💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙10
Yau kwanan khalifa biyu a maid,suna Neman Nihal amma a boye saboda bayason mutane Susan yana nemanta, suna zaune da Yusuf a Zuma hotel wajen shakatawa,sai ga wayan daddy shi,daga ido yayi ya kalli Yusuf, Yusuf yace waye ne? Daddy ne…to ka dauka mana,mezan ce mishi inna dauka,kawai kace mishi ka kawomin ziyara ne,Dan karamin tsuka yayi sannan yace bazaka gane ba,har wayan takusa yankewa yadauka da sauri ya dauka yace,hello daddy! Kana inane khalifa? Daddy ina Maiduguri gidansu khalifa ,Dana naso ingayama…saurin katseshi yayi kaso kagayamin sai akayi yaya?eh? Ni khalifa me kakeson kadawo ne? Kodai akwai munafurcin dakake boyewane ban sani ba? Tayaya zakabar aikin ka kacemin ka kai ziyara ba Hutu ka dauka ba, ba komai ba?kodon kana gadara da company naku ne? To wallahi bari kaji ni babu ruwana kuma na basu izini inkayi misbehaving su hukunta ka,kamar kowa….don haka maza ka tattaro ka kadawo kagaya musu ina ka shiga kwana biyu.
Kayi hakuri daddy inshaa Allah gobe zan dawo…bai saurare shi ba yakashe wayan “ baban khalifa Yanada tsanani sosai amma tunda maman khalifa ta rasu lallaba shi yakeyi,kuma duk abunda khalifa yayi yana bashi hakuri shikenan sai duk jikin shi yayi sanyi,shiyasa tunda yafara hukunta shi akan abunda yayiwa iyayen Nihal baya bashi daman da zaibashi hakuri, ko yanzu ma dagangan yakashe saboda inzai sake magana khalifa zai gane ya huce” kallon Yusuf yayi yace anya bazanyi resigning aikin nan ba?ido Yusuf ya zare yace kai! Ta yaya zakabar aiki bayan yanzu daddy na fushi dakai,nifa inaga akan rashin hankalin da kayiwa iyayen Nihal ne daddy yakeson hora ka,kafada ya daga yace is possible, nidai yanzu shawaran dazan baka shine kayi kokari ka nuna mishi kayi nadama sannan duk abunda yakeso zakayi, inaga wannan ne kadai zaisa idan kasamo Nihal yakara shigema gaba wajen Neman ta,kada kanshi yayi yace hakane,yanzu gobe sai in koma kenan? Yusuf yace eh hakan za'ayi…shuru yayi yana tunanin gaskiya wannan aikin zai hanashi yin abunda yakesonyi.
Washegari yasir yagama shiri zai fita, dakin Ahmad yashiga yasame shi yana karatu,bakin gado yasamu ya zauna yace bakai bacci ba,murmushi yayi yace inaga ta baccin safe,ina kwana yaya? Lafiya Ahmad,katashi lafiya? Lafiya Kalau…dama zan fita ne nace bari in duba ka...Dan Allah Ahmad inason kana kula da Fulani kamar yadda nakeyi,kana sakewa da ita ka dauketa tamkar maagana, kaga yanzu bata da en uwan da suka fimu,kai ya daga halamun gamsuwa yace inshaa Allah yaya zanyi yadda kakeso, murmushi yayi yadafa kafadan shi yace yauwa Dan qanina Allah yayi albarka,Amin yace yana murmushi…nizan fita zan dubata kaima inason idan zaka fita kabi ka duba ya ta tashi,yace toh.
Yana fita dakin ta yayi knocking tace shigo, murdawa yayi tare da yin sallama,ta amsa,samunta yayi kamar jiya akan abun sallah da Qur’ani… tunani yafarayi wannan yana nufin bata manta daily activities dinta ba kenan,ita ta katse mishi tunani da cewa, ina kwana yaya?amsawa yayi cikin fara'a ,zama yayi yana duba agogo yace,zan wuce wajen aiki dafatan dai babu wata Matsala? Kanta a sunkunye tana wasa da en yatsunta tace babu,har zai fita tace ya yasir yaushe zaka kaini inga gari?juyowa yayi sannan yace ki shirya yau idan nadawo sai mufita,dadi taji Wanda harsai da ya bayyana a fuskanta tace toh shikenan Allah yadawo dakai lafiya Amin yace yana fita…dakin maa yaje suka gaisa ya fita a gaggauce saboda yafarayin latti, Ahmad ma saida yagama shirin shi zai fita harya manta, sai ya tuno da Fulani kofan dakin ta ya nufa sa hannu shi yayi kamar zaiyi knocking sai kuma yafasa kome yake tunani oho,sai kuma yakara maida hannu shi yai knocking ita kuma fitowan ta daga wanka kenan, hijabinta tayi saurin dauka tasa, sannan tace shigo,sallama yayi,baki bude ta amsa tana mamakin yau wannan ne a dakinta? Ganin ta kafe shi da ido sai yayi gyaran murya firgigit tayi har saida taji Dan kunya,tace ina kwana? Amsawa yayi fuskan shi a sake…yace zan wuce makaranta ne sai kuma yayi shuru,tace Allah yabada sa'a, yace hope babu wani damuwa? Tace mishi eh,har ya juya tace ya Ahmad! Juyowa yayi ba tare da ya amsa ba,tace yau zamu fita da ya yasir zakadawo dawuri ne sai muje tare? Kada kai yayi yace badamuwa inna dawo zamuje da murmushi a fuskan shi da halamu yaji dadin tayin ,itama murmushin tayi...
