18

38 5 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ




📙18


Yau tun safe Nihal bata sake kwanciya ba ita da kanta ta hadawa ya Ahmad bun karyawa, ya yasir zai wuce office ya leka dakinta yaga bata nan don haka direct yawuce kitchen don yasan bata wuce nan ba,tana firan dankali yazo yace umh.. Yau fa Angel badama duk na tarban ya Ahmad din ne,murmushi tai kawai tace ina kwana yaya,lfy dafatan kintashi lafiya? Lafiya,karfa kina stressing kanki ,dariya tai tace karka damu yayana bazan wahala ba,agogo ya duba yace toh nikam zan wuce, da sauri tace Dan Allah ka tsaya ka karya na Riga nagama ma naka,baki ya bude yace yanzu har kinyi wani girkin tace eh…gashi can a dinning na soyama chips da chicken pepper soup,nadama ma oat nasama ruwan tea a flask, kallon ta kawai yakeyi tanata bayani har ta gama bai Ankara ba,saida ta tafa hannu ta a gaban fuskan shi,sannan ya dawo daga tunanin da ya tafi,kallon shi tai tace yaya tunanin me kakeyi, kanshi yashafa yace kawai ina tunanin yadda kikayi abubuwa dayawa ne a Dan kankanin lokaci, murmushi tai tace nidai yaya kaje kayi sauri karka makara,yace toh Angel nagode sosai sannan ya nufi dinning.


Kafun 10 tagama komai sannan taje tai wanka tayi gaye me daukar hankali,wayanta ta dauka takuna data duba ya Ahmad tai taga baya online…a haka bacci ya dauketa, nocking din dataji ne ya tada ita batasan yaushe bacci me nauyi ya dauketa haka ba,tashi tai ta bude kofan tana murtseke idonta,tsaye yai ya harde hannun shi a kirji yana kallonta yana murmushi, saida tagama ta bude idonta ganin shi tai ya tsare ta da ido,ido ta zare tace ya Ahmad yaushe ka shigo? Yace kekam bakinata baccin ki ba, ko ki kirani… shagwabe fuska tai tace kaifa nake jira bacci ya daukeni…ni kullum saika samomin laifi ta tura baki.. A hankali yace mata it’s ok  nima wasa nake miki yanzu shigowa na,murmushi tayi tace sannu da dawowa yaya muje kaci abinci…kanshi yadan Sosa bayason yace mata yaci abinci yasan bazasu shirya ba,don haka yace mata bari nakai kayana daki nadan watsa ruwa sai inzo ko? Kada kanta tai halamun gamsuwa kuma tana murmushi tace to yaya saika fito bari injira ka a parlor, shima murmushin ya maida mata,yawuce daki.

Agogon parlor ta duba tana zama taga har sha biyu tace Ashe dai rana yayi.


Yagama komai ya fito ya sameta tana jiranshi,dinning suka wuce ita tayi serving dinshi.

Ahmad yayi santin abinci nan ba kadan ba harma ya manta da dazu yaci, sai duri yakeyi yanata sambatun santi ita ko sai dariya takeyi…a haka maa ta fito ta samesu, murmushi tai tace waton nan dai in Fulani na nan su Ahmad har mantawa akeyi dani…shafa kanshi yai yace ai na dauka kina bacci ne shiyasa banson na tasheki…hararan shi tai tace kaidai zaka Kare kanka kawai ai da ko ina baccin saika tadani, murmushi kawai yayi yace afuwan swt mum.

Nihal ta kalla tana murmushi tace sannu Fulani na godewa Allah Daya kawo ki cikin rayuwan mu, da kullum ina tunanin inna mutu ya Ahmad da yasir dina zasuyi saboda mutuwan baban su duk Shiya taba rayuwan su Wanda koni nan sainayi dagaske nake sasu dariya,mishkilallun yara ne wanda nasan dakyar in zasu baiwa mace fuska balle tazamo musu farin cikin rayuwa sai gashi daga zuwan ki komai nasu ya canja…hakan bakaramin dadi yakemin ba,shiyasa nakeson duk randa muka samu iyayenki zan rokesu alfarma subarmin ke har zuwa lokacin dazakiyi aure.. Damm! Zuciyan Ahmad ya buga ,take yafara tunanin yanzu fa duk randa Nihal tai aure shikenan sun rabu da ita, bai taba kawo wannan tunanin a ranshi ba, to ma tukunna waye zata aura? Take yaji duk ya Shiga cikin rudani...


Kuka maa yai tana cewa haba Fulani kuka kuma? Ko dai bakyason zama damu ne? Kai ta girgiza tace mama nima inaji araina bazan iya rabuwa daku ba,ba kukan bakin ciki nakeyi ba farin ciki ne yasani kuka…saboda ni ya kamata nagode muku amma kuma kullum ku kukemin godiya, bazan taba manta alkhairinku gareni ba,hannu maa tasa tana share mata hawaye tana murmushi tace its ok my daughter ki daina wannan kukan kinji na tabbata yadda nakejin ki araina haka ma yarana suke jinki kuma inshaa Allah mun zama zuri'a daya har abada kinji hannu tasa ta rungume maa sosai tana kuka…Ahmad kallon su kawai yakeyi.


Tun ranan da sukaga Ahmad hankalin khalifa ya kasa kwanciya magana yake aranshi wai shin ta yaya za'ace wancan guy din ya bace musu acikin borno kuma ace basu kara ko halamun ganin shi ba? Yusuf ne yadafa kafadan shi,yace haba khalifa meyasa kakeson sawa kanka damuwa ne bayan kasan bakada karfin iko akan komai sai abunda Allah yaso kuma yatsara shi zai faru…addu’a yakamata mudage dashi ko Allah zaiji kanmu yabamu sa'a akan bukatanmu…

sosai maganan Yusuf ya kashe mishi jiki don yasan duk abunda yafada gsky ne,ajiyan zuciya yayi yace hakane abokina gaskiya ina alfaharin samun ka a rayuwa ta kana sani inatuno da Allah a dukkan lamura na, murmushi Yusuf yai ya bugi kafadan shi yace toh ai saika tashi mufita Sana’a ko… dariya yai yace gaskiya kam don ko bazan ganta idan ina yawon nemanta yafimin kwanciyar hankali akan zaman gida…sanda suka shiga mota ne khalifa yacewa Yusuf yau kuma ina zamuje?Yusuf yace umh mufara zuwa wajen kullum(wato inda Yusuf yafara ganin su) dama kullum nan suke fara zuwa kafun suje ko ina,nan take suka kama hanya.


Suna breakfast akan dinning Nihal ce ta dago tana kallon Ahmad dagowan dazaiyi sai suka hada ido murmushi yai ita kuma ta sunkuyar dakai,yace Yadai Nihal? Kamar da akwai magana a bakin ki? Cikin shagwaba yadda tasaba mishi tace ya Ahmad yau zamuje gidan maagana? Dan bata rai yai yace nifa ba zuwa gidan maagana ba yanzu sai tace saikin kwana, murmushi tai tace  bazan kwana ba su Zara kawai nakeson gani, kuma kaga kai ka musu alkawarin inka dawo zamuje gashi harkafi sati da dawowa…yace toh shikenan ki shirya muje,yasir ta kalla tace yaya na zamuje tare ko,kai ya girgiza halamun a'ah, yace nikam bandani,fuska ta bata cikin shagwaba tace haba ya yasir…murmushi yai yace karki damu wataran zamuje amma yau inada meeting kuma bansan yaushe zamu fito ba,badon taso ba haka dole ta hakura.


Sunfito kenan har zasu kama hanya tace lah ya Ahmad Dan Allah mufara zuwa park din nan mana…shuru yai yana tunani yace wane park,tace Wanda muka taba zuwa din nan har wani yaro yaji ciwo… ohh natuna badamuwa bari muje,juyawa yai suka kama hanyan park din.


Shiko khalifa tunda Yusuf ya nuna mishi inda ya taba ganin ta,shikenan yasamu aiki kullum sukazo sai ya kure wajen da ido yai ta imagination kala kala,ji yake kamar zai ganta…


Yusuf ne yagaji da zama yace mishi guy gwara fa mutafi rana tanayin zafi, ajiyan zuciya yayi sannan yace mishi muje…kafadan shi Yusuf ya buga yace don’t give up friend inshaa Allah zamu ganta,yace Allah yasa.

Sannan suka shiga mota, motan su tana fita nasu Nihal yana shiga clashing sukai a bakin gate saidai babu Wanda yaga Dan uwan shi,ita Nihal tana kallon Ahmad tanata mishi surutu, shi kuma khalifa ya kurawa kwalta ido yafada cikin tunanin daya saba ko damuwa ya duba gefe ma baiyi ba, haka suka wuce juna.



*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora