21 & 22

55 4 3
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ




📙21 & 22



Yau ya yasir yadawo da gajiya sosai dakuma tashin hankali, Nihal duk tana kula da yanayinshi, saida yagama cin abinci ya dauki remote zai kunna TV kenan Nihal tace yaya na yau naganka cikin damuwa,waya tabamin kai? remote din ya ajiye sannan ya shafa kanshi yace wallahi, yanayin aikin ne mu wataran in kaji wani case din duk saikaji damuwa yamaka yawa…
Kallon shi tayi dakyau tace wane irin case ne haka daya saka cikin damuwa? Wani case ne na kisa kuma na lura akwai hatsari sosai acikin shi,don matar da ake tuhuma tayi kisan,jikina naban batada gaskiya,kuma dagani tasan kan dabanci sosai.

Ajiyan zuciya Nihal tayi tace yaya inbaza ka iya ba karka karba kabari sukaiwa wani…murmushi yayi yace karki damu Angel inshaa Allah zanyi iya kokarina bana sa tsoro acikin aikina kullum inason temakawa Wanda aka zalunta,narai narai tayi da ido tace toh yayana Allah ya temaka kuma inshaa Allah zan tayaka da addu’a.. Yace yauwa my beautiful angel nagode itama murmushin tai.


Bayan Abba yagama yiwa baffah bayani ajiyan zuciya yayi don shima tabbas yasan dole ershi zata shiga damuwa sosai,amma kuma dolen shi yabata kwarin gwiwa.


Kallon ta yayi da kyau yace Fatima nasan ki da hakuri sosai kuma nasan kinada addini iya daidain gwargwado Wanda zai iya baki dama yadda da kaddara mekyau ko marar kyau,karki manta auren mace daga daya zuwa hudu Allah ne hallas tawa maza karki zamo daya daga cikin matan da suke haramta hallal,kuma ma banda ke ai abun farin ciki ne ace wacce kika sani mijin zai auro kuma wacce ma kuke shiri sosai, don nasha ganinta a gidan nan kuna zuwa tare tana rakoki,Dan Allah Fatima kisawa ranki salama,kin kwantar da hankalinki ki baiwa mijin ki goyon baya kuma ki dauki abun a matsayin kaddara.

tunda yafara maganan kuka kawai takeyi bata iya cewa komai ba sai daga kanta kawai da takeyi halamun gamsuwa, yace Allah ya miki albarka tashi ki shiga ciki kinji,Abban Nihal binta kawai yakeyi da kallo don ba karamin tausayi take bashi ba,haka inna ma tayi ta mata nasiha.


Abban Nihal yaje gidansu yakai sadaki da kuma kudin Sayan kayan aure yace abata kawai tasayi duk abunda takeso... babu yadda ba'ai dashi ba akan yaje sugana da khairat tunda wani sati ne bikin amma fir yaki, haka suka kyaleshi, matan yayunshi kuwa sai murna sukeyi za'ayiwa Ammie kishiya.


Khairat ma anata bangaren duk hankalin ta ya tashi batasan ta ina zata bulowa lamarin ba gashi kuma anqi bata chance din magana.


Khalifa a tsakanin kwana kin nan bakaramin ramewa yai ba.

Yau Nihal tun safe take damun Ahmad akan yakaita park babu yadda ya iya haka ya shirya suka tafi,saidai yau batabi takan kayan wasanni ba,hira kawai sukeyi,kuma yau kam ma ba mutane dayawa a park din…

motan su khalifa ne ya shigo park din, haka kawai khalifa ya tsinci kanshi da tsinkewar zuciya, zuciyarshi sai bugawa takeyi sunyi parking kenan Yusuf zai fita khalifa ya rike hannun shi yace aboki na wlh zuciya ta na bugawa kamar zata fito,ido Yusuf ya zare yace khalifa karfa kaje kasawa kanka ciwon zuciya akan al'amarin da yake hannun Allah,khalifa baice komai ba ya bude kofan ya fito a hankali, inda yake kallo direct nan ne inda Nihal suke zaune da Ahmad,idon shi dazai daga take yadaura su akan Nihal.. Saiji yayi kamar gizon ne kawai ba ita bace, hannu yasa ya murje idon shi amma still itan yake gani…tafiya kawai yafara yana nufan ta,Yusuf kan ma baisan ya tafi ba don yana Danna waya… bai tsaya ko ina ba sai gaban su,ganin mutun a tsaye a gabanta,yasa tafara kallon shi tundaga yatsun kafa zuciyan ta ne yafara bugawa,a tsorice takai duban ta harkan fuskan shi,a razane ta tashi abubuwan dasuka faru ne suka fara dawo mata…nuna shi take da yatsa bakin ta nasonyin magana amma takasa Ahmad ma tashi yai a firgice yana cewa Nihal meye ne?sulalewa tai ta fadi ta suma a wajen,take dukan su sukai kanta khalifa yana kokarin kai hannu da tsawa Ahmad ya dakatar dashi yace karka kuskura ka tabata,wannan maganan kuma Shiya jawo hankali Yusuf shima a dari ya nufi wajen,khalifa kobi takan Ahmad baiyi ba yakai gannu yana jijjigata yana cewa Nihal Dan Allah ki tashi karki tafi ki barni…

HASKEN RAYUWA TAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora