💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙13
Yau sati biyu kenan tun daga wancan ranan khalifa ya canja rayuwan shi, ya riqe ibada sosai,yace babu abunda yafi karfin addu’a,gashi ya rame sosai,Raman shi ba karamin tayarwa da daddyn shi hankali yakeyi ba,kuma yanzu bayayin wani abun magana.
Shakuwa tsakanin Ahmad,yasir da Fulani ba'a magana,tazamo wani bangare na jikinsu ji sukeyi kamar tunda can er gidan ce,itama yanzu ji takeyi kamar bazata iya Barin gidan ba,haka tsakaninta da bena ma sun saba sosai tun bena tajin kishinta harta gane Nihal bason Ahmad takeyi ba sannan ta sake ranta .yau Ahmad zasuje practical asibiti tunda dare yagayawa Fulani akan tashirya zasuje tare..don haka yau ko baccin safe ba tayi ba don yace mata karfe takwas zasuje,tana gama karatun ta ta shirya tsaf…ita taje yahada musu breakfast sukaci dukan su uku,maa kam cewa tayi karsu tasheta don zatayi bacci,tare suka fita ya yasir yashiga motan shi suma suka shiga nasu.
sun fara tafiya Ahmad ne ya juyo ya kalleta itama shi ta kalla murmushi yayi,yace yau dai asibiti zamu shiga ba gun karatu ba balle a ebowa yaya gulma,dariya tayi tace ai saidai in Juliet dinka bata gun nasan dole a taba soyayya nikuma saina shafawa yaya na…girgiza kai yayi yana kallon kwalta sannan yace saidai kinsan bamuyi nisa ba zan iya sauqe ki ki koma gida da kafa,juyowa tayi ta langabar da kanta jikin kujera tace haba ya Ahmad dina yanzu saika ita sauke fulanin ka akan kwalta? Murmushi yayi tare da kashe mata ido daya yace kema kinsan wasa nakeyi bazan taba iya Barin ki akan hanya ba,murmushin jin dadi tai.
Sun isa school ya dauki su benazir suka wuce TH inda zasu jira en ajinsu..tunda suka fara Ciro lab coat dinsu da abubuwan amfani asibiti,hankalin Nihal yafara tashi,hankalin ta bai gama tashi ba saida suka shiga ward tafara ganin nurses da patients take taji jiri nason ebanta wasu irin Abu tafara gani a idonta..dakyar ta karisa kusa da Ahmad hanun shi ta rike dayan hanun ta yana rike da kanta yana ganin halin da takeci dawuri ya riketa yana cewa fulani, babu abunda takeji akanta banda NIHAL! Riketa yayi ya fita saboda kar malamin su ya mishi fada direct mota yawuce da ita ya bude sit din baya ya kwantar da ita,cigaba yayi da kiran sunan ta amma ita a kunne ta Nihal takeji a maimakon fulani…sai kuma tafara ganin wata mata na mata bye bye wacce Ammie ta ne amma bata gane waye bace,a hankali tace mishi zan sha ruwa! Da sauri yadauko Ronan ruwan yasa mata a baki tana cikin sha bacci ya dauketa…ajiyan zuciya yayi sannan ya kwantar da ita ya kunna mata AC sannan ya koma wajen colleagues dinshi,duk abunda ake musu hankali shi baya wajen duk hankalin shi nakan fulani har Allah Allah yake agama yaje dubata,ita ko bena duk tana lura dashi ta fahimci Sam hankalin shi baya wajen don haka itama saitaji duk hankalin ta ya tashi duk ta zaku taji meyake damun shi,ana gamawa Yakama hanyan fita ba tare da yabi takan kowa ba ya fita yana sauri,da sauri itama tabi bayanshi zuwa yayi ya bude motan yaga har yanzu bata tashi ba, sit din direba kawai yashi ga har zai tada motan ya juyo maganan bena,tana sayri tace,haba honey tafiya bako sallama, meyake damun ka naganka cikin tashin hankali, nuna mata Nihal yayi da hannu yace mata batada lafiya zankai ta gida,zare ido tayi tace subhanallah to kabari in rakaku mana,kai ya girgiza mata yace karki damu nagode,tada motan kawai yayi ya tafi yabarta a wajen,tun a hanya ya kira ya yasir ya gaya mishi shima hanyan gidan Yakama kuma ya kira doctor a tare suka shigo gidan tare da Ahmad da sauri ya bude motan yace suma tayi ne ,Ahmad yace a ah,bacci takeyi Kusan awa uku kenan,ido ya yasir ya bude,da sauri ya kinkimeta sai cikin parlor jin hayaniyan su ya fito da maa,ganin fulanin ta a kwance itama ta kariso da gudu tana cewa nashiga uku meya sameta?Ahmad ne ya gaya mata abunda yafaru…yasir ta kalla tace ka kira likitan ne?yace mata eh,sai ko gashinan ya iso ganin su a tsatstsaye ne ya sashi karisowa da sauri yana tambayansu meyafaru?Ahmad ne yabashi labarin…murmushi doctor yayi yace karku damu inta tashi zata tuno wani abun da yashafe ta,ajiyan zuciya maa tayi tace Allah yasa, amma dai Allah yasa kartayi irin wancan baccin nata me tsayi,yace no bazatayi ba…kafun ya rufe baki sai gashi ta tashi,da damuwa sukayi kanta kowa na kiran sunan ta kallon su takeyi daya bayan daya,maa ne tace tace sannu fulani... hannun ta riko tace mama suna na Nihal! Duka tsayawa sukai suna kallon ta, daga kai tayi tana kallon ya yasir tace yaya suna na Nihal na tuno wallahi suna na Nihal hawaye ne yake fitowa a idonta kuma tana murmushi…yasir da Ahmad ne suka maimaita sunan a tare NIHAL!! Girgiza musu kai tayi tana murmushi kuma hawaye nabin idon ta,ya yasir ne ya matso yace mata akwai inda yake miki ciwo? Kai ta girgiza mishi halamun a ah,wasu magani doctor nasir ya rubuta yace asayo mata ,Ahmad ne ya karba ba bata lokaci ya tafi sayowa.
ranan haka suka yini suna lallaba ta har sai dare kowa ya tafi makwancin shi…ya yasir dai saida ya tabbata yabata duka maganin ta kwanta sannan ya juyo zai tafi har ya isa bakin kofa ya Sai kuma ya juyo itama tsayawa tayi tana kallon shi,yace bayan sunan ki ba abunda kika tuna? tsayawa tayi kamar me tunani sai kuma ta girgiza kai tare da cewa babu… sannan yace kinada suna me dadi,amma saidai ni bazan daina ce miki angel ba,saboda kin kawo mana farin ciki meyawa a rayuwan mu,murmushi tayi tace nagode ya yasir Allah yasaka muku da alkhairi, nima bazan manta alkhairinku gareni ba.
Ahmad kuma yau yarasa meyake damun shi,tunda abun nan yafaru yakasa samun kwanciyar hankali, ya rasa gane ciwon Nihal ne ya tayar mishi da hankali ko meye? Bena ce tafado mishi arai Sai yanzu ya tuno da ita wayanshi ya dauka missed col dinta yagani dayawa,kiranta yayi a take,tana dauka ajiyan zuciya tasauke,tare da marairai cewa tace Allah sarki honey na, hankali na yakasa nutsuwa tunda ka tafi cikin tashin hankali,pillow yaja ya kwanta sannan yace I’m sorry baby,wlh lokacin bana hayyaci nane,ya jikin nata? dasauki ta warware,tace toh mashaa Allah, haka suka Dan taba hira yace mata yanajin bacci sukai bankwana,benazir yanzu tafara damuwa gaskiya don shekaransu biyar kenan suna tare amma Ahmad bai taba mata maganan zai tura gidan su ba,kawayen ta sun dameta da yaudaran ta yakeyi,kuma gashi bata kula kowa dalilin shi…
Shikam da yace bacci yakeji Sai gashi baccin ya gagareshi inya rufe idon shi babu abunda yake gani Sai fuskan Nihal….tashi yai ya zauna,tunani yayi dare yayi da yaje ya duba jikinta,wayan shi ya dauka yafara dialling number ta, har bacci yafara daukan ta taji wayan ta na kara dauka tayi,tace hello!acikin muryan bacci,rufe idon shi yayi tare da cewa sorry na tasheki a bacci ko? Kai ta girgiza kamar yana kallon ta tace a’ah badamuwa, kwanciya yayi a Hankali, yace dama inason inji yaya jikin ki ne…murmushi tayi tace nawarke ya Ahmad…ajiyan zuciya yayi yace mashaa Allah dama nakasa bacci ne ina tunanin ko ya kikeji…dariya tai har saida sautin muryanta yafito tace ka kwantar da hankalinka lafiya na kalau nawar ke,murmushi yayi yace toh shikenan naji dadin jin haka ki kwanta kiyi bacci kinji…tace nagode yaya, na nagode da kulawar ka gareni….ji yai bugun zuciyan shi yakaru don haka ko bankwana bai mata ba ya kashe wayan.
Yau satin khalifa uku a abuja,amma fa hakurin shi ya Gaza duk da kullum Yusuf yana kwantar mishi da hankali akan idan yadan Dade shi zaisa ko yazo borno daddyn shi bazai damu da ya dawo gida ba,amma yau kam ya dage dole kawai zai gayawa daddy shi zaiyi tafiya…. Side din baban shi ya nufa,tun daga window daddy yake hango shi, ganin yadda ya rame ba karamin tausayi yabashi ba, tunanin abunda yakesa khalifa irin wannan Raman yakeyi, bude kofan parlor yayi tare da sallama, da sakin fuska daddyn shi ya amsa mishi hakan ba karamin dadi ya mishi ba don yafara ganin halamun nasara,tsugunawa yayi daga can nesa yace ina wuni daddy,lafiya khalifa ya aiki?yace Alhamdulillah, kallon shi yai sosai yace bakada lafiya ne?kai ya girgiza mishi,yace to meyake damun ka haka kake ramewa…shuru yai baice komai ba,Sai kuma yace,daddy inason zuwa Maiduguri…shuru yai daddyn kafun yace mezakajeyi acan, bai dago kai ba yace akwai wani aikin dazamuyi tare da Yusuf ne….shuru daddyn yakarayi sannan yace toh shikenan Allah ya tsare….wani sanyi khalifa yaji a zuciyan shi…fara’a ne ta bayyana sosai a fuskan shi yace nagode daddy…tashi yai cikin hanzari ya nufi side dinshi kan gado yafada yace inshaa Allah wannan karon bazan dawo ba saina samo ki, Hasken rayuwa tah.
Tunda abun nan yafaru Ahmad bai sake fita da Nihal ba don tsoro yakeji kar wani Abu yasa meta…saidai kuma duk yadda yake dannewa abun yana son fin karfin shi don tunaninta yanason hanashi karatu kome yakeyi kawai saiyaji yadawo gida yazo yaganta…sai yanzu yake gane halin da bena take shiga dalilin shi,kuma yanzu yakarajin tausayinta don yaqara tabbatarwa da kanshi ba soyayya bane sunan abunda yake mata ba shakuwa ne (Allah sarki Bena inji zeety).
*Abdlzty💞*