💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙20
Kawance me karfi ne ya qullu tsakanin Nihal da Benazir saboda takarbi number ta wajen Ahmad.
Yau sukayi benazir zata kawo mata ziyara,harda hada baki wai bazasu gayawa Ahmad ba saidai kawai yaganta su mishi surprise.tunda sukayi breakfast Nihal tafara shiri,ya yasir ya tafi office, Ahmad yanata jiranta a parlor yaji shuru tashi yai ya mata knocking tacee shigo don tasan shine,ya bude kofan tare da sallama,ta amsa tare da juyowa tana murmushi…shima murmushin ya mata,yace sai ina zuwa irin wannan gayen? Tasowa tai daga gaban mirror tace babu inda zanje,kafe ta yayi da ido yana mata kallon anya kuwa? Ido ta bude tace yaya dai? Murmushi yayi yace nidai ban yadda ba..hannu ya bude yace anyway dama inajiran ki kizo muga kings of heart ne,tunda kina busy bari naje wajen modu ,da sauri tace no ya Ahmad don Allah karka fita gani nan fitowa sai muyi kallon ko? Kallon ta kawai yakeyi don ya lura akwai abunda take boye mishi…zuwa yai yazauna a parlon yana jirata…ba afi minti biyar ba ta fito,kallon suka fara kamar kullum amma ya lura yau hankalinta nakan wayanta.
hey bae! gani fa a hanya,sokon da bena ta turo mata kenan a WhatsApp ,murmushi tai sannan ta tura mata smiley me heart a ido tace awnch I can’t wait to c u sis,kuma kinsan har yanzu ya Ahmad baisan kina zuwa ba,nadai kawai rikeshi a gida na hanashi fita…
hahhah gaskiya kin kyautamin sosai.
suna cikin chatting din har tace mata gani fa acikin gidan..toh gani fitowa, tashi tai Ahmad yabita da kallo kamar bazaice komai ba sai kuma yace Nihal! Juyowa tai tare da tsayawa cak,yace ina zaki?murmushi tai tace 1 minute yanzu zan dawo,hmm.. Allah yasa bawani abun kike boyemin ba,huh bana boyema komai kawai dai yau I’ve a surprise for u…bata jira mezaice ba ta fita dasauri, tabe baki kawai yai.
Tana isa jikin motan daya kawo bena, bena na fitowa hugging din juna sukai suna farin ciki sosai, bena ce ta leka motan daya kawota tace zaka iya tafiya gida sai bayan la'asar kadawo,da sauri Nihal ta leka tace karka dawo zamu maida ita kawai…murmushi bena tai tace shikenan, jerawa sukai suna tafiya,Nihal tace gaskiya naji dadin zuwan ki,kuma kinga yadda kika wani kara kyau da halamu hutun nan ya karbeki, dariya bena tai tace banson zuga fa,a daidai nan suka iso bakin parlor, Ahmad ne ya juyo murya kamar na bena,juyawan dazai kuwa sai sukai hada ido, kallon mamaki yabisu dashi,Nihal ce tace ya Ahmad diz is my surprise and U’ve to pay for it(kuma zaka biyani surprise din nan) murmushi yai yace yeah gaskiya kinci kyauta, wani dadi bena taji har cikin ranta don batayi tunanin zatazo gidan su Ahmad ya karbeta haka ba,hanya ya nuna mata da hannun shi yace,tafaddal(ki iso) shigowa tai ta zauna a daya daga cikin kujerun parlon, nan da nan Nihal ta cika mata gaban ta da kayan ciye ciye kala kala…sannan tace mata bari nayiwa maa magana tazo kugaisa,samunta tai tana karatun Qur’an don haka saida tabari takai aya sannan tace Fulani kina bukatan wani abu ne? Tace a’ah dama kawata ce course mate din ya Ahmad kuma surkar ki tazo shine nace bari nagaya miki karishe maganan tayi tana noke dariya…maa tace toh kice yau muna da manyan baki,dariya tai tace sosai ma maa,to bari nagama fejin nan gani nan zuwa,data fito dakinta tawuce takira ya yasir,yana ganin col dinta yai picking tare da cewa hope dai angel dina ba anguwa zata ba? Murmushi tayi kafun tace a ah,yaya dai ingayama yau budurwan ya Ahmad tazo shine nace bari ingayama karta tafi Baku gaisa ba…baki ya bude yace ahh ai dolena indawo da wuri kafun ta tafi,yanzu karki bari ta tafi kijata da tadi Takai har 3 kafun nan nadawo..tam yaya zama kadawo ka sameta yanzu tazo ,yace yauwa saina dawo.
Nihal tana shiga dakin maa shuru ne yadan gifta tsakanin bena da Ahmad, kafun Ahmad yace baby shine zaku hademin baki ko,murmushi tai tace nifa kaganni wajen Fulani nazo ba wajenka ba,dariya yai yace koma dai yaya ne ni naji dadin zuwan ki,tace hmm… ai namayar ba zakaji dadi ba tunda ko zuwa gidan mu bakasonyi,zaiyi magana kenan saiga Nihal ta fito daga dakinta,dawowa tai tazauna nan sukaita tadi har maa ta fito suka gaisa,sosai bena ta burgeta don da gani yarinyan tana da tarbiya.
