HASKEN RAYUWA TAH 4

43 5 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ





📙04





Da safe maa gana ce takawo musu breakfast, maa tace toh tunda takawo takira su Ahmad tace basai sunkawo ba,amma suzo su kaisu gida suyi wanka sai maa gana tazauna da marar lafiyan kafun su dawo.

Maa ne kadai taci abincin Karin yasir kam yace sai yaje gida…

Ahmad ne yazo yadaukesu, yana kaisu gida bayan maa ta fita a motan,yasir ne yajuyo yana kallon Dan uwanshi yace Dan Allah Ahmad ka koma asibitin nan kataya maa gana kula da yarinyan nan nima yanzu zan shirya indawo inshaa Allah, kallon shi Ahmad yatsayayi yana mamakin yadda Dan uwanshi yashiga damuwa sosai,kai yakada mishi, yace badamuwa Ku huta nasan bakuyi baccin kirki ba inyaso zuwa dare sai inzo indaukeku.. dasauri ya girgiza mishi kai yace no karka damu yanzu zandawo don inason amaidata kebeben daki Inda ba mutane kuma zan koma wajen hukuma donjin ko ansamu iyayenta…

babu yadda Ahmad ya iya don haka yace mishi to shikenan zansa modu yakawo ma motanka…fita yayi yana ce mishi to shikenan.


Yana shiga daki kan gado yafada ya rufe idonshi,gajiya ne da kuma abubuwan da suka faru suka fara dawo mishi, babban damuwan shi yanzu ta ina zai samu iyayenta… a haka bacci ya kwashe shi, shine bai farka ba sai bayan awa daya…a hankali ya bude ido yanajin kanshi na mishi  wani nauyi,yana tuno a inda ya kwanta anan bacci yadauke shi da sauri ya mike yana salati,bandaki yafada yayi wanka da ruwa me dumi nan danan yaji jikin shi ya ware,bayan yashirya yana fita dinning ya nufa don ba karamin yunwa yakeji ba…abinci yaci sama sama yana duba agogo,
dakin maa ya nufa,yayi sallama yaji shuru,murda kofan dakin yayi a hankali,ganinta yayi akan gado Tana bacci don haka bai tada Ita ba,kitchen yawuce yasa mu me aikin su yace mata idan maa ta tashi tace mata ya tafi asibiti, har ya juya tace mishi yauwa dazun modu yakawo key yace abaka,karba yayi ya fita.


Sanda yafara tafiya har zaiyi hanyan police station sai kuma yaji gwara yafara duba yariyan kafun yaje can, asibiti yawuce,yana zuwa yacewa maa gana ta koma gida,shikuma doctor yaje ya gani don jin ko akwai wani improvement (cigaba), nan dai doctor yakara shaida mishi akan zata iya farkawa,ajiyan zuciya yayi kafun yagayawa likitan yanaso amaida ta Aminity nan likitan ya hadashi da hospital management yayi processing komai sannan yadawo yasameta da Ahmad,yace mishi ya tattara komai zasu koma side room nurses ne suka turata zuwa wannan dakin, sai lokacin hankalin yasir yadan kwanta don bayason cikin mutane.

kujera yaja ya zauna yana facing din kanin shi,yace Ahmad yanzu zan wuce police station don jin ya akeci idan nadawo zakaje kasayo mana abubuwan bukata ko kuma ma ka kira modu sai kabashi yasayo saboda kar abar wajen ba kowa,Ahmad yace to badamuwa nan yasir yabashi tare da lissafa mishi komai.

Yana parking ya hango officer da case din yake hannu shi yana shirin fita,da sauri ya fito ya nufeshi yana mishi sallama…da fara'ar shi shima ya mika mishi hannu yace alanguburo Kaine a tafe,yasir yace eh wlh tundazu naso inzo abubuwan kuma sai a hankali, officer yace hakane,ya me jikin? Jinjina kai yayi halamun damuwa yace Alhmdulillah amma fa har yanzu bata farfado ba,jinjina kai officer yayi sannan yace yanzu dai masallaci zanje kazo muje muyi sallah Sai kuma musan abunyi? Yace badamuwa tunda lokaci yayi, tare suka wuce sukayi sallah kafun nan officer ya mishi bayani akan zaici gaba da jinyanta har zuwa tawarke sannan kuma yanzu zai rakashi sukai cikiya gidan TV da radio. yasir shuru yayi yanajin shi har ya gama sannan yace badamuwa officer za'ayi duk yadda doka ta tanadar…

officer aranshi yake jinjina saukin hali irin na yasir,take suka wuce gidan TV da radio suka bada cikiyanta tare da hoton ta, daga nan sukayi sallama yasir yawuce restaurant don bayason yakara fita inya shiga asibiti.

bayan yagama yawuce asibitin yasamu har maa ta dawo,bayan ya gasheta ne yace" maa aida kin zauna a gida kin huta, murmushi tayi tace yasir kenan ai banida wani Hutu kana cikin tashin hankali, dagowa yayi yana kallonta yace maa ai yanzu na kwantar da hankalina damuwana daya shine yarinyan nan tafarka,tace inshaa Allah zata farka muna nan munata addu'a,yace Allah yasa tace Amin.


Kwandon abinci tafara jawowa tana cewa maza zauna kaci abinci kasan banason zama da yunwa,murmushi yayi yana Sosa keyanshi yanajin son mahaifiyarshi a zuciyan shi,yace maa ai saida nabi wajen cin abinci kafun nadawo..kallon shi tatsaya yi tace nasan bakason ci a asibiti ne to ko zaka koma gida kaci?
Cikin muryan rarrashi takare maganan zama yayi a gefenta yakamo hannu ta yace Allah dagaske nakeyi maa naci abinci, murmushi tayi don tasan yasir ba mutun ne meyin karya ba, tace toh shikenan… Sai lokacin ya lura Ahmad baya nan,maa ina Ahmad? Tace yanzu nace mishi yaje gida ya huta,kaima inason ka koma gida don jinyan ‘ya mace Sai ‘ya mace…

ajiyan zuciya yayi yace kiyi hakuri maa ba gardama zan miki ba amma Dan Allah kibarni inzauna a asibiti nan zanfi samun kwanciyar hankali… tsayawa tayi tana kallon shi kamar tanason yin nazarin wani Abu Sai kuma tace, to ai shikenan Sai mu zauna.







*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now