💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙26
Suna isa aka wuce dashi emergency take aka sa mishi oxygen, Yusuf ne yayi saurin kiran daddy khalifa yasanar dashi halin da ake ciki,hankalin daddy bakaramin tashi yai ba take yasa aka mishi booking flight yakamo hanya.
Ahmad ne ya bude kofan dakinta samun ta yayi a zaune ta hada kai da gwiwa tana kuka mecin rai, shima zama yayi kukan ta yana taba mishi zuciya sunkai minti talatin a haka kafun yace Nihal kina kukane saboda Abba yace bazaki auri khalifa ba? Shuru tai bata ce komai ba kuma bata daina kuka ba,
Numfashi yasauke yace bakya tunanin akwai dalilin dayasa Abba fadan hakan? Amma karki damu mu ako yaushe farin cikin ki mukeso kuma baza muso abunda zai cutar dake ba,zanje intambayi Abba dalilin shi idan har bamai karfi bane zan tayaki rokon shi ya janye furuncin shi yabarki ki aure shi… hannu ta tadaura akan hannu shi cikin muryan ta daya fara dishewa,tace a ah yaya ni bawai ina jayayya akan furuncin Abba bane,wlh na hakura da khalifa har cikin raina tunda iyayena basaso,kawai ina tausayin halin dazai shigane dalili na,khalifa yanasona so mai tsanani,wannan maganan bakaramin sukan Ahmad yayi ba…amma haka ya danne ranshi yayita rarrashin ta.
Daddyn shi ya iso ba bata lokaci Yusuf yabashi labarin duk abunda yake faruwa tundaga farko har karshe kuma bai boye mishi komai ba…daddy yayi kuka sosai kuma duk kanshi yayi blaming, yace yakasa rike amana mamin khalifa,rashin kulawan shi duk shi yajefa khalifa cikin wannan halin,wajen likitan yawuce donjin meyake damunshi yanzu,ya sheda mishi zuciyan shi ne ta buga,take yaji tashin hankali shi ya ninku,a lokacin yafara processing fita dashi waje don samun kyakkyawan kulawa.
Tunda suka koma Ammie tafara rokon Abba akan yajanye maganan dayayi kodon Nihal ma,cewa yayi takyale Nihal yarinya ce bazata gane meyake faruwa ba amma nan gaba zata gane gata Yamata kuma shi ya gama magana bazai janye ba, ran Ammie yabaci tace gaskiya tafara gajiya da halin shi na kafiya, in yafadi abu kamar wahayi wai bazai canja ba,nan tafara irgo mishi kokarin da khalifa yayi wajen ganin ansamu Nihal, duk da ya jinjina wa kokarinshi amma fa azahiri nunawa yayi to wayasa shi da yabari ai yaga ko bazata fito ba, rikici sosai ya barke tsakanin Ammie da Abba,yace tashirya washegari Monday su tafi saboda aikin shi amma fir tace itakam yaje bayan sati biyun zai dawo yasameta,har saida ya hadata da baffah yagaya mishi abunda yake faruwa,sosai baffah ya mata fada yace mata kuma shima yana bayan Abba saboda yafita gaskiya, badon taso ba saidon biyayya tabishi suka tafi.
Daddy khalifa ne yakira Abba yace idan yana free zaizo yasa meshi akwai maganan da yakeson suyi,Abba yace mishi badamuwa, address din shi ya tura mishi,baifi awa daya ba saigashi,isowa yai suka gaisa a mutunce daddy bai bata lokaci ba yafara Neman afuwa on behalf of his son,baya yabo ba fallasa Abba ya saurare shi saida yagama, yace gaskiya naji dadi da har yanzu kuke Neman hada zuri'a dani,don duk Wanda yaso naka kai yaso,amma saidai kayi hakuri Alhaji na riga nayiwa Nihal miji kuma bazan iya janyewa ba,tun farko khalifa shiyafara bata komai amma duk da haka bazan zargeshi don na tabbata haka Allah ya tsara watakila ba matar shi bace shiyasa,kuma ina mishi addu’an samun wacce tafi Nihal.
Sosai jikin daddy yayi sanyi baiso haka ba amma babu yadda ya iya saboda shima in shine hakan zaiyi,haka ya tashi jiki ba kwari sukayi sallama ya tafi.
Yagama tsara komai wani sati za'a kai khalifa asibitin madina don har yau baisan ina yake ba.
Su Ammie har sati biyu ya cika sun dawo jajere ya kuma kira yasir yashaida mishi sun dawo. Yagayawa maa gobe zai kai Nihal, maa tace ai da ita za'aje Ahmad ma yace shima zaije don haka dukan su suka tafi.
A mota ne maa take cewa Nihal 'Fulani idan munje zan roki Abban ki da Ammie alfarma subarmin ke har zuwa lokacin auren ki,Ahmad ne yayi saurin cewa aikuwa maa dakin kyauta mana,yasir kuma yace maa sumafa sonason ganinta a kusa dasu more especially ma Ammie ta,da sauri ta tura baki tace nidai tare da maa zan dawo,yauwa yarinya na Allah dai ya miki albarka, kai kuma aidama yanzu kam dole na inbarta ta kwana biyu dasu,sati nawa zakiyi Fulani? Nihal tace daya, a'ah daya kam yayi kadan kiyi dai at least wata daya da sauri Ahmad yace gaskiya maa yayi yawa,juyowa tayi tace toh sati biyu ko yaya na tana kallon Ahmad, yauwa dama dama,haka sukai ta tadi har suka isa.
A gidan baffa suka sauka,nan akaci abinci da hira kafun suka zauna.
Sosai Abba ya musu godiya, maa ce tagyara zama tace tana Neman alfarma guda biyu a wajen su,baffah ne yace ai yanzu sun zamo en uwa kuma tsakanin su yawuce alfarma tafadi komeye kanta tsaye,don ya tabbata samun mutune irinsu yanzu zaiyi wahala.
Sosai taji dadin karramawan dasuka mata,murmushi tai tace Alhamdulillah… abu nafarko dai shine duk da mace bata zuwa Neman aure amma ni inason innemawa yasir dina auren Nihal kafun iyaye maza su shigo ciki.
Yasir ne ya kafe maa da kallon mamaki don bai taba tunanin alfarman da zata nema ba kenan,take Abba dasu baffah har da Ammie sukaji wani farin ciki ya ziyar cesu,dama Abba addu’an shi kenan don tun randa idon shi yasauka akan yasir yaji kwadayin hada zuri’a dashi saboda mutuncin shi da cikar kamalan shi.
Ahmad ma abun ya mishi dadi sai yaji kamar shi aka bawa… Nihal kam take taji ta gigice zuciyan ta na bugawa da sauri da sauri saboda kar kowa yagane halin data shiga sai kawai ta sunkuyar da kanta.
Nan da nan farin ciki ya gwaraye falon kowa sai Mashaa Allah yake cewa…
Saida aka nutsu sannan Abba yace Alhamdulillah yafi kowa farin ciki da wannan lamarin kuma na abunda zai cewa maa saidai Allah yasaka mata da aljanna don dai shikam tagama mishi komai,baffah ma godiya yayi mata sosai da nuna goyon bayan shi, tace inshaa Allah suna komawa dangin baban shi zasuzo.
Sannan tace saura alfarma na biyu da take nema,shuru akai ana jiranjin mezatace, tace nasan kuna bukatan Nihal yanzu sosai amma duk da haka karku gaji dani Dan Allah Kuban Nihal mu zauna har sai biki yakusa indawo da ita.
Murmushi Abba yayi yace ai hajiya karki damu Nihal erki ce kuma duk yadda kukeso haka za'ayi ni kin gamamin komai da kikeson gudan jinina.
Godiya maa yayita yi kamar badama harsai suka cemata ya isa,agogo ta duba tace mu zamu wuce kar dare yayi,amma nan da sati biyu su yasir zasu dawo su dauketa.
Sam su Ammie suka hanasu tafiya akan subari gobe da safe su tafi,ba musu maa tace Allah ya kaimu.
Sum sum Nihal ta tashi tayi side din inna tana zuwa tafada kujera ta rushe da kuka, Ahmad yana hankalce da ita shima tashi yayi ya sulale yabi bayan ta, yana shiga yaganta tana kuka sosai…
Gefenta yaje zauna yayi shuru,tunani yafara kaddai Nihal batason yayan shi ne take kuka haka…
Dama tunda taji kamshin turarenshi tagane shine ya biyota, a hankali yafara magana, Nihal! Kuka kikeyi saboda ance zaki auri ya yasir? Bata bashi ansa ba taci gaba da kukanta, shikenan ni zanje incewa maa tajanye maganan ta don bakyaso,kuma nasan itama bazatayi abunda bakyaso ba, yunkurin tashi yayi tayi saurin rike hannu shi,Dan Allah karkamin haka yaya wlh inason yaya yasir,ni waye da maa dasu Abba na zasu zabamin miji ince banaso,nima bansan kukan da nakeyi ba ka yadda dani yaya… ciki kuka sosai take maganan, shuru yayi yazauna yana sauraron kukan nata harta gaji ta daina.
Da dare yayi haka yasir ma yatsinci kanshi da kasa yin bacci, ya rasa farin ciki ne yakeyi ko bakin ciki?take wata zuciyan tace mishi ta yaya zakayi bakin cikin auren mace kamar Nihal? Wacce samu irinta zaiyi wuya,ai saidai farin ciki,kuma dama samunta yana daya daga cikin burin rayuwan shi Wanda ya jima da bunnewa saboda wasu dalilan shi da yake ganin da kamar da wuya,sai gashi Allah yabashi ita cikin sauki,tashi yayi a hankali yaje jikin window ya tsaya,dama a side din hamma aka saukesu Wanda yake kallon side din inna,hango ta yayi itama ajikin window amma tabaiwa window baya,yana hango shape din yagane itace,tunani shin itama Nihal kasa bacci tayi kamar yadda ya kasa?kodai bata son shine?take wata zuciyan tace mishi kai da ka kasa bacci ne saboda baka sonta,a fili yace a'ah….murmushi kawai yayi ya koma ya kwanta.
Washegari bayan sun karya suka kama hanya,duka gidan suka rakosu jikin mota,ita dai ta kasa samun sukuni don yanzu duk kunyan mutanen wajen takeji, saida suka shiga mota dagan kan da zatayi suka hada ido da Ahmad gira daya ya daga mata yace yau ba magana ne anty,yana nuna mata yasir da hannu,gyalen ta taja da sauri ta rufe fuskanta, dukan shi yasir yayi a kafada don yana hango abunda yakeyi ta mirror,awnn shikenan tunda kana rama mata…duka dariya akasa suka musu Allah ya tsare,saida yabari su baffah sunyi nisa sannan yace angel! A hankali don baimayi tunanin zataji ba amma sai yaga tatsaya cak,juyowa tai tana kallon shi shidin ma ita yake kallo,a hankali ta ta ko zuwa jikin motan, take care! Kawai yace mata, kai ta daga mishi halamun tam sannan ya tada motan…tana kallon su har saida motan ya bacewa ganin ta sannan ta koma gida,maa tana ganin duk abunda sukeyi amma tayi kamar bata gansu ba.
Suna komawa Abba yace maza su tattara suma su kama hanya,Nihal kam cewa tayi ita abarta a gidan baffah, inna ne tace babu wani gidan baffah daza abarki ja'ira duk kibi kicikamin daki to bazaiyu ba maza ki shirya kibi iyayenki, kukan sakalci tabarke dashi baffah ne ya rarrashe ta..har su Ammie sukagama tana nan tana sakalci,Ammie ce tace zamu tafi tare ne ko kina nan mukama hanyan mu,baffah ne yace a'ah ku bata minti biyar yanzu zata fito maza tashi boddo na.
Dama tayi wanka akwatin ta kawai ta dauko.
Tunda akace anbashi Nihal yaji wani irin sonta yana ratsa jinin shi, jiyake kamar bazai iya jira zuwa sati biyu ya dauko ta ba, maa tasanarwa dangin babansu bayan sun dawo da kwana uku sukaje mishi formal tambaya kamar yadda al'ada ta tsara, a take kuma aka gama komai don baffah yace babu wani Jan lokaci don haka nanda wata biyu aka tsaida date.
Ahmad kuma Hutu yakare yanzu harsun fara house manship dinsu.
Yau ne ranan daza'a dauko Nihal Ahmad da yasir ne sukaje kuma har abuja sukaje wannan karon,itama tayi kewansu ba kadan ba.
Tunda suka dawo rayuwa ta canja don Ahmad yadaina shigewa Nihal kamar da yanzu kam ma sai tsokanan ta daya tsiriyi,yasir kuma yanzu soyayya ne da kulawa na musamman yafara mata,amma duk da haka kullum inzai fita sai yabaiwa Ahmad amanan kula da ita kamar kullum.
Tun tanajin nauyin maa itama harata sake yanzu, sosai takejin soyayyan ya yasir acikin zuciyan ta,ita take kula da abinci shi yanzu.
A kwana a tashi yau saura sati biyu bikin Nihal da yasir kuma ranan ne suka maidata jajere, su Ammie ma duk sun dawo gida saboda a jajere za’ayi bikin kafun a dauketa a kaita maid, duk wani gyaran jikin da uwa takewa erta lokacin babu Wanda maa batayiwa Nihal ba.
*#yasirnihal💞**Abdlzty💞*