25

42 6 1
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ




📙25




Guest falo yasir ya bude musu yashigo dasu,falon su yadawo yacewa Ahmad yakira maa,saigata ma tafito tace muje, zuwa sukai suka gaisa dasu,khalifa ne ya shaida musu abunda yake faruwa.

shuru sukai kafun yasir yace to shikenan yanzu nida kaina zanje garin ko Allah zaisa adace.

Saida sukazo tafiya khalifa ya sunkuyar da kai yacewa maa Dan Allah mama inason ganin Nihal,sosai yabaiwa maa tausayi,Ahmad kam take zuciyan shi tafara tafasa yashige ciki yabarsu,yasir ne yadafa kafadan shi yace kayi hakuri abokina yanzu Nihal bazata jure ganinka ba don tana cikin tashin hankali…kai ya jinjina tare da gamsuwa da bayanin yasir.


Suna fita yasir ya kira Ahmad a waya,saida yazo suka zauna sannan yasir yace gaskiya ban gama yadda da yaran nan ba,idan har Nihal fiancee shi ce ta yaya zaije har garinsu amma ace yarasa number iyayenta da kuma address din inda suka tafi? Don haka gobe Friday da kaina zanje garin domin samu muhimman labarai akansu.


Maa ce tayi ajiyar zuciya tace don maganan fiancee kam fiancee shice saidai akwai wani boyayyen al'amari Wanda mu bamu sani ba sai idan kaje zamuji meyake faruwa.


Nifa gaskiya kwata kwata hankali na bai kwanta dashi ba,bana ma son shi,inji Ahmad kenan,maa ce tace kaidai babu ruwanka kabari mubi komai a hankali, yanzu mukoma ciki muyi mata bayani akan halin da ake ciki.


Yana bude kofan tadago kai dasauri takalleshi tace khalifan baisamo su Ammie na ba? Karisowa ciki yai tare da cewa ya akayi kika gane shi yazo? Take idonta  ya Ciko da kwalla shshshh yace mata tare da sa yatsanshi akan lebe,yace banda kuka plss Nihal, yanzu dai kizo maa tace inkira ki hawayen ta share suka fita.


Ya yasir ne ya mata bayanin yadda sukayi,kuka tasa tace shikenan Abba na ya manta dani har ya kara aure abunshi,harda daukan matanshi su tafi ko su damu dasun barni a baya,kuka takeyi sosai maa tazo tana shafa bayanta tace karkice haka Fulani bakisan halin da suke ciki ba, yasir ne ya matso yace mata ki kwantar da hankalinki gobe zanje dakaina muji yadda ake ciki…

cikin kuka tace yaya kabarsu kawai in sun dawo ai zasuji labari idan har sun damu zasu nemeni....karkice haka komeye iyaye sukai ba'a fushi dasu kinji,shuru tai bata kara cewa komai ba,sai kuka kawai.


Washegari yasir yana zuwa office bai jima ba ya kama hanyan jajere, yana zuwa gidan baffah ya nema kakan Nihal, bai wani sha wahalan nema ba yasamu,yaje baffah ya karbe shi a mutunce bayan sun gaisa yake shaida mishi abunda ke tafe dashi bakaramin jin dadin labarin yayi ba da sauri ya kira inna yake shaida mata wacce Nihal take hannu shi yazo itama zuwa tai suka gaisa…sannan ya kwashe duk abunda yafaru yagaya musu,take baffah yace mishi yaji dadi da Nihal ta fada hannu mutanen kwarai irinshi amma khalifa kamar yadda yagaya musu ita zai aura karyane don lokacin data bata shida kanshi yazo yace kota dawo yafasa,babu kalan rashin mutuncin da baiyi ba….
Don haka karma subar shi ko kallon Nihal din yayi.. Sosai abunda baffah yafada yabaiwa yasir mamaki,to yanzu meyake nema daya dage dason ganin ta? Kodai dgsk ne dabakin shi aka dauketa? Koma dai yayane zaigano a hankali.


Take baffah yakira Abba ya sheda musu abunda yake faruwa… yana gayawa Ammie ta gigice akan ita dole saita dawo a ranan dakyar ya danne ta yadda washegari.


Yasir number shi da address dinshi yabasu akan duk lokacin da suka zo su ne meshi…sannan yakoma gida,yaje yabasu labari yadda yayi dasu baffah dakuma dalilin tafiyansu abuja,Sai lokacin taji hankalin ta yadan kwanta don koba komai taji ansa mu cigaba a gidan su,saidai abu daya yake bata haushi wai anyiwa Ammie ta kishiya?hmm.

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now