💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
Jama'a kumin afuwa zantafi break na kwana biyu hope bazaku damu ba😌...thanks, luv u ol❤
📙14&15
Yau khalifa Yakama hanya cikin farin ciki da annashuwa jiyake kamar yasamo Nihal yagama.
shine bai iso ba sai daf da magrib a gajiye ya karasa gidan su Yusuf…da yake yasan da zuwan shi takanas maman shi ta ajiyewa Yusuf abinci kala kala,Allah Allah yake yagama komai Yusuf yasake bashi labarin gamuwan shi da Nihal,kallon shi Yusuf yayi yace ya naga kanacin abincin da sauri ko akwai abunda dazakayi ne?bayan yakai spoon bakin shi yace ai wallahi ingayama badon dare yayi ba dole muje inda kaga hasken rayuwa tah….dariya Yusuf yayi yace gaskiya yarinyan nan ta tafi da imanin ka,Allah dai yasa mukara cin karo da ita,Amin inji khalifa,amma kasan wannan karon inaji ajikin zanga Nihal inshaa Allah Yusuf yace Allah yasa mudace.
Bayan sun gama komai ne sunyi shirin kwanciya khalifa yazauna yayi tagumi,kafadan shi Yusuf yadafa yace khalifa me kake tunani haka,ajiyan zuciya yayi yace Yusuf akwai wani sirri na da nakeson gayama,saboda yanzu inaga kaf duniya kai kadai ka fahimci halin danake ciki…
Zama Yusuf yai yace nikuma nama alkawarin rike mana sirrin ka kuma inshaa Allah zan temake ka…murmushi me kama da yake khalifa yai sannan ya tashi yaje ya jingina da gini yasa hannun shi a aljihu yadaga kanshi sama yace Yusuf inajin tsoron gayama saboda banason rasa ka a rayuwa ta…zuciyan Yusuf ne ya buga sannan yace wane irin rasani kuma,leben bakin shi ya cije yace nasan ina gayama zaka gujeni,ajiyan zuciya Yusuf yayi sannan yayi murmushi yace indai wannan ne karka damu…
Dawowa yayi gefen Yusuf ya zauna yace abokina yau zangaya ma sirri na da babu Wanda yasani kaf duniya, duka nutsuwan shi Yusuf ya tattaro yamikawa khalifa sannan yace injinka…
Tunda mami na ta aifeni bata kara samun aihuwa ba,wannan dalilin yasa nazama Dan gata awajen iyayena,duk da ko wane Hutu muna zuwa jajere amma mami na bata bari na inyi abokai da yaran garin ,Yusuf kafi kowa sanin babu abunda nake nema in rasa a duniyan nan…
Ban taba sanin wahalan rayuwa ba sai bayan rasuwan mami na lokacin ina ss3,dangin daddy suka dage akan ko yabasu ni su rike ko kuma ya kara aure lokacin daddy yanajin daya rabu dani gwara ya auro wacce zata na kula dani,badon yaso ba ya auri wata mata me suna Rukayya,tunda matan nan tashigo gidanmu rayuwa yaqaramin kunci saboda dama rasuwan mami na yakasa Barin jikina,ita kuma tunda tagane irin son da daddy yakemin sai taji kaf duniya babu Wanda ta tsana bayan ni,tun daddy baisan meyake faruwa ba har yazo ya gane tana kuntata min,yayi shawara da en uwan shi akan zai saketa gaskiya idan bazata iya son gudan jinin shi ba,en uwan shi sukace Sam kar yafara sakin mata akaina idan nagane hakan bazan barshi ya zauna da mata ba kuma zan raina su,gashi kuma lokacin tanada ciki,suka bashi shawara akan saidai yaqaro wata mata,haka yabi shawaran su ya auri wata a damaturu saboda ita Rukayya a abuja take…amma Sam ba asamu canji ba don farida har tafi Rukayya munafurci da iya mugunta…
a lokacin bani kadai ba hatta daddy saida yayi kewan mami na saboda baisan masifan zama da mata ba sai bayan mutuwan ta.
Harna fara karatu a university of abuja rana daya daddy ya yanke shawaran fitar dani waje duk da bayason inyi nisa amma yasan hakan ne zai fi mana kwanciyar hankali, ya kaini Malaysia hmmm…Yusuf acan kuma na sake ganin sabbin rayuwa a rayuwa tah iyaye na basubar ni na saba hidima da abokai ba balle kuma en mata, Yusuf ban taba sanin duniyan mu a lalace take ba sai da naje wancan kasan, en mata ne fitsa rarru suka sani a gaba akwai wata yarinya mimie data sani agaba ranan na dage nace zan mata warning akan tabar rayuwa ta, wallahi yariyan nan daga fara magana na tun kafun na karisa tasa hannu ta a fuska ta tsala wani irin ihu sai da na tsorita,mutane suka taru kawai tahau cewa don na nemi muyi iskanci tace ita ba er iska bace shine zan mareta nan take wani saurayi a wankeni da wani mahaukacin mari wai bansan mimie kayan shi bane kuma ko bansan ba'a shiga gonan shi ba? Don haka sai ya koyamin hankali dakyar room mate dina yabashi hakuri ya jani muka tafi….tundaga wannan ranan shida abokan shi suka fara takuramin badama mu hadu a hanya sai sunyi abunda zasu sa mutane suyita min dariya…