💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙02
Kofan dakin aka bude, take dukansu suka mike, likita da nurses ne suka fito duk sai share gumi sukeyi, dasauri su yasir sukayi Kansu babban likitan ne ya juyo yace waya kadeta acikin Ku?
Yasir ne ya nuna kanshi yace gani,likitan yace kabiyoni office, binshi sukayi tare da maa,suna shiga likitan ya nuna musu wajen zama yace bismillah! zama sukayi shima ya zauna sannan ya juyo yacewa maa, meye halakan ki da bawan Allah nan? Tace Dana ne na ciki na, girgiza kai likitan yayi yace "good", sannan ya cigaba yace gsky case na accident bamu cika karba ba sai da hannun hukuma,amma wannan sbd anzo emergency case ne shiyasa muka fara dubata kafun muji meyafaru, yanzu Abu na farko saikun kawo police na biyu kuma yarinyan tayi mugun tsorata Wanda shiyasa ta dogon suma kuma kwakwalwan ta ya bugu Wanda inta farka ba lallai ta tuna rayuwan ta na baya ba ma'ana zata iya loosing memory inta farka, bayan haka bata samu wani rauni a zahiri ba (physically).
Dukansu kallon doctor sukeyi har ya gama bayani, maa ce tace mun gode likita inshaa Allah yanzu za'a kawo police din,yasir kam bai iya cewa komai ba haka suka fito,Ahmad maa tasamu tace maza yaje ya dauko police, hakan kuwa akayi sunzo sunji labarin da yasir yabasu sannan da Wanda likitan yabasu,don yagaya musu duk yadda akayi akwai abunda ya razana yarinyan sbd motan bai wani bugeta ba...police sunje garin don Neman iyayen yarinyan amma da ikon Allah basu samu ba don har hoton ta an nuna musu amma sunce ba er garinsu bace.
Haka suka yini a asibitin dukansu ,maa erta maagana takira tagaya mata halin da ake ciki ita tayi girki takawo musu....
*Yasir shine babban d'a awajen hajiya fati wacce suke kira da maa, sai maryam takebinshi wacce suke kira da maagana sbd taci sunan kakarsu sai autansu Ahmad shi yake binta.yasir kakkyawan saurayine ajin karshe, kyau irin na yaran shuwa Wanda suke zubi da yaran larabawa, baban su yasir shuwa ne maman su kuma kanuri,yasir bashi da hayaniya hasali ma baya shiga harakan mutane,wannan dabi'un nashi sunkara tsanani ne tun rasuwan babansu sbd shakuwan shi da mahaifin shi shiyasa rasuwan shi ya taba rayuwanshi sosai.
wannan dalilin ne kuma yasa duk en uwanshi da mahaifiyar su sukejin tausayin shi sosai,basason abunda zai tabashi ko kadan....
*Abdlzty💞*
