💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙11
Acikin wannan hayaniyan harda Yusuf abokin khalifa ai tunda yaga Nihal hankalin shi yatashi yafara Neman khalifa a waya amma Sam baya shiga saboda yana hanya,juyowa yai a dabaran ce yadauketa Hoto,harsai da maman yaron nan tazo godiya sannan yagane da Ahmad suke tafe…
ya yasir ne yazo yagansu cirko cirko da sauri yakaraso yake tambayan su me yafaru, Ahmad ne yagaya mishi, ganin ta dayayi a rude kamar hankalin ta baya jikinta Shiyasa shi gaggawan ce musu maza sukoma gida take suka wuce parking space suka shiga mota.
shi kuma Yusuf ya juya turawa khalifa voice note a WhatsApp, juyowan dazaiyi kawai yaga sun bace, nemansu yahau yi a wajen amma ko kadan bai sake ganisu ba,dunkule hannu shi yai yanaushi iska,sukuma tunin sun kama hanya wani babban shagon saida waya yatsaya yace musu minti biyu yana zuwa,yana shiga yafito suka wuce gidan,suna isa ana kiran magrib don haka yana parking suka wuce masallaci shida Ahmad ita kuma tashiga ciki…
maa ta tarar a parlor tana ganin ta ta bude baki cikin mamaki tace lafiya Fulani naga kindawo ba mayafi nan tabaiwa maa labarin abunda yafaru sannan suka wuce donyin sallah…
saida akayi isha suka fito Ahmad ne ya kalli yasir yace yaya anya kuwa yariyan nan ba ma'aikaciyar asibiti bace?yasir ne ya tsaya yace meka gani? Yace yadda naga tabaiwa yaron nan temako kuma harta gane abunda yadace a mishi..shuru yasir yayi sannan yace is possible don ranan ma doctor nasir yayi magana shigen wannan, dafa kafadan Ahmad yayi yace kasan me nakeso dakai?kai ya girgiza mishi halamun a'ah,sai yasir yace inason yakasan ce duk randa zakuje aiki asibiti kadauke ta kuje tare zai temaka sosai wajen dawo da tunanin ta,kai yakada halamun gamsuwa sannan suka wuce gidan.
ita kuma tunda tashiga tayi sallah hankalin ta yakasa kwanciya duk jinta takeyi arude…suna shigowa gida ya yasir yakira ta ganinta yayi duk wani irin,tambayan ta yayi ko bata da lafiya ne?tace lafiya na kalau saidai tunda naga yaron nan yaji ciwo hankalina yakasa kwanciya inajin kamar nasan wani abu irin haka..shuru duka sukayi sannan ya yasir yace ki kwantar da hankalinki kinji inshaa Allah komai zaizo mana cikin sauki,amsa mishi tayi da toh,kwali yabata na wayan daya sayo mata Samsung mekyan gaske,da farko kin karba tayi tace yaya ni kuma wane waya zan rike ku kadai nasani kuma kullum muna tare, yace ai mu din ma wataran bukatan kiran mu zai kama,amma Sam tatsaida gardama har saida yabata rai kafun ta karba yasa mata sim ya daura mata numban shi Dana Ahmad Dana maa Dana maa gana, karba tayi tana murmushi tace nagode sosai yaya,shima murmushin ya maida mata yace ba damuwa.
Khalifa yanagama waya da wa en can mutanen datanshi ya bude nan yaga messages din Yusuf sunkai goma da sauri ya bude jikin shi har rawa yakeyi"kai guy naga fa yarinyan nan gashi wayanka baya tafiya"saiga hoton da Yusuf ya dauketa yashigo daya bude har saida ya razana , pillow shi ya nausa yace damn it,wallahi ita ce, why Nihal? Meyasa saida nabar borno zaki bayyana? voice din ya bude "guy nafa ganta da wani yaron shuwa kuma naji kamar ana cewa mijinta ne…tashi yai yayi wurgi da wayan yana cewa noo wallahi bazaiyu ba ni khalifa nine mijin Nihal ba zan bari ta auri kowa ba ina Raye bazaiyu ba,nan yayita sambatu daga karshen yaje yasakewa kanshi ruwa…..
Tsugune yake a tsakiya sauran sun zagayeshi babban su kuma yanakan kujera a zaune,duk sun zagaye idon su da farin Abu sun kuma yafa bakin mayafi,shi kadai ne baiyi wannan shigan ba, ogan sune yataso ya zo kanshi yana hararan shi,sannan yace khalifa meyasa kakeson yiwa kungiya taurin kai? Kuma me kake nufi da kanason kabar kungiya bayan kasan hakan ba maiyuwa bane?dago idon shi yayi Wanda babu tsoro ko kadan acikin ta yace nagama bayani master,kuma dama ni ban shigo don na zauna har abada ba,wani rikitacciya dariya yakwashe dashi yanayi yana nuna khalifa da yatsa har yaje ya zauna,sannan ya bata fuska yace khalifa duk yadda nakeson nuna maka ilan barin ka kungiyan nan ka kasa ganewa..babu abunda zamu kara ma cema kaje ka gwada mugani, mu ko kai,tashi katafi!! Da wani irin murya me firgici yayi maganan sai da khalifa ya firgita…
Fita yayi yashiga motanshi ya wuce gida…dakin shi ya bude ya Shiga ya maida kofan ya rufe yajingi na da kofan…take ya rushe da kuka me cin zuciya ya sulale ya zauna a wajen,kuka yake yana kiran mamin shi,Mami na meyasa kika tafi kibarni a lokacin danake bukatan ki?nasan da kina nan ke kadai zaki iya sharemin hawaye na….babu Wanda zai fahimce ni a irin wannan lokacin saike kadai…kuka yayi sosai kamar ranshi zai fita,sannan yaje dauro alwala yafara jera salloli shine bai kwanta ba har saida yayi sallah asuba yayi azkar kafun ya kwanta…
Yauma kamar kullum da zai fita saida ya duba ta yabata maganin ta tukunna,Ahmad ma yashiga dubata yasamu tana bacci har yajuya zai tafi tace ya Ahmad zaka tafi makaranta ne,juyowa yayi yaganta Ashe idonta biyu kawai tana kwance ne,yace eh amma karatu ma zanje inyi,da zance miki ki shirya muje ne amma kuma sainaga kamar kina bacci da sauri ta tashi tace, Allah zamuje tare? Kai ya daga mata,da murnanta ta sauko tana cewa to kabani minti biyar bari na watsa ruwa,yace toh, sannan yakoma dakin shi,itama sharp sharp tayi wanka kafun tasha tea a tsatstsaye,fitowa tayi taje dakin maa tagaya mata zata raka ya Ahmad sosai maa taji dadin maganan, harta fito parlor ta tuno tabar wayanta a daki,zuwa tayi tadauko saida tazauna kafun ta nemo number ya yasir takirashi,ringing biyu yadauka ,sallama tayi ya amsa,yace harkin tashi daga baccin? kai ta daga kamar yana kallon ta kafun tace eh, yace dafatan dai komai lafiya kuma babu inda yake miki ciwo? Tace eh,yaya dama zan raka ya Ahmad karatu ne shine nace bari in gayama,sosai yakejin dadin yadda take girma ma shi,murmushi yayi tare da lumshe idon shi yajingina da kujera…sannan yace badamuwa kudawo lafiya,amma fa ki kula da kanki sosai inhar kikaga abunda zai Tayar miki da hankali kigayawa Ahmad yadawo dake gida kinji,tace toh yaya,sannan suka kashe wayan.
*Abdlzty💞*