HASKEN RAYUWA TAH 9

57 4 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ



Nifa a kaf masoyana banida kamar ki maman muhsin... Inajin dadin samun mutun irinki a rayuwa tah, nagode da addu'o'in ki garene, Allah yabar zumunci ya kuma sada mu a Aljannah,Amin😇




📙09




Khalifa ya shigo maid amma baisan ta ina zai fara Neman ta ba,waje yasamu yayi parking ya tsaya Yana tunani,can ya yanke shawaran zuwa wajen wani abokin shi ko zai temaka mishi,da wannan tunanin Yakama hanyan new GRA….


A wajen abokin shi Yusuf ya sauka Dan abokin daddyn shine,Yusuf yakaishi yagaida su maman shi sannan suka dawo side dinshi,kallon khalifa yayi yace gaskiya mun Dade fa bamu hadu ba tun rasuwan mamin ka,kafun kafita waje karatu,kanshi yashafa yace eh wlh, kai kuma don bakada kirki ko nema na bakayi ,baki ya bude yace lalle khalifa bakajin kunya sau nawa ina nemanka saikayita yin Abu kamar baka gane ni ba,dariya khalifa yayi yace to naji aboki na ayafemin,hannu Yusuf ya bude yace ai yanzu kam ka wanke kanka dole na na hakura.

yanzu kayi wanka Sai muci abinci,hannu shi khalifa ya kamo yace abokina nazo ka temakeni ne katayani ceto rayuwa ta,zama Yusuf yayi yace inajinka wane irin temako kakeson inma dahar kake danganta shi da da rayuwarka,ajiyan zuciya yayi sannan ya Ciro mishi hoton Nihal ya ajiye yace wannan yarinyan nazo nema kuma itace rayuwa ta inban sameta ba Yusuf wallahi zan iya mutuwa…hoton Yusuf ya dauka yake kallo sosai,sannan yace kabarni a duhu khalifa,budurwar ka ce? Ko kuma Baku taba haduwa ba yanzu kazo nemanta don ka sanar mata kana sonta?

mikewa yayi sannan yace wannan da kake gani sunan ta Nihal matar dazan aura ce don har iyaye sun shiga maganan mu sai wataran zata koma makaranta tabata har yau babu ita babu labarin ta,huh! Numfashi yasauke sannan yacigaba,lokacin data bata tsabar rudun Dana shiga wasu abokaina a garin jajere sukaban shawara akan inje incewa iyayenta nafasa nabiye musu mukaje mukayi musu rashin mutunci Wanda yajawo Bacin ran daddy na... Abun mamaki shine tun daga ranan Allah yaqara bijiromin da soyayyan Nihal kuma ko baccin kirki nadaina samu saboda tunanin Nihal, nayi nadama sosai Yusuf amma mutane sunkasa ganewa,har yau daddy na fushi yakeyi dani.

haka naje gidansu dakyar mamanta ta saurare ni kuma itama don nace mata zanne mo Nihal ne kasan yadda iyaye mata suke akan yaransu,amma data sanarwa baban Nihal ranshi baci yayi sosai har yace mata karta sake bari na intaka kofar gidan shi,amma duk da haka bai hana taban goyon baya ba saidai tace kar ina zuwa saboda baban ta bayaso amma zata tayani da addu’a inje Allah ya tsare.

nabi kauyen da tayi accident anan naji labarin ankawo ta Maiduguri, kaji abunda nake tafe dashi….

ajiyan zuciya Yusuf yayi sannan yace gaskiya dole ka shiga tashin hankali,amma fa kaima kayi kuskure yaya za'ayi da hankalinka ka biyewa en kauye,da hankalinka da ilmin ka? Na biyu kuma yaya akayi kasan accident tayi kuma har kasan kauyen da akayi?

Nan take khalifa ya duburburce Sai yanzu yagane Ashe ya kwafsa a labarin sa,take dabara yazo mishi yace wani abokinane yaban labari akan kwana ki police sunje gamdu da hoton ta suna Neman iyayenta wai anbugeta da mota,kaji yadda akayi nasani….

jinjina kai Yusuf yayi yace inshaa Allah zantaya ka nemanta Allah dai yasa adace, yace Amin, Sai kuma Abu na gaba abokina, Yusuf yace inajinka.. Dan Allah banason kowa yasan abunda yakawoni garin nan saboda banson en gidan mu da nasu su sani har sai na samota,yace toh shikenan inshaa Allah bazan gayawa kowa ba.


Garden din gidan yaje ya tura a kirata,me aikin sune taje dakinta tace wai tazo yasir na kiranta a garden,gyalen kayan jikinta ta dauka dama shi take jira,saida ta fito parlor ta tuno batasan inda garden din yake ba,kitchen ta wuce tasamu me aikin tace mata ta rakata,ta kofan baya suka bi,daga nesa ta nuna mata shi tace gashi can bari in koma wajen abinci kar ya kone,tace mata nagode,hango shi tayi da kana nan kaya ajikin shi yana zaune akan kujera, a hankali take tafiya harta isa sallama tayi kanta akasa,dagowa yayi ya kalleta ya amsa sannan ya nuna mata kujera yace bismillah…

zama tayi sannan yace me zakisha akawo miki?shuru tayi kamar bataji shi ba Sai kuma tace nakoshi, kallonta yayi yace ai drink ba abinci bane bari akawo miki,waya yakira baifi minti biyu ba saiga Ahmad ya kawo musu,yace yauwa Ahmad sannu,ni yaushe kadawo ne?yace banjima da shigowa ba…tunda yace Ahmad din nan sunan ya tsaya mata arai ji takeyi kamar ta taba sanin irin wannan sunan,binshi taketayi da kallo har ya juya,yasir ma tsayawa yayi yana nazarinta saida yaga dai batada niyyan dawo da hankalin ta sannan yayi gyaran murya, a zabure ta juyo,karkacewa yayi yana kallonta yace kingane shi ne? Kai ta girgiza da wuri tace a'ah kamar dai nasan sunan ne…shuru yayi baice komai ba,dataga shurun ne yayi yawa tace ya yasir ina jiranka,gyara zaman shi yayi kafun yace mata zan rokeki alfarma daya, dagowa tayi tana kallon shi donjin mezaice, Dan Allah ko me zangaya miki banason ki Tayar da hankalinki kuma inason ki daukeni a matsayin Dan uwan ki ko bayan labarin dazan baki kuma ki dauki maa tamkar mahaifiyar ki…shuru tayi nan take tunanin ko Ita waye ce kuma ko su waye iyayenta ya bijiro mata,hawaye ne yafara fita a idonta,rufe idon shi yayi sannan ya bude yace idan har kinsan zakisa damuwa a ranki ni nafasa baki labarin ya tsume.

da sauri tafara goge idonta tace nama alkawarin bazan tayar da hankali na kuma nadaina kukan…..

Numfashi yasauke sannan yajingina da kujeran da yake kai,yace “wani ranan asabar natashi da niyyan kaiwa wani aboki na ziyara da yake garin potiskum,nakama hanyan tafiya ko nisa banyi ba ina wajen wani kauye da ake kira da gamdu ban Ankara ba ban kuma San ya akayi ba, kawai dai ganinki nayi akan kwalta babu yadda banyi ba don ganin cewa ban tabaki ba amma hakan ya gagara kaddara ya riga fata, daga nan nadawo dake cinkin borno shine doctor yake sanar mana akan ba lallai bane inkin tashi ki tuna rayuwan ki na baya a lokaci daya ba,saboda kafun motan ya bugeki akwai abunda ya razana ki….

Shuru tayi tana jiran yaci gaba saiji tayi yana cewa,Kinji iyakacin abunda muka sani dangane dake,bayan wannan muma bamusan ko garin Ku ba.


Dagowa yayi yaga tana kuka sosai kamar ranta zai fita…rufe idon shi yayi saboda yadda kukanta yake taba mishi zuciya, a hankali yace Dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan haka zai iya cutar dake,idonta da sukayi jawur tadago tace ya yasir dole inyi kuka,kofa suna na ban sani ba balle garin mu balle kuma iyayena... Cikin kuka sosai tayi maganan ,yace ki kwantar da hankalinki na miki alkawarin inshaa Allah zan temaka miki mugano komai,amma in kina kuka me tsanani haka zakisa inji bazan yafewa kaina saboda komai yafaru ta sanadi nane,kuma yanzu duk abun da zai sameki alhakin na wuyana….


Ya yasir koba ka bugeni aranan ba Allah ya riga ya kaddara abunda zai faru,kuma ni naji dadi da yazama Kaine mutumin Dana fada hannun shi saboda kun bani kulawa tamkar ku kuka aifeni babu abunda zance muku sai godiya da addu’an Allah yasaka muku da mafificin alkhairi.

Cemata yayi.. Tashi mushiga ciki kije ki huta kinji kuma kicire damuwa aranki karki sawa kanki wani ciwon kinji,kai kawai tadaga mishi,shi yafara mikewa tabi bayanshi,kaita yayi har dakin ta ya dauko magunguna ta yaballa yabata sannan ya bude fridge ya dauko mata ruwa,sanda tasha sannan yace toh ki kwanta ki huta kinji ba musu ta kwanta shi kuma yafita tare da ja mata kofan dakin.


Dakin maa ya wuce samunta yayi tana rike da remote tana canja tasha,murmushi tasakar masa,tace Dan albarka ina kabaro er dakin naka,don yau tunda kafita take damuna wai yaushe zaka dawo,kujera yasamu ya zauna sannan yace yanzu taje ta kwanta, maa tace lafiya dai kam? Yace lafiya kalau,nabata labarin yadda akayi muka sameta ne shine tayita kuka dakyar nasamu tayi shuru….

Jikin maa kam sanyi yayi duk saitaji ba dadi... Allah sarki ni badon likitan nan ma yace a fada mata ba wallahi damun barta ta tuno don radin kanta, saboda nasan yanzu zatasa damuwa aranta Wanda zai iya jawowan taki sakewa damu…

Ajiyan zuciya yayi,sannan yace gayamatan dai shine mafi alkhairi don idan har mukace zamu boye mata dole zatayita damun mu Wanda hakan zai iya sawa mu mata karya,maa tace hakane Allah yabamu nasaran samun iyayenta,yace Amin.



*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now