💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
Kuyi hakuri zakuga page din nan kadan...busy nane yai yawa amma daga yau inshaa Allah na zauna komai zai daidai ta..luv u ol💖
📙19
Yau kam tasamu ta hau lilo tayi wassani dayawa…ba karamin jin dadin wajen tai ba,dakyar Ahmad yajata suka tafi.
Yau khalifa ya shirya zuwa gaishe da Ammie,yayi yayi Yusuf ya karashi yaqi,haka Yakama hanyar damaturu shi kadai, yana isa direct anguwan su Ammie yawuce,shima ya rasa meyasa ya kagu dayaje ya ganta,yana zuwa kofan gidan yaji zuciyar shi tana tsinkewa haka ya daure ya kwankwansa kofan saida yai sau biyu kafun akazo aka bude, wata kanwar Ammie ce ta bude,tana ganin shine tabata rai ta hada giran sama Dana kasa tace malam lafiya?Kodai yauma kazo ka sauke mana kwandon rashin mutunci ne?to wallahi ka gaggauta Barin kofan gidan nan kafun Abban Nihal yazo yasa meka,tana isa nan ta turo kofan zata rufe,da sauri yasa hannu ya rike yace Dan Allah umma Amina kiyi hakuri, Ammie nazo gaisarwa,kallon mamaki ta tsaya tana mishi sannan tace ka gaisheta kace mata uwar meye?ko kuma kazo ka karisata ne…cikin masifa da daga murya take maganan, da karfi ta tura kofan ta rufe..ciki ta koma tana huci,Ammie dake kwance ansa mata drip a hannu a hankali ta juyo tace Amina ke kuma dawaye haka naji kina masifa?
Juya fuska tai tace banda dan rainin hankali nan kome yazo tagaya miki oho,wallahi na tsani yaron nan kamar yadda natsani mutuwa.Ammie ce ta juyo da kyau tace nikam banson hauka gayamin waye shi? Banda khalifa mana zuciyan Ammie ne ya buga dum,tambayan ta tai karfe nawa yanzu? Tace karfe shadaya ne, maza je ki duba inbai tafi ba kice mishi yashigo…
sake baki tai tana kallon yayarta da mamaki…Ammie batasan lokacin data daka mata tsawa ba “wai bazakije bane harsai yafi” kamar ba ita bace take magana dakyar ba..saida umma Amina ta tsorita tashi tai taje waje aiko a inda tabarshi anan tasameshi yana tsaye,harara ta watsa mishi tace ka shigo,biyota yai, zuciyan shi bakaramin tsikewa yai ba ganin Ammie a kwance da sauri yakarasa kusa da ita yana cewa Ammie meya sameki bakida lfy ne?duk a rude yake jera mata tambayoyin,murmushi tai me kama da kuka,tace banida lfy ne khalifa,meyake damunki Ammie? ajiyan zuciya tai tace ciwon zuciya ne khalifa…amma yanzu da sauki ma shiyasa muka dawo gida…
khalifa baisan ya akai ba kawai hawaye yafara zuba a idon shi,khalifa kuka kuma? Ni yanzu kaga yamin babu wani labari akan Nihal har yanzu? Hawayen idon shi yashare sannan yace akwai Ammie…
abokina yaganta acikin garin borno nan ya labarta mata abunda yafaru Ammie batasan lokacin data mike ba tace ohh Allah na ni Fatima Allah kabayyana mun gudan jinina kafitomin da ita Allah…sai kuka Ammie takasa tare hawayen ta khalifa ma kuka… umma Amina ne tazo ta rungumeta tana cewa kiyi hakuri adda..sai harara take bankama khalifa,tace toh ai saika tafi tunda kazo ka kara daga mata hankali…tashi yai kamar kwai yafashe mishi a ciki har zai bude kofa Ammie tace Dan Allah duk randa kagane wajen da take kazo ka gayamin cikin sheshsheqan kuka tayi maganan…shima kasa bata amsa yayi kada kanshi kawai yayi ya fita,yana fita Amina ta tura baki tace gsky adda baki kyauta ba kinsan yanzu idan Abban Nihal yaji abunda yake faruwa bazaku shirya ba,Kada kanta kawai takeyi idonta a rufe hawaye nabin kumatun ta,leben bakinta ta cije dakyar ta bude idanunta da sukayi jajawur…tace Amina bazaku gane yadda rashin Nihal yake tabamin rai ba,kuma khalifa yayi kuskure amma ya gane kuskuren shi,to meyasa baza'a yafe mishi ba? Dukan mu fa en Adam ne babu Wanda yafi karfin yin kuskure,sannan bari kiji yanzu ko Abban Nihal baya nemanta kamar yadda khalifa yakeyi,kuma ni yagama min komai daya nuna soyayyan shi a irin wannan lokacin, dole inbashi goyon baya Dari bisa Dari..
A kufule Amina tace wlh kome khalifa zaiyi bazan yadda dashi ba don ya nuna mana rashin mutunci kuma wlh ni babu ruwana fuu ta tashi tashige daki don talura bazata shirya da addan nata ba.
Ranan khalifa yayi kuka kamar ranshi zai fita…nadama ne sosai aranshi,yanajin duk abunda zai samu Ammie shine sanadi,sannan yanzu yakarajin dole yaqara dagewa wajen nemo Nihal dawuri tun kafun wani Abu yasamu Ammie.*Abdlzty💞*