27

45 4 2
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ




📙27



Tayita kiran Benaxir tagaya mata bikinta amma wayan ta baya shiga.


Yaune akayi walima  saura kwana daya daurin aure kenan kuma a ranan ne yasir suka fara samun nasara a case din daya tsaya mishi a wuya kuma da ikon Allah sun samu sa'an gano wasu daga cikin wayanda sukayi kisan,kuma  har an kamo yaran da sukai kinsan sai a zama nagaba za'a yanke musu hukunci, da farin cikin shi yakira Nihal ya gaya mata itama ta tayashi murna sosai.

Acikin gidan dama akwai side din yasir da Ahmad me 3bedrooms da kitchen da komai da komai,tun baban su yanada rai ya Gina musu amma tsabar sakalci irin nasu babu Wanda yataba  zama awajen kullum suna tare da maa,nan aka gyarawa Nihal sosai , aka canja komai na gidan, maa ta tsaya akayi komai mekyau,koda Abba ya kira  akan za'azo mata Jere ma, maa cewa tayi ai tamata komai saidai in idan da abunda takeson Akara ne,Abba yadage akan baza'ayi haka ba dawainiyya zai mata yau shi da yakamata ace yadauki nauyin kamai ne zata dauke mishi,haka dai sukayita jayayya karshe ya kyalle ta amma sai da ya tura mata kyautan million uku,saboda yace bazaiyu yabar mace da hidima ba.

Yaune aka daura auren YASIR JIDDA SHUWA DA NIHAL AHMAD LAMIDO a sadaki naira dubu Dari Wanda baffah ne yabiya.
Tunda aka daura auren zuciyan ta yake tsinkewa balle da aka fara
Guda wai masu daukan amarya sunzo shikenan kuka ya balle mata,haka aka mata nasihu irin Wanda aka sabayiwa amare aka dauke Nihal sai borno garin shehu.

Daf da magrib suka isa side din maa aka kaita direct nan dangin Abban ta suka damqa amanan a hannun maa,ranan babu yadda yasir baiyi ba maa tabar shi ya yaga Nihal amma taking fir taki wai sai gobe…shi kuma haka kawai yaji ya kasa samun nutsuwan bari sai goben, maagana yasamu yace Dan Allah tasan yadda zaitayi takawo mishi Nihal kofan kitchen nabaya yana jiransu a wajen, tsokanan shi tayita yi wai yakasa hakura yace mata eh yaji koma meye zata ce,cikin sa'a kuwa tana zuwa tasamu Nihal ita kadai ce don dama ba kawaye take da ba,da sauri ta dagata tajata suka lallaba ta kitchen, itakam binta da kallo kawai takeyi don bata gane inda takeson kaita ba,tana bude kofan ta turata yasir tagani a tsaye,tace tam gata nan kuma minti biyar nabaku kafun maa ta ganoni,ta rufe kofan kitchen din,ajiyan zuciya kawai ya sauke,hannu ta yakama side dinsu yawuce da ita saida sukazo bakin kofan tatsaya tace yaya maa fa zata nemeni! Juyowa yayi kawai yadagata cadak kamar er baby,idonta ta bud duka tana mamaki kamar ba ya yasir dinta ba, bai tsaya ko ina ba sai akan 3seater ya direta…
Gwiwanshi yasa akasa ya riko hannu ta duka biyu, numfashin shi ya sauke a hankali hannun ta yasa a kirjinshi yace, Nihal inason ki fiye da yadda kikejin bugun zuciyata, please kimin alkawarin zama dani har karshen rayuwa ta! Hannu shi ta rike tace please yaya meya kawo duka wannan abun inason ki cemin kema kina sona ne,hannu shi damke tace yaya inason ka fiye da yadda nakeson kaina and trust me tun randa nafara ganinka zuciya ta ta harba, rufe idon shi kawai yayi sai hawaye zatai magana yayi saurin tashi yahau kan kujeran ya kwanta, ya daura kanshi a kan cinyanta ya lumshe idonshi,itama haka kawai taji duk jikinta yayi sanyi, hannu tasa tashare mishi hawayen daya bi kumatun shi,tace meyasa ka kuka yaya? Murmushi kawai yayi ba tare da ya bude idon shi ba yace mata nima ban sani ba,karewa fuskan shi kallo tafarayi sai yauma taga Ashe duk kallon da take mishi bata taba ganin ko kwatan kyanshi ba,a hankali takai hannu ta tana shafa gashin kanshi kara rufe ido kawai yayi yana smiling, a hankali ta gangaro gashin giran shi, gashin idon shi da suka tsatstsaya kamar na mata tazubawa ido, a hankali ta iso harkan bakin shi,hannu yasa ya rike yatsanta sai lokacin tafarga da shirmen da takeyi take ta dibibice tafara yunkurin tashi amma takasa, juyowa yayi ya zuba mata manyan idanun shi,duk sai taji kunya yakamata ta kasa kallon shi hannu shi biyu yasa yazagaye kugunta take taji tsikar jikinta ya zuba,narai narai tayi da idon ta tace yaya maa fa..ko karisawa batayi ba sukaji knocking, kofan ta kalle shi a tsorice,tashi yayi yana murmushi yace relax baby a gidan mijin ki fa kike duk kike wani firgita,kumatun ta yalakata yace bari na duba.

Yana budewa maa ya gani tana tsaye,keyanshi yafara sosawa yace maa da…ma zan ba..ta abu ne,duk sai i'ina yakeyi, cewa tayi nikam fitomin da yata koma me zaka bata saika jira gobe,Nihal najinsu ta tashi tagyara gyalenta ta taho…hanya kawai yabata maa takama hannun ta ,shima daya hannu yakama juyowa tayi takalleshi ta bude duka idonta irin halamun yabari mana,idonshi daya ya kashe mata ta wafce hannu ta,suka wuce…maa sai mita takeyi wai maza basuda kunya,yanzu ga duk shuru shuru irin na yasir amma don dare daya ya kasa hakuri, ita dai Nihal duk kunya ya cikata saima haushin kanta takeji data biye mishi gashi yanzu yasatajin kunya.

Washegari tun karfe goma en jajere suka tafi kafun azahar duk en biki sun watse, zuwa la'asar maa tasa ankara gyara mata ko ina,ansa turaren wuta a gidan an kunna AC,sannan tafara gyara Nihal,tasha tsummin turare kam,na wanka daban banda Wanda aka turarata dasu,kamshin jikinta kadai ya ishi gidan basai ansa wani ba,maagana sai tsokanan takeyi wai gobe sassafe zatazo karban sauran Kazan ta,sosai Nihal takejin tsoron abubuwan da maagana take cewa,duk sai taji jikinta ya mutu.

Bayan sallah ishah maagana ta rakata side dinta,sosai maa tamata nasiha sannan suka tafi, karfe takwas ya yasir ya shigo gida tare da Ahmad dawasu abokan shi guda biyu,side din maa suka fara zuwa ta musu nasiha sosai sannan suka rakashi side dinshi maagana kadai suka samu a parlor.. Take suka fara mata maza tafito musu da amaryansu tace ai babu megani amarya sai sun sayi bakin ta, rafan 1k yasir yacire yace mata gashi amma dai shi bakin amaryan shi babu kudin da zai sayeshi,itakam guda tasa tace Kansu akeji itakam ta kara wuta,daki taje tafito musu da Nihal nan aka Dan taba raha kafun kowa ya watse Ahmad aka bari a last saboda  yasir yace mishi yatsaya, suna watsewa shima mikewa yayi yana hamma yace wallahi yaya bacci nakeji kasan duk wahalan bikin nan akaina yakare..zama yasir yayi yace Ahmad inason inbaka amanan Nihal Dan Allah idan bana nan kana kula da ita kar kabari ta nemi abu Tarasa kaji? shuru yai sannan yace watannan yaya na lura bada amana bayama wahala daga zuwan Nihal zuwa yau kabani amanan ta yakai sau dubu…duka dariya suka sa,yasir yace to yazanyi saboda banida Wanda yafika ne,dafashi Ahmad yayi yace kar ka damu inshaa Allah idan ina Raye matar yaya na bazata sha wahala ba,murmushi yayi yace nagode Dan uwana.

Juyowa yayi kan Nihal yace to anty nima ga amanan yaya na ki kulamin dashi don kinsan banida kamar shi,kai kawai ta girgiza mishi tana murmushi, yace to saida safe nabarku lafiya.

Zama yayi agaban ta ya nade kafanshi tare da zura mata ido, gyalenta taja ta rufe idonta,hannu shi yasa ya mikar da ita suka tashi tare hugging dinta yayi yanajin kamshin turaren ta yana kunce mishi kai a hankali yajanye jikin shi yace zamuyi sallah ko,jekiyi alwala nima bari nayi …rakata yayi har kofan toilet din sannan ya wuce nashi dakin,data fito bata ganshi ba dakinshi taje dubashi taga shima lokacin yake fitowa a toilet yace yauwa kizo muyi sallah anan abun sallah ya shimfida musu.

Suna idarwa sukaji ana musu wani irin knocking kamar za'a balla kofan juyowa yayi ya kalleta itadinma shi take kallo da sauri yatashi, saurin Riko hannu shi tana girgiza mishi kai,murmushi ya mata yace karki damu kinji,gefen fuskan ta yashafa da hannu shi take hawayen idon ta suka zubo.

Yana bude kofan aka wurgo su maa da Ahmad da me aikinsu harda me gadi, tsabar tsikewan zuciya baisan lokacin da yayi baya baya ya fada kan kujera ba, shigowa suka farayi kowa da mask a fuskan shi, mutanen gidan kuma duk sun daure musu hannu ta baya sannan sun rufe musu baki,jinshi shuru ne yasa Nihal fitowa abunda tagani shiyasa kame a jikin gini zuwa sukayi suka fincikota sai lokacin yasamu karfin tashi da karfi ya ture Wanda yajawo ta yana nuna shi da yatsa yace karka sake tabamin mata ta,dariya suka sheqe mishi dashi,ogan cikin su ne yace muba abunda zamu da matan ka saboda ba ita mukazo nema ba,ajiyan zuciya yayi yace me kukeso kufada konawa ne zamu Baku amma karku taba kowa a gidan nan…dariya suka kara sa mishi sannan yace karka damu muba  kudi mukeso,kai mukazo nema,rufe idon shi yayi cikin Bacin rai ya damke hannu shi sannan yace me nayi kuke nema na,binga yaji akan shi take Nihal tasa hannu akanta tace Dan Allah karku kashe shi,hannu tadaga mata halamun tayi shuru,sannan yayi murmushin takaici,maa yajuya ya kalla idon ta sai zubar da kwallah takeyi tana girgiza mishi sannan ya kalli Ahmad yaga yadda idonshi sukayi jajawur kamar zasuyi Jini shima kai yake kada mishi…kallon mutanen yayi yace dadinta ba me tabbata a duniyan inma kasheni kukayi kuma watara dole zakuje inda na tafi,dariya suka kwashe dashi sukace waya cema mu muna tsoron mutuwa aibama tsoronta… dayan ne yayi tsawa yace kugama dashi yana bata mana lokaci!!! kafun yayi magana suka daukeshi da bindiga a kirjin shi,wani irin ihu Nihal tasa tafadi ta sulale a wajen ta suma,sukuma take suka tsallekeshi suka fita.

Ahmad ne yaya rarrafa yadinga girgizata da kafanshi amma shuru,dakyar ya lallaba yaje wajen table na glass yadinga goga hannu shi harya samu abunda aka daura shi yafara sullubewa da sauri ya zare ya sunce bakin shi da gudu yayi kan yasir ihu yayi me karfi yace yaaaayaaaaaaaah!!! Hannu daga ya nuna mishi maa,da sauri yaje ya sunce su,sannan ya ebo ruwa ya watsawa Nihal itama a firgice ta tashi da gudu dukansu sukayi kan ya yasir,kuka maa takeyi kamar ranta zai fita tana cewa wayyo babana karka tafi kabarni…hannu shi da yake rawa sosai kamar bazai iya dagashi ba ya fara share mata hawaye,maza Ahmad dauko mana mota muyi asibiti kayi sauri,harya tashi yasir ya rike hannun shi yajawo na Nihal ya hada,tsayawa kallon shi sukai dakyar ya bude bakin yace Ah..mad Ama..na,kallon Nihal yayi data dawo kamar mutun mutumi saboda kwakwalwan ta yatsaya cak baya iya mata aiki balle tayi kuka…dasauri Ahmad yatashi yakawo mota har kofan wajen, shi da megadi suka ciccibeshi suka sa a motan shima Ahmad din duk jikin shi rawa yakeyi shida maa suka shiga gaba sai nihal tashiga baya tadauki kanshi tadaura akan cinyan ta fuskanta ya kurawa ido yana murmushi hawaye nabin gefen idon shi,abunda yafaru jiya ta tuno,take tasa wani kuka me tsuma zuciya,tana cewa Dan Allah yaya karka tafi kabarni,hannu ta ya damqe gam yace ina…son ki,da sauri ta rike fuskan shi duk jikinta na bari tace inason ka  yaya na,Ahmad gudu yakeyi baimasan kalan tukun da yakeyi ba,suna Shiga akayi saurin turasu emergency…

Likitocin basu fi minti goma da shiga dashi ba suka fito duk suna cire nose mask dinsu a kideme su Ahmad sukayo Kansu Nihal harta farajin hajijiya ma,kamar daga nesa take jiwo maganan su suna cewa we are sorry maa bullet ya riga yashiga zuciyan shi…bata karisa ji ba ta sulale kasa,faduwanta sukaji kuma aka sakeyiwo kanta da gudu.

💔💔💔💔💔💔💔💔😭😭


*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now