk yadda taso danne zuciyanta abun ya faskara saboda da Dama karfin hali kawai takeyi don jiya bata iya ta runtsawa ba ko kadan, don haka da sauri ta ajiye tsintsinyan ta wuce daki..suku ma Dama hakan sukeso dariya suka kara sheqewa dashi,tana shiga kan gado taje tafada tafara rera kuka kamar kamar yarinyan…
Wani farin mutun ne yafito daga toilet dagani kasan mijin tane, gogen kanshi yakeyi da karamin towel jin gunji kukantane yasashi tsayawa yana kallonta,a hankali yazo yazauna a gefenta ajiyar zuciya yasauke,sannan yashafa kanta, yace naji duk abunda yafaru..nayi tunanin Fatima zuciyan ki tayi karfi by now…
Inda sabo yakamata ace kin saba da rayuwan gidan nan,akan Nihal kuma yanzu haka fita zanyi mucigaba da bincike, nima hankali na ba a kwance yake ba karfin hali kawai nakeyi,amma kukanki yanakara tayarmin da hankali..Dan Allah Fatima kiyi hakuri kinabani karfin gwiwa please…
Dagota yayi ya rungume dukansu ajiyan zuciya sukeyi…a hankali tafara magana “yanzu in Nihal tabata yazanyi da rayuwata..dasauri ya rufe mata baki da hannun shi yace kidaina fadan haka inshaa Allah ma ba zata bata ba,maganan yakeyi tare da mikewa, yanzu ma bari kiga infita idan muka gama da hukuma zanbi gidan bappah(gidan babanta) saboda su tayamu da addu'a,jikina naban nihal bata hanun mugaye.
Rigarshi ya zura ta mika mishi hulanshi tana cewa Allah yasa a dace, yace Amin..hannu ta ya rike yace Ammie! Dago ido tayi tana kallonshi,yace please no more crying please wifey! Kai kawai ta girgiza mishi,murmushi yayi ya fita.
***Ahmad (baban Nihal) nurse ne yana aiki a asibitin cikin garin jajere fatima (maman Nihal) ita kuma malamar makaratan secondary ce, dukansu asalin Fulani jajere ne kuma en boko,sunyi auren soyayya tun shekaru shatara dasuka wuce,suna zama a family house nasu Ahmad ne Wanda babansu ya Ginawa kowa part dinshi tun kafun Allah ya mishi rasuwa kuma yabar wasiya akan yanason yaranshi su zauna waje daya ko bayan ranshi,kuma dama kwata kwata mazan uku ne sai mata hudu, Ahmad kuma shine karamin su a maza amma yanada kanne biyu mata, Wanda suma duk sunyi aure tunda dadewa…Ahmad yanada halin dazai iya Gina gidanshi amma saboda wasiyyan babanshi yake zaune da en uwanshi, amma yanzu kam zaman gidan ya isheshi saboda yadda matan yayun shi sukasa matarshi a gaba basuda aiki sai hassada da gaba dasu,har sun fara zuga yayunshin ma,yanzu babu shirin kirki a tsakaninsu…
don haka yanzu duk yagama shawara da sauran en uwanshi akan Zaibar gidan kuma duk sun bashi hadin kai,batan nihal yanzu duk shi ya ruda su….
*Abdlzty💞*
