💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙17
Yusuf ne da khalifa suke zaune a garden din gidan khalifa ne ya rage sautin karatun da yakeji yace abokina yakamata fa mufara zuwa inda kaga Nihal don wallahi kullum daurewa kawai nakeyi..murmushi Yusuf yayi yace badamuwa aima naga kokarin ka,gobe in Allah yakaimu saimu fita ko,yace toh Allah ya kaimu.
Yasir badon yaso ba saidon kawai irin nacin maagana da yaranta yasa yabarsu suka tafi da Nihal, koda tagayawa Ahmad shima baiso ba duk da baya gidan haka yayita mita dakyar ta lallabashi,amma yace mata gaskiya duk randa zaidawo dole tadawo,murmushi tayi tace duk yadda kace haka za'ayi yaya na.
Ya yasir ma duk yadda chat bai dame shi ba amma tafiyan Nihal gidan maagana saida yasashi ya koya saboda bayason kullum ace Sai yaje gidan,saidai shi chat dinshi baya wuce “Angel kintashi lafiya?, hope kinsha maganin ki?,dafatan dai maagana tana kula dake? Da rana kuma “Angel kinci lunch kinsan banson fa kina wasa da abinci kinji, kina kulamin da kanki…haka da dare ma…kuma zai kira maagana ma yaji ya take,maagana harta fara mishi mita wai meyasa yake tunani kamar bazata kula da ita bane…bayan yadda suke jinta tamkar er uwarsu haka itama takeji..saidai yayita bata hakuri, dama tun tana gida ma haka suke, maagana Allah ya diga mata mita shikuma yasir bai iya expressing kanshi ba lokuta da dama Sai maa tashiga maganan su ta tsawatar mata.
Gobe Ahmad zai gama exams don haka tunda safe yadamu Nihal Sam tasan yadda zatayi tadawo gida,don gaskiya bazaiyu yadawo gida bata nan ba ita kuma tace mishi tanajin kunyan kar maagana taga kamar tagaji ne,yace toh shikenan tunda kunya takeji shi zai fada mata,da sauri tace a ah kabari zangaya mata…tana kashe wayan taje tasamu maagana, tana ganin ta tafara murmushi tace ai nadauka bacci kikeyi shiyasa na hana yaran nan zuwa saboda karsu dameki…murmushi tai tace a ah idona biyu,Sai da tasamu waje tazauna tayi shuru,maagana tana nazarinta don ta lura kamar akwai abunda takeson fada,amma bata cemata komai ba.
Dakyar nihal ta danne ranta tace maman sayid,dama inason inje gidane in duba maa kwana biyu banganta ba…mumushi maagana tai tace badamuwa Sai anjima idan direba yadawo yakai ki,amma fa yau zaki dawo?Murmushi kawai Nihal tai batace komai ba….
Bayan azahar kuwa Ahmad bai yadda Nihal zata iya fada ba Sai gashi yakira,tana dauka tace su uncle Ahmad sai yau aka tuno damu ne dariya yayi yace ai gwara ni nakira ki amma ke ko exams wishes baki turomin ba,baki takama tace lallai wannan shine inbaka iya kama barawo ba sai ya kamaka…tace toh uncle kanadi gone (kayi hakuri) ka yafewa ur only sister, tabe baki yai yace ai dama ke kinsan yadda zaki lallaba mutun idan kin mishi abu dariya sukai duka,sannan yace yauwa ba wannan bane yasa nakira ba fa,kinga har zakisa in manta dalilin kirana,tace toh inajinka,Allah yasa dai bawani laifin nai ba..murmushi yayi yace nine dai zan nemi alfarmanki kiyi hakuri ki kyale mana Fulani tadawo gida kinga gobe zangama exams…
umhum,ba sai kazo ku gaisa ba…da sauri yace a’ah karki mana haka gidan baya dadi idan bata nan,ai kin danata ai sai kuma tadawo, dariya tai tace uncle nifa bangane ba I’m sensing something…dariya yayi yace kinason kiyi gulma dai,nidai ba komai barima kiji…dariya tayita yi har ya kashe.
Tstayawa tai tana tunani, kaddai uncle yasir da uncle Ahmad dukansu suke son Nihal? Idan kuma hakane halamu ya nuna tafison Ahmad saboda ta tabbata donshi takeson zuwa gida,meyasa for ol diz while bataji tanason ganin ya yasir ba sai shi?kodon shi yana zuwa may b shiyasa.. Tace amma fa mu gsky ma uncle yasir muka kamawa,uncle Ahmad hakuri zakayi ehen! Haka tayita magana ita daya.
Kafun yamma Nihal tashirya kayanta tsaf jiran tafiya kawai takeyi,yamma nayi aka kaita gida itama sai farin ciki takeyi…Yau Ahmad yagama exams duk Sai sauri yake tayi bena ce ta kalleshi tace saurin me kakeyi haka kamar gidan zai gudu.. Kallon ta yai yace bazaki gane bane nayi missing din gidane sosai.. Murmushi tai tace toh gashi ni kuma banason ka tafi don nasan zanyi missing dinka..tsayawa yai yace kinsan meza ai yanzu kafun akawomin motana muje muci abinci ko? Sosai taji dadin hakan.
Khalifa da Yusuf kuma yau sunce unimaid zasuje suci abinci,saboda suna raba kafa wajen Neman Nihal duk inda sukasan mutane na taruwa can suke zuwa….direct restaurant din dasu Ahmad sukaje suma can suka nufa…
Ahmad har sunyi order ankawo musu sunfara ci…lokacin kuma su Yusuf suka shigo,suma waje suka samu suka zauna opposite din su Ahmad,har sun zauna sunyi order kenan,sai Yusuf ya hango Ahmad, tsayawa yayi cak! Khalifa ne yace mishi kai lfy wa kake kallo haka?.
Shiko Ahmad lokacin yasa waya a kunnen shi yana saukewa yace mata muje ko? Ankawo min motan,tace toh shikenan, nikam zan koma hostel injira su xulaifa,kacewa Fulani inzanzo zan kirata yace toh shikenan.
Kafun Yusuf ya Ankara gani yai suna kokarin fita,da sauri yacewa khalifa,shine Wanda ranan naganshi da Nihal katashi mubisu arude khalifa yatashi suka rufawa Ahmad, suna fitowa shikuma yana shiga mota har ya tada ita ,suma motan su suka shiga suka bishi a Dari…khalifa jikin shi har rawa yakeyi,don ji yake kamar ya fita a motan ya bishi da kafa…suna isowa wani traffic Ahmad na wucewa aka tsaidasu…
Take idon khalifa ya canja kala sai girgiza kai yakeyi,tun suna hango shi har yasha kwana,tsaki sukaja a tare,ana sakesu suka eba a Dari sukai kwanan da yayi saidai ko walkiyan shi basu gani ba.
Khalifa dunkule hannu shi yai ya rufe ido,jikin shi duka rawa yakeyi,parking Yusuf yai shima duk Sai yaji ba dadi… a hankali yace kayi hakuri khalifa inshaa Allah zamu sake haduwa dashi kaga yanzu munga wajen zuwa shi guda biyu…
Khalifa bai iya cewa komai ba haka Yusuf ya juya dasu gida,abincin da basuci ba kenan.
Tunda suka koma gida khalifa yakara shiga rudu sosai, wai ace suga Wanda Nihal take hannun shi amma yabace musu,meyake shirin faruwa ne…..har dare yana cikin wannan tashin hankalin Yusuf yabashi baki har ya gaji.*Abdlzty💞*