💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙29 & 30
Ita dai maa duk addu’an ta sudawo kawai don yanzu ganin takeyi gwarashi akan Nihal din.
Da ikon Allah dai gobe zasu dawo, Nihal kam tana gadon asibiti batada aiki daga shan drip sai bacci,duk ta lalace tayi fari fat kamar ba jini a jikinta,ta rame sosai, ya yasir kam shi aka harba amma Nihal ita tayi jinya.
Dukansu sukaje taryo shi a airport akabarta da nurses, jirgin su na sauka yafara raba idanu ta ina zaiga en gidan su,yaran maagana ne sukazo da gudu suka rungumeshi ba tare da ya lura ba sai lokacin ya hango en gidansu da sauri ya karisa kowa na farin cikin ganin shi…saida aka gama mishi oyoyo sannan yace maagana ina kuka kaimin matata?murmusawa tai ta nuna mishi Ammie da ido,kunya ne yaji ya lullubeshi take yahau kame kame,maa ne ta rankwashi kanshi tace ai sai mun baka wahala kamar yadda kabamu.
Yanason sannin inda take amma yanajin kunyan tambaya,dayaga halamun fa basuda niyyan gaya mishi cire kunyan yayi yace Ahmad ina amanan Dana barma ? Shima rarraba ido yafarayi don ji yake kamar yakasa rike amana yayan shi,Sosa keya yayi yace yanzu dai yaya muje kaci abinci ka huta ko,hannu shi ya fizge yace babu inda zanje nidai kawai ku gayamin ina take,take yaji zuciyan shi na bugawa kaddai wani abune yasamu Nihal dinshi,maa ne tadafa shi tace baba na ka kwantar da hankalinka batada lafiya ne tana asibiti amma na tabbata yaukam ciwonta yakare don dama Kaine kajawo ciwon.
Cikin kaduwa yace maa bazanje gida ba ku kaini asibitin naganta, take suka dunguma sai asibiti.
Kamar kullum yauma tana bacci amma daga kaganta zakasan baccin wahala takeyi.
Duk fita sukayi sukabarshi a dakin,zama yayi a gefenta yana kallon kalan Raman datayi kamar wacce tayi shekara ba lafiya, tausayin ta yaji ya cika mishi zuciya, hannu yakai a hankali ya shafa gefen fuskanta hannu ta takai wajen don tadau wani abun,Sai taji hannu,a hankali ta bude idon ta dishi dishi take kallon shi saita dauka imagination takeyi, Mirza idonta tayi saita ganshi Ras,yana mata murmushi saidai shima ya rame sosai.
Yunkurin tashi tayi amma takasa,saida ya temaka mata ta tashi,kallon shi take kamar yau tafara ganin shi,sai kawai tafashe da kuka da sauri ya rungumeta,itama shiga cikin jikin shi tayi tana kuka sosai,a kunne ta yace mata I’m sorry baby,duk saboda ni kike wahala haka.... Bazan sake nisa dake ba,ko mutuwa ma tare zamuyi kinji,maganan shi dariya yabata ,don haka tafara dariya kuma hawaye na zuba a idonta,hannu yasa yana share mata hawayen, banason ganin hawaye a kyakkyawan fuskan nan yana tabamin zuciya, kuma kinga yanzu zuciyan tawa akwala ce yakarishe maganan tare da daga mata gira,da sauri takai hannu ta kirjin shi,tace yaya na hope kawarke..cije baki yayi yace ban warke ba bayan kin tada hankali shine kawai Abba yadawo miki dani haka,kwantar da kanta tayi akan kirjin shi tace yaya bazan iya rayuwa babu kai ba kazamo wani bangare na jiki na,kaine HASKEN RAYUWA TAH,ajiyan zuciya yayi tare da shafa kanta yace nima haka,amma fa dole za'a canja min suna banson yayan nan,dagowa tayi tana kallon shi,gefe ya kalla tare da tamke giran shi,tace to me kakeson incema? Da sanyi murya tayi maganan, yace aike zaki nemo,kuma yanzu nan nakesonji, shuru tayi tana tunani sannan tace Nuru Hayaty…lumshe ido yayi yace so sweet…saidai.. Tace saidai meye? Yayi tsayi yana mata murmushi, tace umhh mi Amor! Yauwa sweetheart tare da kankameta kamar wani zai kwace mishi ita.
Ammie da Abba sun tattara sun koma,yanzu maa jinyan su duka biyu takeyi,amma yasir ya fita warwarewa,dagewa yayi akan dole sukoma side dinsu , fir maa taki tace Shiya koma inya matsu,amma erta kam sai ta warware kuma tashirya ta.
Bayan sati biyu yau nihal suka koma side dinsu,saidai tana shiga tsoro da fargaba ne suka kamata dakyar yasir ya lallabata tazauna amma da tace Sam saidai takoma wajen maa,saidai duk da haka bata iya bacci ba,dakyar tadan sake da gidan.
Yasir da Nihal rayuwa me tsafta tare da soyayya da tausayin juna sukeyi,babu me yadda Dan uwan shi yayi nisa dashi kona kwana dayane, hankalin maa sosai yakwanta, Ahmad kuma yakammala house manship dinshi yazamo cikakken likita,kuma sun daidaita benazir don ya lura bazai taba samun meson shi tsakanin da Allah kamar ta ba.
