💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
*A kullum mutun yazamo mesa rai ga rahmar ubangiji da kuma yarda da kaddara mekyau ko marar mekyau,a lokuta da dama Allah yana jarabtan bawanshi da abunda yafiso domin yagwada karfin imanin sa....*
📙28
BAYAN SATI DAYA
Shower yasakanwa kashi ruwa na zuba kamar ba mutun a wajen,idon shi a bude yake jijiyoyin kanshi duk sun tashi,abubuwa dayawa yake sakawa acikin ranshi don bayajin zai iya barin wayanda suka aikata wa ya yasir wannan aiki su tafi a banza. Yakai awa daya ahaka kafun nan yafito,rigarshi kawai yasa yayi hanyan waje maa ce takirashi Ahmad! Ansawa yayi cikin disheshshiyar muryan shi Wanda tsabar bakin ciki ne yadasar dashi ba kuka ba, don har yau bai samu yayi kukan dayakeson yi ba,zama yayi ba tare da ya kalleta ba….
Kallon shi tayi kamar na seconds talatin kafun nan tayi ajiyan zuciya, tace Ahmad inason kanasawara ranka salama kuma komai da kake ganin yana faruwa da sanin mahalicin mu,wani abun yana faruwa da bawane domin agwada karfin imanin shi da tawakallin shi…
Yana nuna ma duk yadda mukeson yasir zai iya daukeshi acikin mu kuma a second daya,sannan babu abunda zamu iyayi akai.
To sai muje gode mishi da yasir bai mutu ba,tunda yana tare damu, banason kayi wasa da rayuwan ka, kuma in da zakabi shawara ta ma daka bar maganan nan mubarsu da Allah,ai Allah yafisu.
Jajayen idon shi yadago yace maa zan iya yafe komai amma banda irin wannan to zarcin, akan idona zasu harbi ya yasir?idan har muka barsu bazamu tsira ba nan gaba sai sunmana abunda yafi wannan, koda kuwa mutuwa zanyi bazan tsaya ba sainaga bayan su.
Shuru maa tayi ta sunkuyar da kanta dayaga batace komai ba tashi yai ya fita.
Barrister kasim ya kira, yace mishi yazo office yanzu ma akan case din suke investigation, kasim abokin yasir ne Wanda dashi sukeyin komai a wajen aiki kuma yanzu ma haka shiyaci gaba da bincike akan case din.
Hotunan wayanda ake zargi kasim ya mikowa Ahmad dubawa yayi yaga babu Wanda zai gane acikin su domin ranan basuga fuskan su ba…zuciyar shi ne take suya jiyake kamar ya kurma ihu,a take lokacin da ake Harbin ya yasir ya fado mishi tunowa yayi Wanda ya harbeshin hannun shi akwai wata zab gagiyar tabo wacce takai Harkan yatsunshi,da sauri yacewa kasim yasake bashi hotu nan yagani, yana karba yafara kare musu kallo harya kusa gamawa baiga abunda yake zargi ba,sai akusa dana karshe yaganshi….jikin shi har bari yakeyi yace ya kasim gashinan shine ya harbi ya yasir wlh shine bazan taba manta wannan tabon hannu shi ba,karba kasim yayi yace wannan dama ana zargin su suke sponsoring yaran da aka kama,tashi yayi yace zo muje.
KAFUN SATI DAYA
Ana zuwa nurses suka dagata aka shiga da ita ciki maa ne tabisu tana salati tana wayyo nihal kema karki tafi kibarni, nashiga uku yarana zasu tafi subarni… office likitocin sukaja Ahmad dukda shima acikin rudu yake amma yafisu dauriya,likitan ne yace mishi ka nutsu kajini, bullet ya taba zuciyan shi amma duk da haka bai mutu ba,saidai gaskiya akaf Nigeria bana tunanin akwai inda za'a iya mishi aiki inda hali saidai ku kaishi india nan ma sai kun hanzarta saboda zai iya rasa ranshi….ajiyan zuciya yayi ya runtse idon shi hamdala yayi dayaji yayan shi yana da rai,yanzu damuwan shi daya wazai temaka mishi abubuwan sun mishi yawa,wayanshi ya dauka yakira maagana yace maza tazo asibiti ko bayani bai mata ba yakashe ya kira Abba,yagaya mishi halin da ake ciki,sannan yaje yasamu maa akan Nihal, tana ganin shi tazo ta rungumeshi tana kuka sosai,tana cewa shikenan yasir dina ya rasu ya tafi yabarni,ni Fatima ina ganin rayuwa,dago kanta yayi duk hannu shi na rawa yace maa kibar kuka ki kwantar da hankalinki ya yasir bai mutu ba,ido tazare tafara jaa da baya tana girgiza mishi kai,Ahmad karkayi tunanin zaka rarrasheni da irin wannan kalaman,kuma mutuwa daya ce…dasauri ya katseta wallahi maa bai mutu ba, yana nan,take yagaya mata bayanin da likitan ya mishi,cikin rawan jiki tace bani wayanka,acikin Daren nan za'a fara shirin tafiya India, tsabar yadda jikinta yake rawa ma takasa samun number da take nema cikin sauri ta mika mishi tace kiramin rawanyi kura(yayanta da yake zama a UK) kiranshi yayi ya bata take ta mishi bayanin komai adaren yayi waya Nigeria akagama komai akan karfe 3 wannan Daren private jet dinshi zaizo yadaukesu Wanda yanzu haka saura awa uku,Abba ma adaren yasamu yataho karfe biyu ya iso har cikin asibiti jirgin yazo da Abba da Ahmad ne suna tafi,kafun su isa rawanyi yayi waya India har yayi magana da asibitin dazasu je, suna isa da minti talatin aka shiga dashi operation.